← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 60

Sashe 7

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi, ina daga tsallake ina jiran shanun su gama wucewa" Zuchiyata ce naji tana bugawa da ƙarfi, idanun Debisi naji sunyi mun kaifi. Na so Debisi so na haƙiƙa, soyayyarshi ta wahalar da rayuwata, dan zuchiyata bata iya son abu ba, in zata so abu da gaske take sonshi, haka kuma ban iya ƙin mutum ba" Bamu dena kallon ƙudan da muke ma juna ba har sai da garken shanunnan suka gama wucewa. A hankali na isa ƙarƙashin bishiyar. Carab ya amshe ƙwaryar damammiyar furar dake hannuna. Na shimfiɗa tabarmar dana fito da'ita, tare da cewa. Bismillahi Buradomi ka zauna" Murmushi yayi mun, irin wanda ada nake mafarkin ganin yanai mun. Banda a yanzu dan tuƙuƙi naji zuchiyata nayi mun. Kuma ina fatan ba cewa zaiyi sona yake yi ba, dan zan iya zaginshi tsab, laifinshi mai girmane a gareni, babu abinda zai iya faɗamun in yarda ba yaudara bace" Waje na samu na zauna kamar yadda yai mun izini. Shiru ne ya biyo baya na tsawon minti shida kafin yace "Bansan ta inda zan soma ba Iyabo. Gashi zuwan nawa ya haifar da matsala mai girma, ina mai neman gafararku baki ɗaya. Amman kafinnan me kika je yi a Kano, sannan wannan ramar duk ta rabuwa da Gwadaben ce, ko kuna cikin wata damuwane?" A jijjere yayi mun tambayoyin da na yi jim, ina cinka cinkar wanda zan sona amsawa a cikin zuchiyata. Sai na sake jin amon muryarshi yana cewa "Da zan baki shawara, da nace ki shirya ki bini mu koma Kano. Tunda kika baro Kano kika barmu cikin kewa da alhinin rashinki. Nawa kuwa yafi na kowa. Kuma a kwana biyu kacal da nayi a rugarnan na tabbatarma kaina rayuwarki ba zata taɓa yi miki daɗi ba. Ke da kika taso a maraya, ga hasken lantarki, ga ruwan famfo, ga makarantu, ga titina, ga_ga_ga. Amman anan fa babu abunda suka sani sai kiwo da tallar nono, ace kamar Dada tallar Nono itama take zuwa yi, su Ɓodɗo ma tallar suke ɗauka fa" katseshi nayi ta hanyar cewa. Tambayarka ta farko gareni shine. Naje Kano ne nayi fasfo zan tafi ƙasa mai tsarki da izinin Allah neman kuɗi. Tambaya ta biyu kuma. Ciwo nayi mai tsayi shi yasa na rame. Gwadabe kuma yana ɗamfare a raina tsaiwar numfashinane kaɗai ka iya kawo ƙarshen soyayyar Gwadabe. Batun rashin iya zaman rugarnan kuma. Zan iya ko dan Dada, da ƙannena. Bana jin komai na dangane da kewar birni, ko ƙyale_ƙyalen dake cikinta. Ni babu abinda a halin yanzu yake burgeni. Nafi samun nutsuwa a haka" Ashe ni na kasheshi da namaki ban sani ba. Sai da na juyo naga bakinshi a hangame yana kallona, da halama ya ɗan jima yana kallon nawa "Saudiyya fa kika ce zaki je neman kuɗi Iyabo?" Ya faɗa a ƙagauce da son jin amsata. E Saudiyya da izinin Allah, Lokaci kawai zamu jira." " Da izinin wa zaki tafi Iyabo, me yasa Kano bata isheki neman kuɗi ba har sai kin dangana da ƙasa mai tsarki, sannan me yasa baki yi tunanin Aure, ko komawa makaranta wanda nasan yana daga cikin burukanki na rrayuwa ba?" Ya sake jejjero mun wannan tambayoyi cikin ɓacin rai a wannan karon. Baki na tsuke bance mishi komai ba. Tsawa ya daka mun wacce tasa ƴan hanjina kaɗawa. "Ba dake nake yi ba kin mun banza ba?" To ni kam Burodami me zance maka? A halin yanzu babu wani karatu, ko aure a gabana. Rayuwar mahaifiyata kawai nake dubawa, da mafarkin samar mata da sauƙin rayuwa. Ka dai taya ni da adda'a zaifi. Dan babu makawa zanyi tafiyarnan. In kaga banje ba Allah ne baiyi ba. Kayi haƙuri kar kace na bijire maka" Sai yayi shiru na wasu daƙiƙu kana yace. "Amman ba kya ganin in kika tsallake ƙasarki Najeriya, kika tafi wata ƙasar neman kudi. Ba kya ganin wasu zasu yi miki kallon da bai dace ba? Ballantana kinga ke bazawarace kina da ƴaƴa. Acan kuma baki san hannun waɗanda zaki faɗa ba" Hannu na gari zan faɗa da izinin Allah. Kuma wama zai san na tafi Burodami Debisi?. Kaga Dada tana cikin halin da ya kamata a taimaka mata. Kuma ni bazan wuce shekara uku ba zan dawo. Kafin in dawo amman sai na tabbatar da na samu dukkan abunda naje nema." Ajjiyar zuchiya ya sauke, yayi shiru yana kallona, ni kuma nayi ƙasa da kaina. "To batun aurenmu sai kin dawo za'ayi kenan. Ko kuwa zaki amince a ɗaura kafin ki tafi? Dan ni harna sanarma Baffa Musa sababin zuwan nawa. Yayi murna matuƙa da jin hakan" Wani kallo nayi mishi, wanda ko a mafarki banyi tunanin akwai ranar da zata zo da zan yi mishi wannan kallo ba. Aure a tsakaninnu babu shi har gaba da abada. Har gobe nice Iyabo mai ƙibarnan, wannan wacce sai da ka kwanta jinyar ƙiyayyarta. In ma mafarki kake yi ka farka" Ina dasa aya sai kawai na miƙe hawaye fal Idanuna. Takalmaa nake shirin sawa yayi maza ya miƙe shina. "Iyabo" Ya kirani da sauri. Cak na tsaya. Ban tafi ba, ban kuma juyo ba. Ina jiyo takunshi har izuwa daf dani. "Nasan kina sona Iyabo kar ki soma yaudarar zuchiyarki. A rashinane kika auri Gwadabe. Iyabo zan baki farin ciki irin wanda mafarki da hasashe ba zasu iya hasko miki ba. Duk duniya ba wanda zai soki sama dani, sai dai ya biyo bayana." Hawayena na share, tare da lumshe idanuna, zuchiyata kuwa sai aikin turiri take. Da ƙyar na haɗiyi miyau nace. Iyabonnance dai wannan mai ƙibar da kaƙi aurenta sabida wannan halitta tata. Ba canjawa nayi ba. Duk da nasan na zabge rabi da kwatan ƙibata, a sanadiyyar halin yau da gobe Ka sani kibata zata iya nunkuwa da kaso sama da hamsin akan na da wanda ka guje ni dominta. Debisi ina mugun girmamaka ne ma yasa harna tsaya saurarenka. Amman da ba dan haka ba ko kusa dani baka isa kazo ba. Maganar soyayya ko aure babu ita, dalilin da yasa ka barni ina budurwa. Dalilin ne dai yasa na barka bayan na zama bazawara" Ina dasa aya nayi shigewata cikin gidan. Duk a tsakar gida na tarar dasu, amman banda Daso. "Adda Jabu Yaya Debisi ya kawo miki wata ƙatuwar leda, tana wajen Adda Daso. Muma duk yayo mana tsaraba mai yawa" Ɗan murmushi na ƙaƙaro nace. Ayya. Ai Burodami Debisi ba daga nan ba ta wajen kyauta. Boɗɗo ku taso muje gidanki, dan acan nake son mu tattauna kamar yadda na faɗa miki ina da Magana da zamu tattauna daku. Ina zuwa bari in samu Daso in sanar mata" A cikin bukkarmu na sameta tayi tagumi sai aikin tunani take faman yi, dan bata san ma na shigo ba har sai da nazo daf da'ita. Ta ɗago fararen idanunta ta zuba mun su. Akwai damuwa sosai a tattare da'ita, wanda a tunanina baya rasa nasaba da kewar tsohon mijinta marigayi. Daso wai me ke damunki ne, ni tunda na dawo na ganki wani sukuku. Ko duk rashin lafiyar Dada ne?" Na jefeta da tambaya, tare da kafeta da idanu domin karantar yanayinta. "Ba komai abubbuwane sukai ma zuchiyata nauyi Jabu. Amman zamu tattauna zuwa dare" kai na gyaɗa mata kawai. To ni zanje gidan Ɓoɗɗo akwai maganar da zamu yi dasu duka" Kur ta mun da idanunta kamar mai karantar wani abun a fuskata, sai kuma ta ja numfashi tace. "Bari in zo muje, inaso dama inje wajen Hama, in yaso in kun gana tattaunawar sai ki same ni a ɗakinta" Hakan ko akayi, a hanya ne take labartamun Debisi ya kawo mun wata ƙatuwar leda, ta adana mun ita. Ni dai kai kawai na gyaɗa. Mun ci tafiya sosai kafin muka iso gidan. Matan gidan duk suna tsakar gida anata tuwon dare, wasu kuma suna wanke ƙoren tallar nononsu, Yafendnmu bata nan bata dawo daga can gidan Baffa Musa ba. Daso ta ya da burki a ƙofar bukkar Hama, tana zaune tana tuƙin tuwon masara, masararnan fara tas gwanin ban sha'awa. Da dariya da haba_haba muka kaisa da Hama kafin muka shige bukkar Boɗɗo. Bayan kowa ya nemi waje ya zauna, sai na yi gyaran murya na soma da cewa." Dukkanku kun fini sanin irin halin da Dada take ciki a gidan aurenta. Da irin matsalolin duka, da tsangwamar da Baffa yake yi mata. Ku yi haƙuri Baffa mahaifinku ne, amman nasan ku kan ku kunsan yana zaluntar Dada. A shekaru irin na Dada ai yaci ace ko da an daketa a baya, a yanzu a barta ta huta ko dan kaifin idanunku. Ga yawon talla, duk rauni da da gajiyar dake jikinta tana talle. Amman anan naga ku kamar talla wani abune na dole." Boɗɗo ta tari numfashina da cewa. "Talla tana cikin sharaɗin aurenmu mu kam. Domin da kuɗin nononnan zaki ɗauke nauyin ci da sha na gidanki, harma ki yi ma kan ki sutura da dukkan buƙatu. Su kuma maza aka barsu da kiwo. Sai dai wasu matanma suna fita kiwon su dawo lafiya. Dukan da Baffa yake ma Dada ni shine damuwata. Anan ɗakin mun sha zama domin tattauna wannan matsalar, rashin mafita ke sa mu yi haƙuri kawai. Amman zukatanmu na sosuwa ainun, hakan ya zabtare kima da darajar Baffa ta Uba a garemu. Domin mun fi son Dada sama dashi sai dubu babu haɗi" To ni dai ina da shawara, so nake zan tafi saudiyya neman kuɗi. In na tara kuɗi zan dawo, inaso Baffa ya saki Dada ne kawai. Ni kuma zan ɗauketa harda su Yusufu in sai mata gid, ta zauna ta ci moriyar haihuwa ko wanke_wanke ni zan dinga yi mata ko da nayi aure. Amman meye shawararku kune ƴan uwana?" Boɗɗo tace. "Da hakan zai faru wallahi Adda sai mun fi kowa farin cikin faruwar hakan. Ni da Amaduyal mu muka san irin wuya da dukan da Baffa ya dinga yi ma Dada. Har ɗaureta yake yi a jikin gadonta ya daketa ciki da waje." Anan suka sake fayyace mun halin da Dada take ciki a gidan aurenta. Kuma duk suka bani haɗin kai akan suma sun amince a saki Dada. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, duk yawan shanayen Dada dake hannun Baffa bazai yarda ya bayar ba.
Chapter 7 · 0% Book details