← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 60

Sashe 50

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

17 Ina daf da shiga gidan wan mahaifina Alfa Kulle dan in mishi sallamar gobe zan koma ƙauyenmu. Sai naji muryar Burodami Debisi. "Iyabo tun magriba nake jiranki a tsakankanin gidajannan biyu. Dan nasan gobe zaki tafi wajen Hamma. Nayi imani da ace yasan kin dawo da yanzu yana naniƙe dake" Cikin kishi da jin zafi yake maganar. Ni dariya ma ya bani sosai. Sai da na dara tukunna kana nace. To mu shiga inma Alfa sallama in mun fito sai muyi magana. Shi kuma Alfa muna shiga bayan na karanto mishi inaso zan koma ƙauyanmu kamar jirana yake sai yace. "Ba zamu saka miki idanu ba, sai kuma ki kawo maganar aure a gabanki hakanan. Na baki wata biyu ki fito da miji, in baki fitar ba zamu fitar miki. Dan da ace Toye yana da ranshi ma ko Saudiyya da kika je ba zai bari kije ba. Tun kafin jama'a su soma miki wani irin kallo gara ki fitar da mijin aure" Kaina a sauke nace. In sha Allah kafin lokacin yayi zan fitar Baami." A gidan muka ci abinci a cikin ɗakin Iyaa Ramata." "Kin tuna da wancan gadon da in kun mun lefi ke da Bose kuke shigewa?" Cewar Debisi daya samu saken daga ni sai shi a ɗakin. Dariya kawai nayi inacin amala. "Yaya batun aurena dake ya kwana Iyabo? Tunda Allah ya dawo dake ya kamata muyi magana tsayayya" Rai na haɗe nace. Har abada ni da kai ba zamu zama mata da mijiba, muna nan a matsayin Yaya da ƙanwarnan. Na riga na faɗama tun kafin in tafi. Ina ni ina haɗa miji da Soja?" Murmushi yayi mun har yana gyaɗa kai. "Lallai yarinyarnan bakin ki ya buɗe. Nifa wallahi da gaske nake yi, da kinsan irin yadda sonki yake nuƙurƙusar zuchiyata nayi imani da tuni kin ceci ran ɗan uwanki" Kallon dana watso mishi bansan na iyaba, a mafarki banyi zaton zan iya mishi makamancin wannan kallon ba. Amman sai gashi nayi. Hannuna na tsame tsam a abinci na ficewara na bar gidanma baki ɗaya. Koda na shiga Yemisi na zaune tana zaman jiran mijinta su koma gida. Ban jima da shigowa ba sai gashi, ko shigowa baiba cikin ƙailula yace ta fito su tafi, gaga_gaga yai ma Iyaa sallama. "Iyabo wai menene tsakaninki da Hamma? Dan naga damuwar da yayi akan lamarinki abun yayi yawa, yafi ƙarfin ace ƴan uwantakane kawai. Duk sanda Daso zata zo bayan tafiyarki dashi ake zuwa. Shine nake son jin ina fatan ba tallar nono zaki koma yi ba, ki dawo mai sharar kashin shanu da dafa madara. Ai in abune mai daɗi da ba haka ba. Rayuwar matan fulanin daji cike take da bauta, matan da yawa da wannan tallar nonon suke ciyar da gida, su kuma mazan suna bin jeji_jeji suna kiwon shanunsu. Ke irin rayuwar da mahaifiyarki take yi irinta zaki jefa kanki aciki? Kwanaki can da Debisi yaje ya tarar da Daso ba lafiya ga ƙaninki Amaduyal ya dawo daga inda suke fita kula da shanu ga kuɗi a jikinshi a kaita asibiti ubansu ya hana. Sai Debisi ne ya dinga jigilar sai mata magani shima a ɓoye ana bata. Irin rayuwar da kike sha'awa kenan ko?" Illahirin jikina sai naji yana rawa da ƙyar nai kokuwa da harshena wajen sarrafashi. Iyaa ni bazan yi tallar Nono ba. Kuma Hamma shi yana fita aiki a birni masinja ne a ma'aikata bai dogara da iya kiwon shanu ba, mijin Baɗɗo yafi fita da shanun.Sannan.... "Otito ( ya'isa haka) ki dai yi tunani ki kalli uwarki a matsayin mudubi zaki gane mai nake nufi. Rayuwar ƙauye sai ƴan ƙauye madamar suma sun fito ko ziyara dan dole suke zuwa" Ta dinga mun kwatance iri da kala. Da waɗannan tunanin gari ya waye damu. Gaga_ gaga bayan nayi wanka nayi Sallah, saina saɓi akwatina. Nayi sallama da mutan gidanmu sai tasha. Motar Adamawa saura Mutum uku ta cika, nayi zamana ina ta aikin tunanin yadda rayuwa zata kasance inna auri Yaya Hamma. Sai wani shashe na zuchiyata ya tunasar dani cewar "Ai masoyi masoyine imma a birni imma a ƙauye. Zaman aure nutsuwa ake nema, soyayya babu ruwanta da ɗan birni babu ruwanta da ɗan ƙauye. Ban rufekuba na faɗa muku ni Allahn da yayini in inason abu idanuna rufewa yakeyi bana ji ko gani akanshi. ( Ina maƙiyan Hamma kuna dai jin tsuntsun soyayya abinda take faɗe) Wannan tunanin saiya saisaitani, yayinda motarmu ta saitu a hanya ita kuma, mukaita ratata gudu. Bayan gushewar sakanni, mintuna, awanni sai gani a Jere Banyo cikin yardar Ubangiji sai dai galabaita da nayi. Hanyar shigowan tananan inda na barta babu abinda ya canja. Gidan Yafendona na nufa kai tsaye da sallama na shiga. Harira kaɗai matar Jatau ce a gidan itama da halama dawowarta kenan. "Jabu use kece a garin naraba da baƙin larabawa" Da kwaɓaɓɓiyar Hausarta tayi magana Nice Hari, Yafendo bata dawo tallan nono bane?" Sai naga fuskarta ta sauya daga murnar ganina izuwa alhini. "Hmmm Yafendonki tana gidanku wajen Baba Daso jikinta yayi tsanani sosai yau dan ance batasan wanda yake kanta ba ma" Daga tsayen na saki akwatina iyakar jakar hannuna da kuɗaɗena suke ciki na sake mata kyakkyawan riƙo. Sauri_ sauri gudu_gudu na dinga haɗawa dashi zuchiyata tana fat_fat harna iso ƙofar gidan. Dawowar Baffan su Boɗɗo daga kiwo kenan. Yana tsaye yana kora shanu ciki. Ni kuma na rakuɓe a gefe ina jiran garken shanun su gama shiga, mu gaisa in kuma roƙeshi inason ganin Dada. ko kallon inda nake baiyi ba har sai da shanun suka gama shigewa ya kalleni. "Kar ma kice gidannan zaki shiga. Na haramta miki shiga cikin gidannan ɓilgel (Yarinya) Dan haka kiyi maza ki bar wajennan. A guje wani saurayi ya fito yana faɗin "Baffa Dada zata mutu jijjiga take yi" Jin haka yasa na kutsa kai da gudu cikin gidan, da kuma ƙarfina dan idanuna ya rufe sai ganina nayi a ɗakin Dada a tsaye. Baffan yayi yinƙurin hanani shiga gidan, da ƙarfin tsiya na bangajeshi nayi shigewata Tozali nayi da sanyin idanuna yana tallafo kan Dada daga kwancen da take duk ya kiɗime. Wata ajjiyar zuchiya ya sauke. "Adda Jabu ashe kin dawo, gashi inzo kin samu Dada a wani irin mawuyacin hali rai a hannun Allah" Cewar Baɗɗo data ƙarashe maganarta da kuka. Hannunta na riƙe nima ina kuka ƙannena suka tawo gareni suna neman kafaɗar da zasu ɗaura kansu suyi kukansu. Mijin Baɗɗone yace. "Amaduyal dole fa akai Dada asibiti" Inajin haka nace. Anemo mota maza zamu kaita asibiti yanzu" Da sauri na ƙarasa kusa da'ita da ƙyar take jan numfashinta Yaya Hamma yana goge mata fuska da jiƙaƙƙe tsumma dan zazzaɓin jikinta yayi tsanani ainun. Sannu Dada" Carab tana jin muryata Allah cikin ikonshi saita riƙe mayafina carab kamar wacce zata gudu. Kukanmu kawai ke tashi a ɗakin har su Amaduyal suka shigo da sauri Yafendo Mahaifiyar Yaya Hamma tace. "An samu motarne?" "Ansamu malam iro zai kaita a motarshi. Ina fita shi kuma ya kawo kaya yana saukewa," Kintsa Dada akayi bayan mazan sun fita daga ɗakin. Dani da Boɗɗo ne muka tarairayota jikinmu su Yafendo na taimakawa har muka fito. Kishiyoyin Dada su kai ca a kanmu. "Ke Boɗɗo ba Baffanku yace kar a kuskura a fitar da'ita gidan ko wanne me magani ba?" Yafendo tana sharce hawaye tace. "A wannan gaɓar da Yaya Daso take buƙatar taimako, bama buƙatar sahakewar mai nagge. Mujenku Jabu" Har munje bakin ƙofar fita muka jiyo Baffa a bayanmu yana cewa "Indai kuka nuna kun fini iko da Daso, to in kuka fitar da'ita a gidannan to na saketa saki ɗaya. Ku kuma Cubu ku wuce cikin gida ƴan gatan uwa." Wani baƙin cikine ya dirarmun a ƙahon zuchiyata babu shiri na runtse idanuna, yayinda hawaye masu zafi sukaita shatatomun. Amaduyal da Hamma ne suka amshi Dada suka fice da'ita. Yafendona tana kuka tace. "Me nagge kanka ka cutar ba Daso ba. Kuma ka sani sai Allah ya tsayar daku ya fitarma da Daso hakkin zaluntarta da kayi a rayuwa. Ga gidanka nan, ƴaƴanma gaka gasu ƙila sune zasu zama jarabawarka. Sannan ka shirya tsab tunda bakwa aure dole ka dawo mata da garken shanunta." Da gaggawa muka fita a cikin gidan, Yaya Hamma ni yake kallo idanunshi sun zama jawur kamar garwashin wuta. Namadi ne yace. "Yafendo ku shigo mu tafi numfashinta tuni ya ɗauke fa" Bayan akori kurarnan muka shiga dukkanmu. Boɗɗo tana goye da wata fara kyakkyawar yarinya mai gashin fulani a kayinta. Sai dai ita uwar duk kazanta da rashin zama a waje ɗaya ya komaɗar da'ita. Kaina na sauke ƙasa ina ma Dada adda'ar Allah ya bata tsawon rayuwar da zata ji daɗi taci ribar ƴaƴa. Cikin gaggawa muka wuce babban asibitin gwammati dake cikin garin Adamawa, sun so mu tsaya a asibitin Girei, ni kuma nace mu tafi babban asibiti kawai, ai kuwa muna shiga na shiga cikin asibitin da hanzari dan neman agajin ma'aikatan jinya. Yaya Hamma da Amaduyal kuma suka kinkimo Dada zuwa wani dogon falo. Ma'aikatan jinyarnan da suka ga mu fulanin Daji ne sai suka banzatar da lamarinmu ga Dada ko numfashi bata yi, sai da muka yanki kati muka biya kuɗin gado kana suka sauraremu. Ward ɗin mata aka kwantar da Dada, sai dai bata samu gado ba, a katifa aka kwantar da'ita. Kasancewar ɗakin cike yake dam da marasa lafiya, rabi da kwatan majinyatan ɗakin fulanine. Wani dattijon likitane yazo kan Dada, dubanmu yayi yace. "Ku duka yaran majinyaciyarne?" Yafendona tace. "Duk yaranta ne, mu kuma ƙannenta ne" Kai ya girgiza yace. "Allah sarki, to ku ɗan dakata daga waje zan dubata, inna gama sai ku dawo ko? Amman zaku iya komawa gida ku ɗebo kayan jinya dan naga jikin mahaifiyar taku da tsanani riƙeku zamu yi. Ku tawo da bargo babba na rufa, dan zata iya jin sanyi cikin dare, wannan na asibiti bashi da kauri" Ni dai da ƙyar nake ɗaga ƙafata sabida yanda naga halin da Dada take ciki, da irin ƙanjamewar da tayi duk saina sare. Zama muka yi a bencin da aka tanada domin zama. Babu me cewa da kowa komai. Ni dai duk ɗagowar da zanyi saimun haɗa idanu da Yaya Hamma. Hankalinshi gabaki
Chapter 50 · 0% Book details