← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 60

Sashe 13

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haÉ—e da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*
[8/8, 3:11 PM] +234 803 969 6400: NAMA YA DAHU....
ROMO ÆŠANYE....
LITTAFI NA BIYU
3

A hankali na isa na zauna a gefenshi. Idanu kawai ya zuba mun sai naga yana kaÉ—a kai.. Kwanon abincin na tura mishi gabanshi.
Ga Amala abincin bugun gaban yarbawa da fatan kana iya ci" Dariya yayi mun yace.
"Tun kafin ki zo duniya nake cin Amala. Ai nayi zaman oghomosho, sarkin garin Oghomoshon ma bafulatanine. Kinsan tun shekaru aru aru yarbawa suke a matsayin bayin Fulani. Hakanne yasa auratayya tayi ƙarfi a tsakanin Yarbawa da Fulani. Sai kiga bafulatani sak amman sai kiji bai iya ko fillancin ba sai yarbancin. Haka sai kiga beyerabiya na zagargaza fullanci. Ki duba Dada yanda naga da yarbanci zalla take magana dake." Ajjiyar zuchiya na sauke nayi dariya. Shima dariyar yayi ya soma kantara lomar Amala miyar ewedu sai dalali take yi a hannunshi. Sai da ya cika bakinshi da ( phomo) ganda kana yace.
"Ni ko kibar matan yarbawa na birgeni, kuma Allah ya zuba musu sura masha Allah ." Dariya nayi sosai nace.
Ku da kuke da farare kuma siraran mata masu gashi" Dariyar shima yake yi mun.
"Jabu kenan. Ai cikakkiyar mace Æ´ar duma_duma daban take da siririya. Shi kyau a sura yake ba'a fuska ba ai. Bance sirara basu da kyau ba. Kuma bance yarbawa sun fi filani kyau bane. So nake ki fahimta, wani namijin mai sha'awar haÉ—a shinkafa da doya ne. Wani kuma taliya kaÉ—ai ta wadatar dashi" Cikin karantar yanayinshi nace dashi.
To kai a wacce matsayar kake ne?"
"Koma a wacce nake zaki sani ne" Cikin raha dai mu kaita hirarmu har ya kammala cin abincin nashi. Kana nayi mishi sallama na tafi.
Sai zuwa washe gari na haɗu da su Burodami kokodeen da su Burodami Debisi. Kuma na zagaya gidajen nasu naga yaransu, na gaisa da matansu. Yemisi dai babu yabo ba fallasa, dama ya lafiyar kura ballantana tayi hauka. Haka dai akaita mana shirin tafiya, dan har munje anyi mana gwaje_gwaje iri da kala a asibiti. Ana washe gari zamu tafi ko bacci na kasa yi dan dadi, da kuma wata fargaba data lulluɓeni. Burodami Debisi, da Yaya Hamma, da Hafizu sune abokan rakiyar tamu har zuwa filin jirgi, ko ince ɗakin jira. Gefe guda muka keɓe da Yaya Hamma da jikinshi naga har rawa yake yi, idanuna a cike da ruwan hawaye. Naso Yaya Hamma ya furta mun kalmar so kafin in tafi ya jaddadamun matsayina a zuchiyarshi. Amman kunya da ƙauyanci ya danneshi. Haka dole mu kai sallama ba tare da naji inda soyayyarmu ta kwana ba. Ko da muka shiga cikin Bus ɗin da zata kaimu gaban jirgi ai sai na sake fashewa da kuka, ina tunano fuskar Yaya Hamma, da yanda yake ta aukin jaddadamun alƙawarinmu. Burodami Debisi kuwa kamar ya shaƙo Yaya Hamma ya rufeshi da duka haka yake ji. Gurin dake ɗaure a shintsiyar hannunshi daya bani na sake damƙewa a hannuna.
Yau ni Iyabo gani a cikin jirgin sama zai tashi damu zuwa ƙasa mai tsarki. . Hukunci sai mai tsaga idanu. Allah sarkin girma in ji kishiyar mai duwawu.

MaraÉ—i

Gwadabe:.
Auwala bai dire Sabitu a ko ina ba sai a gaban malam, ga almjirai cike da wajen. Tun kafin Malam yayi magana. Baba Asshi ta fito babu ko mayafi a jikinta. Kallon da taga gardawan Malam Magaji na yi mata ne yasa ta koma daga zaure.
"Auwala wannan wanne irin riƙo kayi mishi kamar ka kamo barawo" Malam ya girgiza kanshi yana bin ƙofar zauren da kallon baƙin ciki. Baba Fhatsima ce ta fito saye da katon mayafinta ta jaye Hadiza tare da cewa.
"Koma me ya faru a barshi a tattauna a cikin gida. Auwala cikashi, kai kuma Sabitu jeka abinka. Allah yayi muku albarka baki ɗaya. Hadiza ta jawo suka shigo zauren Baba Asshi ta harareta sama da ƙasa tace.
"Ni nawa yaran sai ki tsine musu ai, tunda naki kika sama albarka. Ni na ji jaraba fa, kun bi kun sani a gaba Fhatsima kin hana mun jin daÉ—in aure" Baba Fhatsima Taso tsaiwa ko wacce zata hanata bacci ta feso mata. Auwala sai ya kama hannunta suka shige. Su kuma su Gwadabe suka wuce barayinsu dan watsa ruwa su ji daÉ—in jukkunan nasu. Gwadabe yana wankannan yana tunanin me yasa gida in da mace sama da É—aya ake yawan samun rabewar kai ne. Ta ina kuma matsalar tafi rinjaye tsakanin matan, ko uba da yake zama majingina a wajen mata da yaran gida.?
Da wannan tunanin ya fito. Fitowarshi ke da wuya Ine tazo ta yi kiransu gabaki É—aya harda Gwadabe izuwa turakar Malam. A babban falonshi duk suka gurfana Malam ya soma magana da cewa.
"A wannan karon duk macen data nuna zata kawo mun rabewar kan ƴaƴa ni zan iya sallamarta ta tafi gidansu. Allah yana gani daidayya ina bakin ƙoƙarina dan ganin nayi adalci a tsakanin matana harma da su yaran nawa. Ke Fhatsima kece Babba a gidannan na faɗa ba tun yanzu ba zan haɗe kan yarana da matansu dukka a gida ɗaya dan su rayu tare yaransu su cuɗu da juna ta yadda zasu shaƙu da junansu. Wannan magana tamkar a rubuce take ba fashi. Duk da Asshi ta nuna ita bata bukatar a haɗe yaranta dana Fhatsima. Harma Jamilu ya goyi bayanta a kan hakan. Rikicin Sabitu da Hadiza ne yasa na dawo da wannan maganar baya. Nasan ko wacce nayi mata bayani ita kaɗai Amarya malam uwar kissa ta dubeshi da taushin murya tace.
"Allah shi gafarta malam ni nawa yaran da suka kasance ƙananu ya za'ayi dasu to?" Dariya malam yayi cikin so yace.
"Amarya harda su Rabi'u za'ayi wannan ginin. Su kuma mata _matan da zasu yi aure ko wacce zan bata kadara a matsayin kyauta, kanana marasa aure kuma sai in ajjiye musu zuwa lokacin da Allah zai ƙadarta su yi aure. In kuma ta Allah ta kasance a kaina sai a danƙa musu baya cikin gado na basu halak malak, hatta ginin da Shi Tasi'u zai musu baya cikin gado na mallakawa kowa halak malak harda Gwadabe dan gudun kar in kwanta dama tashin tashina ta tashi. Dan kuna ganinane kuke samun damar faɗace_faɗacen nan da kuke yi. Wallahi duk ranar da za'a wayi gari bana doron ƙasa zaku yi dana sani, za kuma kusan mahimmancina. Zaku iya tafiya" A lokacin dai jikkunansu duk ya mutu, amman kowacce tana jaye ƴaƴanta suka shige ƙurya sai labari yasha banban. Wannan kyauta da malam ya furta bata cikin gado itace ta tayar da ƙayar baya, baƙin ciki da hassada ya shigo, musamman ga wadanda basu da damar cin tudu biyu. Haka bikin yaran gidan yaci gaba da matsowa, sai shirye_shirye aketa ta faman yi kowa ta ciki na cikinta. Yaya Tasi'u da matarshi Anty Badi'at ba zama, dan ita ta shiga cikin nijer ta siyo kayan gadajen Amare da kayan kitchen ita da Amaryar Malam. Kwana bakwai da Baba Magaji ya ba Gwadabe ta cika, Baba Magaji baice komai ba, shima Gwadabe yaƙi cewa komai, zuchiyarshi kullum cikin taraddadi take kawai, har aka tsunduma sha'anin biki dai Baba Magaji na kallon Gwadabe ya zuba mishi idanu.
To al'adar auren Maradi ya banbanta da al'adar aure a Najeriya ƙasar hausa. Su yanda suke bikinsu shine.

*KAN GORO*
Shi yanda ake yinshi shine. Iyayen Ango zasu tawo da goronsu a jarka za'a daddaleshi, yana danganta da yanayin karfin miji. Zasu tawo da balis ( Akwati) wasu suna zuba kaya a ciki, wasu kuma basa zubawa, zasu tawo da kuÉ—in sadaki, da hidimar girke_girke rigi_rigi.
Iyayen Amarya maza su kuma zasu zauna a manyan taburmai domin tarbar iyayen ango da wannan kaya. Iyaye mata a gida kuma zasu yi girki na alfarma a fito dashi. Anan za'a tsayar da lokacin Aure da bai haura wata guda ba, wasu ma sati guda ya danganta. To su dangin Ango zasu tafi da wannan gara ta dafaffen abinci tare da tsayayyen lokacin Aure.

*LIFARAN*
shi kuma lifaran ( Anko) ake nufi. Daga kawo wannan kayan aure da kuÉ—i. Dangin Ango, da dangin Amarya sai su fidda Ankon biki.

*LALLE*
Amarya zasu zauna zaman lalle na kwana biyu ita da ƙawayenta.
Chapter 13 · 0% Book details