← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 60

Sashe 47

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

buɗe. Ɗagowar da zata yi muka haɗa idanu. Saina fashe da kukan farin ciki dan ada na fitar da ran sake sanyasu ga idanuna. Iyaa ai saita soma wannan kwakwazo data saba, kafin kwabo jama'ar gidanmu duk suka firfito ciki harda yemisi da titsetsen cikinta a gaba, ko me take yi a gida duku_duku ohon mata dai. Iyaa Kokodeen ce ta ja hannuna zuwa cikin gida ɗakin Iyaa. Nan aka shiga gaisawa da tambayar bayan rabuwa. Sai cewa suke yi nayi kyau na yi haske, amman na rame. Ni dai sai dariyar yaƙe. Ruwan wanka Lekan ya kaimun, na shiga na gargasa jikina. Kafin in fito nazo na tarar da kwanukan abinci har daga maƙota. Sannan matan unguwa har sun soma cika gidan anzo yimun sannu da zuwa. Na zama kamar watan ramadan, kowa sha'awata yake yi haƙorina na maka har biyu maƙale a bakina sunata sheƙi, na fahimci hakan ya ƙaramun kwarjini sosai. Ni dai sai yaƙe baki nake yi, amman ta ciki na ciki. Amala naci na ƙoshi na sha baƙin bunu. Kwanciya nayi dan in ɗan huta, dan a niyyata gobe in Allah ya nuna mana zan kama hanyar ƙauyanmu, suma in gansu su ganni, sannan inga ajiyata dana ajjiye.( Maƙiyan Hamma ya jiki? 🤣) Bani na farka ba sai azahar, Burodami Debisi da Burodi Kokodeen suna ɗakin, ga yemisi a gefe ana musu sulhun da aka saba. Burodi Debisi muna haɗa idanu yayi mun murmushin da ada in banyi mafarkin irinshi daga gareshi ba yau, nayi gobe dan tsananin yadda nake mafarkin in zama matarshi. Sai gashi kash yanzu idanunshi a kulle suke akan sona. Yayinda nima idanuna suka makance akan son Yaya Hamma. "Iyabo kece kika sake wani kyau da kwarjini haka? Kai maraba lale da shigowa ƙasarmu me albarka." Kaina na sunkuyar dan bazan iya juran irin muguwar hararar da yemisi ke watso mun ba. Kafin in gaishesu Yemisi tace. "Dama a wannan karon ke kike barazanar kashe mun aurena sai gashi kuma kin dawo gida. Dan Allah in aurenshi kikeso kiyi me yasa tun farko ba kui aurenba, me yasa zaki ɗauke tunanin mijina daga gareni" " Mama Iyare Yemisi ( Kinci uwaki Yemisi)" Iyaa ta zageta, dama dai jira take yi sai ta sau kuka kawai. Ni kuma so nake in yaɓa mata maganar da zata sake ingizata amman saina gaishe da Burodami Debisi, da Burodami Kokodeen, Kokodeen yace. "Tunda kika tafi ba'a waya dake. Iyaa har ramewa tayi sabida tunanin ko kina lafiya. Hakama Dada da wani dogon ɗan uwanku Hamma. Dan duk sanda Dada zata zo tare suke zuwa, suna yawan zuwa in banda kwana biyunnan da basu zo ba muke tunanin ko ba lafiya ba.. Gabana ya yanke ya faɗi ras jin an ambaci ba lafiya ba. Yanayin aikine, kuma ni bama waya a hannuna shiyasa. Gobe sassafe nake so dama in wuce Jeren." Burodami Debisi yace. "Ki zauna ki huta mana kafin ki tafi" Iyaa tace. "Gara taje, ina tunanin Daso ko babu lafiya fa. Wannan karon sun jima basu shigo ba . Gobe ta kama hanya kawai. Ki yi sallah sai mu tattaka mu je gidansu Uwani kafin Hajiyarta ta rigamu zuwa aji kunya" To Iyaa" Ina faɗar haka na miƙe na fice ɗauke da buroshi da makilin dake jakata. Bakina na goge na ɗauro alwala na shigo. Dabino da bagaruwa da na jefo a jaka da ruwan zamzam na ƙananun fararen roba na ciro ƙullin nasu Iyaa na ajjiye mata. Ga wannan Iyaa, kayanmu suna jirgin kaya. Ba zasu wuce wata guda ba, dan munyi sare_sare sosai ne" Nan Iyaa ta soma rawa tana shi mun albarka. Ai kuwa wannan dabino sai Iyaa ta shiga aikin kididdibashi ana kasabta harda maƙota ma. Da haka suka ci gaba da shari'ar Yemisi dake gabansu, Iyaa ta lallaɓata tasa Debisi ya bata kuɗin cefane akan da yamma zata koma. Ina Idar da Sallah na saka doguwar jallabiya irin baƙin larabawannan ni da Iyaa muka kama hanyar gidansu Uwani. A hanya ne take sanar mini cewar sunje dubo Yarana dai aka tabbatar musu wai yaran suna Abuja wajen Matar abokin Gwadaben. Ajjiyar zuchiya na sauke nasan ko babu komai zasu samu ilimi. Allah shine masani idaniyata cike take da son ganin Ƴaƴana. Amman nasan ƙila yarannan sai sun girma a kwatanta musu inda nake rayuwa su neme ni. Ina musu fatan samun nasara da dacewa akan dukkan abinda aka ɗaurasu akai. Inma karatu, inma sana'a domin dogaro da kai. Daga su hai mahaifin nasu ina musu adda'ar samun ɗaukaka. Har a ka'aba na yi musu wannan adda'ar na jaddada. Da tulin tunani da misalai muka shiga gidansu Uwani dake cike. Ƙannenta duk sun cika gidan, da yaran kawunta dake aure da yaransu. "Ahh Toyosi yau kune a tafe. Sai kika ga baƙin larabawa sun sauka" Cewar Hajiyan Uwani. Musa wanta yana zaune yana cin bagaruwa Yace. "Kaga Hajiyoyin ƙannenmu Makka kiran Allah, kun sha aikin Hajji da umara har kun gaji, ga sallar juma'a a masallacin ma'aiki arrasul S A W." Na kalli Uwani dake daga cikin ɗaki Hafizu da yaranta suna maƙale da'ita. Ido ta kashe mun, ni kuma nayi dariyar da mu kaɗai muka san fassararta. Ai kuwa Musa ya saki ihu. "Ihuhu jibi haƙorin makka yadda yake ƙyalli a bakunanku. Dan Allah ko umara ku biya mana da ramadana dai mu je" Ni dai sai Dariya nake yi. Hajiya na gaisar na shige ɗakin da Uwani take. Iyaa kuma suka shige ɗakin Hajiya. "Iyabo barkanku da dawowa baƙin larabawa" Zama nayi yaran duk suka rufeni. Safwan na ɗauka ya girma sosai. Hafizu ina yini mun sameku lafiya?" "Lafiya lau sai alkhairi. Kin ganni nafi awa nawa ina lallaɓa ƴar rigimarnan amman haƙona yaƙi kai ga ci" Yaran na kalla nace. Amira kama hannunsu, ga ɗari biyu kuje ku siyi wara kuci ko? Kafin kayanmu su ƙaraso yarana na siya muku kaya masu kyau da tsada. Harda Hafizu a washe baki. Suna fita saina dawo da hankalina kan Hafizu. Ina saurarenka" "Iyabo kinsan kun tafi kun barni akan baifi wata ɗaya nima yayi mun ragowa in tafi Canada ba. An samamun aikin da bamu san wanne iri bane. To ko bayan tafiyarku saida muka fi wata huɗu kafinma muka tafi. Tsaiwa kwatanta azaba da wahalar da matasa ƴan cirani suke sha a ƙasashen waje ɓata bakine Iyabo, abun duk gidogace ruɗune. Shekarata biyu a daddafe na dawo da kuɗin da bai taka kara ya karyaba, banda jinyar jiki dana sha. Dawowata ke da wuya ina zuwa ƙauyenmu sai mahaifiyata take nina mun Farida tace ai an ɗaura aurena da'ita. Kinsan mutanen ƙauye gani suke yi wani kuɗi nayi. Ni kuma a cikin kuɗin da nazo dashi da ƙyar na ƙuƙuta harda bashi na sai ɗan ƙaramin gida mai ɗakuna uku rak. Amarya ta tare a ɗaya, ɗayan nazo wajen Hajiya na karɓi yarana suka tare a ciki, ɗayan kuma na kulle mata a matsayin ɗakinta. Shine fa taƙi fahimtata ca take wai ita in saketa kawai. Yanzu taya zan saki uwar Ƴaƴana uhm Alaja Iyabo ki duba zancena sabida Allah kiyi mun adalci" Jikina yayi murus hankalina sai naji ya tashi. Lallai in har haka ta faru da Uwani. Ni kam ina cikin goma sha biyu. Uwani duk sabida rufin asirinsu ta tafi wannan ƙasa, amman jibi abinda ya biyo baya kafin dawowarta. Ina kuma gani da ko kalmar so Yaya Hamma bai furtamun ba?" Da ƙyar na yakice tunani na sauke ajjiyar zuchiya nace. Shikenan Hafizu zata dawo ɗakinta amman dole sai dare. Sai dai da yamma ni da Ummi zamu zo mu yi mata jere" Baki ya washe yana dariya ya miƙe. Har fa ya kai bakin ƙofa ya dawo. "Alaja Iyabo ni kuwa kayan naku masu isowa har dila nawa ne?" Hararar da Uwani ta zabga mishi ce yasa yayi firgigit ya fice yana dariya" "Kikace zan koma Iyabo? Ni wallahi da naso in haƙura da Hafizu. Duk wannan tatsuniyace fa ya baki ɗan iska marar mutunci" A'a Uwani ki koma kan ƴaƴanki, ki riƙe sana'arki ki kula da kanki da Ƴaƴanki. Ki godema Allah ba mazinaci Hafizu ya zama ba, kuma ki gode Allah baki mallaka mishi dukiyar da kika sha baƙar azaba wajen tarata ba. Yanzu dai ki taso muje mu sai kayan ɗaki na gani a faɗe." Harara ta gallamun. Nayi dariya nace. Zaki bari matarshi ta rainaki ne, ke da kike Hajiya? Uwani kiyi haƙuri dan Allah karma ki nuna ma kishiyarki wai kinji zafin abinda suka aikata miki." "To Shikenan Iyabo. Na ɗauki shawararki. Amman sisina bazan iya kashewa akan Hafizu ko matarshi ba wallahi in tsirara zasu yi yawo sun dade basui ba. Muje ni dalla" Fitowa mu kayi, daidai Iyaa itama ta fito. "Ina zakuje kuma?" Zan raka Uwani ta siyo kayan ɗakine da daddare zata koma gidanta" Hajiya ta taɓe bakinta tace. "Sun gama tata ɓurzar kenan? Ai haƙuri dama dole za,a yi daga ƙarshe, kindai ga halin mazan dai. Wannan ya isheki hankali sai ki tattala dukiyarki kiyi abinda zai fissheku. In da ke kaɗai kike da Hafizu to yanzu ku biyu ne. In da ƴaƴanki ne kaɗai ƴaƴa yanzu suna da Ɗan uba harda wani cikin" Ni dai jikina sake mutuwa murus yayi. Zuchiyata saita shiga cikin taraddadin abinda ni kaina zanje in tarar a ƙauye. Ni dai har muka isa shagon saida kayan katako da Uwani da ƙannenta mata biyu da suketa mana biyayya mu ga hajiyoyi. Kado da sib da mudubi kawai muka siya, sai labule da makeken kafet mai taushi. Kayan kitchen kuwa ɗan tsakura tayi sabida nanda wata ɗaya kayanmu zasu iso. Ni da ƙannenta ne muka wuce gidan, ita kuma ta wuce kasuwar kurmi ɗan siyayyar kayanmu na mata. Gidan wani irin gantalallen gidane ginin laka, ko filasta babu a tsakar gidan, datti da shara takota ina. Hafizun yana zaune a ƙofar ɗakin da ya kasance na Uwani. Amarya kuma sai wanki take yi ga ciki a jikinta ga yaro a ƙofar barandar ɗakinta a kwance." Hafizu masu motar kaya suna waje ka taimaka musu. Amarya barka da gida" Na faɗa a tare. Babu yabo babu fallasa ta gaishemu kana taci gaba da wankinta. Niko ƙare mata kallo na shiga yi tsab, in banda abun ɗa namiji ni dai banga
Chapter 47 · 0% Book details