← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 60

Sashe 10

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gimbiya Iyabo sai wahalar da zuchiyata sonki yake ta yi. Ni na ɗauka dake zan koma Kano a matsayin matata fa, ashe abun ba haka bane. Ki tausayama masoyinki ki tsamoni daga cikin halin da kika sanyani, kaina bisa wuya, banda tuno baya. Kuma nayi imanin su Iyaa da Burodami kokodeen zasu yi alfahari da aurenmu Iyabo " Duk wannan maganar yana yinta ne cikin kyakkyawan lafazi mai taushi. Maganganunshi babu inda basa ratsawa a jikina. Sai dai kash ya makaro, dan banga abinda zai iya cemun in yarda dashi ba. Ina Mai baka hakuri ka fitar dani a zuchiyarka dan Allah. Nayi imanin a rashin samun yadda kake so a wajen matarka soja ne yasa kake son ni ka aureni" Da sauri ya fuskanceni sosai cikin kidima yace. "Wallahi bazan iya ba. Baki san irin azabtuwar da ruhina da gangar jikina suke yi bane shi yasa. Ki dena tunanin dan ban samu yadda nake so a wajen Yemisi bane na dawo gareki. Iyabo ina sonki" Ɗan guntun murmushine ya sufce mun ba tare da na shirya ma hakan ba. Zaka iya, tunda har na iya cire sonka a zuchiyata. Na rungumi soyayyar Gwadabe har kuma ya samu matsayin da babu wani ɗa namiji da zan iya bashi wannan matsayin. Kaga kuwa zaka iya, dan a baya sonka ya rufe mun idanu ta yadda bana ji bana gani. Ido da addini kaƙi fur a haɗa mu aure. Kaje ka auri sojar matarka siririya irin samburin matan da suke burgeka. Na roƙeka ka barni in auri namijin da yasan darajar ƙiba irin Gwadabe. Wanda zai dinga kammamani yana kuranta kyauna" Baki na tsuke nayi kicin_kicin. Daya isheni ma da magiya sai kawai na fashe mishi da kuka. Da ƙyar ya rarrasheni nayi shiru. "Shikenan Iyabo, zan sake baki lokaci. Ni gobe zan koma asubanci zanyi. Amman fa ki sani zan jiraki kije ki dawo sai muyi auren" Allah ya tsare ka gaishe mun da kowa da kowa. Banda matarka Yemisi, dan nayi imani batasan wajena ka tawo ba" Bai iya ce mun komai ba na yi tafiyata na barshi a wajen. Yaya Hamma kuma yana daga can gefe can gaba da inda su Daso suke tsaye. Dole ta gabansu zan wuce, hakan yasa saida na tsaya aka gaggaisa kana na Isa wajen Yaya Hamma Daso ta bini da idanu kawai. Zama nayi a gefen itacen da yake zaune, muka ƙurama juna idanu ƙur kamar zamu haɗiye junanmu. Idanunshi jawur harda kwantaccen hawaye marar yawa a cikin idanun nashi. Lumshe idanu yayi, yaja wani numfashi marar fassara a gareni, yai amfani da murya mai salon taushi da sanyi tarara wajen cewa. "Me yasaki kuka, kuma me Debisi yake nema a wajenki ne Jabu, na fahimci akwai babban sababin daya kawoshi rugarnan?" Ƙireni da idanu yayi. Nima ajjiyar zuchiyar na sauke. Na fayyace mishi ƙudurin Burodami Debisi a kaina. Na tsokata mishi ɗan labari akan cewar iyaye a baya sun haɗamu aure amman sai ya nuna baya ra'ayina. Amman na ɓoye mishi dalilin shi na ƙin nawa. Murmushi naga yayi har yanayin fuskarshi sai da ta sake. Gyara zama yayi yace. "To cika mun alƙawarina da kika ɗaukarmun akan kina dawowa zaki sanar dani dalilin zuwanki birni" Dariya na kwashe dashi, shima dariyar yake yi. Kwashe labari nayi na bashi. Da kuma dalilin da yasa zan tafi ɗin. Tashi ɗaya ya birkice har yana tsugunnawa akan guiwowinsa a gabana. Idanunshi suka cika fal da hawayen da suka kasa gangarowa. "Na roƙeki kar ki tafi Jabu ki barni. Shekara uku ban saki a idanuna ba, ai abune wanda ka iya kwantar dani. Ni zan siyar da saniyata in baki kudin a hannunki ki siya ma Dada gida, kiyi sana'arki da sauran kuɗin ki yi haquri ki janye wannan tafiyar dake shirin rabamu. In kuma ni kike so in mata duk abinda kike so a shirye nake. Yafendo uwatace, ina jin motsin sonta da tausayinta a raina. Jabu na roƙeƙi kar kiyi nisa damu, rayuka da yawane zasu jikkata" Mamaki ya kamani, to me Yaya Hamma yake nufi da wadannan kalami nashi? Ni ba yarinya bace na lura sarai tun zuwana yana ra'ayina. Amman ban tabbatarba sai jiya dana ga kishin Debisi ƙarara a idanunshi. Wannan kalamai nashi na yanzu sun ƙara tabbatarmun Yaya Hamma rainon sona yake yi. Kuma na fahimci Daso na tsantsar sonshi, Yafendo ma ta sani kuma tana fatan faruwar hakan. A duk sanda Yaya Hamma zai zo gida, sai Yafendona ta alaƙanta zuwan da Daso. Gashi matarshi ƙawarmu ce, mutuniyar kirki mai son jama'a. Kayi haƙuri ka tashi dan Allah yaya Hamma mu yi magana ta fahimta dan Allah " A tsugunne a gabana Daso ta iso ta sameshi. Numfashi ta ja tare da saurin yin turus, ganinta ne yasa ya tashi ya zauna. "Ki shiga gida Daso, ban gama magana da'ita ba. In muka gama zan rakota, ina buƙatarta tare dani" Fuu ta wuce har tana haɗawa da gudu. Tausayinta ya kamani, dan babu son da ya kai son maso wani ciwo, zafi ne dashi kamar zafin fitar rai daga gangar jiki. Mun fi awa ɗaya da rabi muna tababa tsakanina da yaya Hamma akan tafiyata. Bamu cimma matsaya ba Baffa ya fito ya korani ciki dan gaskiya dare yayi har ƙafa ta ɗauke magiya kawai Yaya Hamma yake yi tare da tambayata shanu nawa zai siyar ya bani kuɗin. Ko da na shiga bukkarmu a zaune ƙiƙam na samu Daso ta kurama aci bal_bal idanunta. Ledar gabanta ta turo gabana ina tsaye. "Ga saƙonki na wajen ɗan uwanki" Murya ba daɗi ta yi maganar. Ledar na ɗauka na zauna. A hankali na zazzaro kayan dake ciki. Kayan tea na gani, da macline da brosh, sai mayafai biyu, takalmi biyu da atampa ɗaya leshi ɗaya, sai zungureriyar wasiƙar da bani da niyyar karantawa. Biyu na raba kayannan cib na ba Daso, kayan tea ɗin kuma na ajjiye mana. "Ki riƙe abunki ni bana so" Wai Daso na yi miki laifine kike fushi dani. In akwai matsala ki sanar mun mana?" Na jefeta da tambayar ina ɗaga murya dan ta mugun ɓata mun raina ainun. "Hmmm" Shine iyakar abinda tace dani. Kayana na kwashe na mayar ko da na ɗane gado na kwanta Amman me? Sai bacci yace bani bashi. Tunanin Dada ya cakuɗe mun da tunanin furucin Yaya Hamma na ɗazu, da irin yanda duk ya kiɗime. Hasko mun da hoton Gwadabe da zuchiyata tayi sai hawaye ya soma tsiyayomun masu zafin gaske. Babala ta zalunci zukatanmu data ƙi amincewa mu rayu a tare. Nasan duk inda Gwadabe yake kuwa yana can zuchiyarshi a batse da kewata. A tsakanin ni da Daso babu wanda ya runta Washe gari sassafe ni da Hari muka gama duk aikin gida. Ina gama karyawa nai ma Yafendo sallamar ni zani gidan Baffa Musa. Acan na tarar mijin Dada yazo ɗaukarta, kuma abun haushin harta fito daga ɗaki ma suna tsakar gida. Da ƙyar na danne zuchiyata na bashi girmanshi albarkacin uwata da yake aure. Shi kuwa banza ya ba ajiyata, in kun tanka ya tanka. Har a kan fuskar Dada banga tayi farin cikin zuwan mijinta ba, fuskarta ma cike take da tsoro. Amman haka ya tusata a gaba suka tafi, ni ko da kuka na fice a gidan na dawo gida. Na tarar da su Yafendo sai dafa madara suke yi, taga na shigo da kuka kamar karamar yarinya dai. "Jabu lafiya kaddai Adda Daso mutuwa tayi?" Ganin yanda duk suka ruɗe suka yo kaina yasa na yi musu bayanin dalilin kukana. Yafendo da Hari ne su kaita rarrashina dai haka. Gaga_gaga haka rayuwa tai ta tafiya. Ko wacce rana kafin faɗuwarta sai hawayena ya zuba. Dada jikinta ya warware har ta soma fita tallar Nono. Sabida tsananin tausayinta yasa nake binta wajen sana'ar nonon nata. Sai tayi zamanta a gefen rumfa. Ni kuma ni zan zuba Nono in kai, in je in kwaso ƙworena. Munayin hakan ina jin daɗi itama tana jin daɗin hakan, dan karayar tata bawai ta warke sumul bane. Ƴan tsegumi suka sanarma da Mijin Dada ai ana ganinmu tare. Kwatsam muna kan siyar da Nono sai gashi ya zo dan ya zama ganau ba jiyau ba. Da ganinshi Dada jikinta ya soma mazari. Kwafa yayi kawai yaa bar tashar fu. Ranar dai haka muka ƙarashe kasuwarnan cikin taraddadi. Wannan shine silar da na dena bin Dada wajen sana'ar tata. Ta ɓangaren Hamma kuma shaƙuwar data shiga tsakaninmu shakuwace ta ban mamaki. Banda Dada da ƙannena,shi kaɗai nake gani ya yaye mun damuwata da kalamanshi masu sanya kuzari, gashi kullum sai naci tsire da lemun kwalba, Abunka da ƙauye tuni ƴan tsegumi suka tseguntama Hama ana ganin Hamma kullum da wata mace har dandali. Dan babu ranar da bama zuwa dandali, da Hama ta gane ai nice mijinta ke ƙwaƙwa, duk wannan far'a da haba_haba da take yi muni sai du ta dena. Har ta kai ta kawo ta dena kulani, ko na gaisheta ma da kyar take ka da baki ta amsa, harma abu ya zame musu rigima a tsakaninta da Boɗɗo. Daso kuwa tsakanina da'ita takun saƙane, taƙi ta yarda ba soyayya muke yi da Hamma ba. Tunda duk shakuwarnan bai taɓa cewa yana sona ko zai aureni ba. Ita kuma ma a lokacin har Baffa ya san da zaman Manga. Dan ance mishi zuwa kaka ya turo manya a gama komai. Ita kuma tayi tsalle ta dure kan cewar Allah ya kasheta bata son Manga. Baffa kuma yace ya bata kwana talatin ta fito da mijin aure in ba hakan ba ya aura mata Manga. Ni dai sai shirin tafiyata na sanya a gabana, nayi watsi da iskantakun Daso. Lokacin da labarin tafiyata ya shiga kunnen Dada bata ja ba, sai ma fatan samun nasara da tai mun. Baffa Musa ne yaso ya turje, amman su Dada suka haɗu suka tausheshi. Yaya Hamma dai ko hirar tafiyar tawa nayi mishi sai ya gimtse fuskarshi shi yasa ko zancan ma ni bana yi mishi, shima baya so, yayi juyin duniya in janye wannan tafiya. Ni kuma fur naƙi amincewa, har shanu biyu ya siyar da daddare sai ga kuɗi dumus nera na gugar nera har nera dubu ɗari cib Miƙo mun yayi nasa hannu na amsa
Chapter 10 · 0% Book details