← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 60

Sashe 21

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Hambali ya gano a zaune ya jingina da garu, Babala tana zaune a kujera, Auta na ƙasa a gefen ƙafar Babala. Ɗakin Babala yasha gyara kujerunma sababbi fil, hatta labule sababbi ne aka zuba. "Babala lafiya na ganku kunyi jigum? "Hmm lafiya ba lafiya ba Gwadabe. Kaine a tafe sassafe haka?" Babala ta bashi amsa. Waje ya samu ya zauna, Babala ya soma gaisarwa, kafin Yaya Hambali. Babu yabo babu fallasa ya amsa, dan ko juyowa ya kalleshi bai samu wannan darajar ba. Auta ce tace. "Yaya Gwadabe sannu da zuwa" Jiki a mace yace. "Yauwa Auta, ya mai gidan naki?" Shiru bata amsaba, Babala tace. "Yaya ka baro su Yaya Magaji, da fitinannun matanshi marasa daraja?" Ɗan murmushi yayi, a ranshi yace. "Babala ba zata canja ba" A fili kuma yace. "Malam yana Saudiyya shi da Baba Fhatsima yau kwanansu biyar ma. Duk kowa yana lafiya, sunce ma in gaisheki" Mikewa tsulum Yaya Hambali yayi. "Babala ki gama dashi na dawo in kum gama. Dan bazan iya zama inuwa ɗaya da wannan kangararren yaron marar jin maganarki ba" Yana gama faɗin haka ya fice, Gwadabe ya bishi da idanu galala. Babala ta amsa mishi da cewa. "Kangararre fa, yaro aita nuna mishi annabi yana runtse idanu. Ni kaga banyi ma tunanin zai sake zuwa dubamu ba" Yaya Hambali dake tsaye yana sa takalmi yace. "Sabida Bara'u ƙanin ubanshi yazo, da wannan ɗan nashi me cakuɗe da jinin yarbawa ai" Yana gama kunna Babala yayi tafiyarshi. Ai fa nan Babala ta inda take shiga ba tanan take fita ba. "Shima Bara'un ashe kangararrene irinka?. Yasa wannan yaro ɗan wajen beyerabiyar tsohuwar matarka a makarantar boko Har gida naje na samu Sakina matarshi nace da'ita ina son ganin shi Bara'un. Wallahi ko da yazo na zayyanama Bara'u bana son wannnan ɗa yayi boko. Yaronnan ya shafa toka a idanunshi yace in yi haƙuri dole a yanzu yara suna buƙatar ilimin boko. Ko da wanku ya shiga zancan ƙarshe ma Bara'u ce mai yayi ai shima yaranshi na zuwa boko dole shima wannan ɗan yarbawa yayi boko. Zan yi maganinku dukka, har wajen uwarshi naje na kai ƙararshi ai" Gwadabe dai yayi jim yana saurarenta sai zuga faɗa take yi. Sai da ta gama tayi mai isarta yace. "Ayi haƙuri dai Babala dan Allah." Hannu yasa a ajjihu ya zaro kuɗin da Yaya Tasi'u ya bashi ya kawo mata." "Ga wannan inji Yaya Tasi'u yace a kawo miki, matarshi ma ta bada tsaraba" Hannu tasa ta fisge kuɗin da ƙarfi. Gwadabe dai in da sabo ya saba. Tsarabar daya tawo dashi duk ya cicciro ya baza a gaban Babala. Yadinga mata bayanin mutanen gida da za a rarrabama. Ya ware nata dana Auta dana Yaya Halima. "Banga na yayyenka su Fodiyo ba, balle nasu Da u. Me kake nufi kenan Gwadabe?" Sauke kai yayi ƙasa yayi jim kaɗan. "Kiyi haƙuri nan gaba in zan tawo zan tawo musu dashi, amman yanzu kam babu nasu" "Baka isaba dan ubanka. Yayanku meye a rayuwarnan bai yi maka ba? Ya ciyar dakai ya shayar dakai, yayi maka sutura, ya goyaka a bayanshi ya kai ka makarantar allo data boko da guminshi. Yau sabida wata ƴar iskar beyerabiya shine kake shirin yanke halaƙarka da ƴan uwanka maza? To ni zan tattare duk abinda ka bani in basu bana buƙatar ka sake kawo mun komai madamar ba zaka baiwa ƴan uwanka ba. Kasan ai sunfi ƙarfinka ta ɓangaren arziki. Yanzu haka duk mota suke ja har Da'u. Jebeka kai a fige a bushe, sai uban naɗin buzaye a ƙaron kanka. In baka yi wasa ba ma a haka zaka ƙare Gwadabe" hawayene suka gangaro da gudu zuwa kan kuncinshi. Ya kasa furta daidai da kalma. "Bama son duk abinda zai fito daga hannunka Gwadabe. Munfi ƙarfinka,tun da majina a hancinka nake juya kuɗi. Da wasa kar kayi gigi ƙafarka ta tako gidana bana son yin hulɗa da kai har gaban abada mitsiyaci" Cewar Yaya Hambali dake tsaye a dokin ƙofa, yaji dukkan tattaunawar Gwadabe da Babala kan tsaraba. Babala ta turo ma Gwadabe tsarabar da yayo mata dana su Yaya Halima. "Gashi dani da ƴaƴana bama buƙatar komai daga gareka. Wannan dai da aka baka saƙo ka kawo mun na karɓa. Matan gida kuma kaje ka rarraba musu da kan ka" "Babala kiy mun rai kiyi haƙuri. Yaya Hambali kaima kayi haƙuri. Duk tsawon watanninnan tsarabarnan nake ta siye ina jefarwa. Iyakar abinda kuɗina ya iya siya kenan." Ya faɗa cikin sigar rarrashi. Kamar sake tunzura Yaya Hambali yayi ma. "Shine nace maka kaine mitsiyaci Gwadabe. Dan wannan duk tsarabar bata wuce in siyeta a take in bayar da'ita sadaka ba" Babala tace. "Faɗa mishi dai. Baka ga yanda arzikinshi yaci uban nada bane. Gidanshi na kano an ruguje ya dawo gidan bene Ai kaga yanda gidannam ya dawo ko gidan mai gari albarka, ga babbar motarshi a ƙofar gida" Gwadabe yana zaune suka ƙare mishi tanadi tsab, ko tari baiyi ba, idanunshi sun kaɗa sun zama jawur. Yanzu iyayenmu sun zama abinda suka zama. Nuna fifiko akan ƴaƴansu masu sukuni akan waɗanda su Allah bai basu ba. Miƙewa yayi da tsarabar matan gidan ya kaima Goggo Yabi yace ta raba a tsakankaninsu. Bayan ya dawo ɗakin Babala ne tace. "Ya batun Aure, ko kanaso kace ba zaka sake aure bane tunda ka rabu da ƙanwar uwarka Iyatu? Ga Laila tayi aurenta, yarinya da kyanta Allah ya taimaketa ta auri mashahurin ɗan siyasa, baka ga gidanta ba." "Aure zanyi Babala. Baba Magaji ya haɗani da ƴarshi Bazawara Hadiza harma mun sasanta kanmu, Lokaci kawai ake jira. Kuma..." Ta katseshi da cewa. "Kuma me? Dama shi Yaya Magaji abinda yake so kenan shi yasa ya goyi bayanka ka bijere akan auren Laila, ashe tashi ƴar yake ma tanadin talaka kamarka? Na lura so yake ya yanke zumunci damu, domin matsawar Iyatu taji wannan batu zata yi fishi. Dan kawai Allah ya jarabceta da ɗiya me ciwon sata." Nan Babala taita jujjuya zancan. Gwadabe na son ya faɗa mata batun ƙanwar Tamu, amman tsoro ya hanashi, dole ya ja bakinshi ya tsuke. "Babala ni zan shiga ciki in yi wanka. Jazuli yana ciki ne?" Ya tambaya da dariya a ƙoƙarinshi na danne damuwar data addabi zuchiyarshi. "Ka dai je ɗakin nasan a buɗe yake. Wake zama baya neman arziki? Jazuli yana Kano Yayanku ya buɗe mishi shago, ya kan dai shigo Takai lokaci zuwa lokaci" Kai kawai ya girgiza ya ɗauki jakarshi yana shirin fita Babala tace. "Kazo ka kwashi tsiyarka fa Gwadabe" Fita yayi tare da cewa. "Ni lada nake nema. Ko zubarwa kikayi daidai ne Babala" Har yabar barayin bai dena juyo sababin Babala ba. Wanka yayi ya shiga ɗakin Jazuli ya zauna a bakin katifa yana mai cike da zulumin irin furucin da Babala ta daɗe tana jifanshi dashi na rashin arziki. Gashi duk abinda yasa a gaba baya samun nasara sam. Ko haƙon zinari ya shiga rijiyar zaiyi. To sai dai fa yasha wahalar banza. Sau huɗu ya taɓa samun dutsen zinare ƙananu suma. Amman Auwala da Mammada sau nawa suka samu, sai dai fa in an siyar su ɗan tsakura mishi na kashewa. Dan aikin haƙan zinare ba aiki bane na wasa, balle har wanda ya haƙa ya baka kuɗi me yawa, aikine mai cinye ƙarfi da ƙuruciya sosai. A hakanma yaga ƙoƙarin su Auwala da suke sammishi wani abun. Dan kullum fa a cikin shan ƙwayar bature suke maganin ciyon gabɓai. Ga auren mata biyu a gabanshi, bai tara ba bai ba wani ajjiya ba. Atampa biyu kawai ya ajjiye. Auwala kuwa ya gama haɗa kayan akwatinshi tsab, takalmane kawai ya rage. Iska ya furzar a bakinshi a fili yace. "Anya bazan fito in faɗa ma Tamu gaskiya ba kuwa? Ni bani da ƙarfi, kar in auri mata biyu in zo in gaza wajen kulawa dasu. Yana da kyau Tamu yasan yanayin samuna fa. Amman bari inje in samu Bara'u inji ta bakinshi" Zuruf ya miƙe cikinshi ya wani juya mishi. Sai lokacin ya tuna ashe fa baici abinci ba ma. A ƙofar gida ya tarad da Yaya Hambali da abokinshi Inusa yaron mai gari. "Gwadabe kaine a garin namu?" Ya tambeshi da fara'a. Fuska Gwadabe ya sake ya miƙa ma Inusa hannu suka gaisa. "Ciwo kayi ne Gwadabe, kai kaga yanda duk ka faɗa kuwa?" Kai Gwadabe ya sosa kana yace. "Sha'anin rayuwa ce kawai Yaya Inusa. Yau da gobe bata bar komai ba, a dai samu a adda'a" Girgiza kai yayi cikin tausayawa yace. "Allah ya rufa asiri. Zamu yi magana da Hambali muga me ya dace a taimaka maka dashi" Buɗar bakin Yaya Hambali yace. "Da za a taimaka mishi da bama zaka ganshi a haka ba. A lokacin da naso in taimaka mishi ai ƙi yayi. Inusa in dai kanaso zumuncinmu yaci gaba, to kar ka sake ka taimaki Gwadabe da sisin kwabo" Sai wani huci yake yi, yana hura hanci. Yaci jar shadda dinkin tazarce, idanunshi cike dam da farin kwalli. Murmushi Gwadabe yayi kawai ya wucesu. Tafiya kawai yake yi, amman baya ma iya ganin gabanshi. Tunanin shi kuwa shine. Anya Babala itace ta tsugunna ta haifeshi kuwa? Anya su Yaya Hambali ƴan uwanshi ne su kuwa? Sai dai yana tuna yanda suka taso cike da kulawar Yaya Hambali, ya kuma haɗe kawunansu duka, cikin soyayya yake musu komai. Har wanka yayi musu da hannunshi. Gashi da yawan taimako, hakannema yasa gashi duk ya jaye ƴan uwan nashi, kuma dukkansu da bazarshi suke taka rawa. Daga sanda ya Auri Iyabo zuwa yanzu yana ganin ƙiyayya. Sun kwana basu ci abinci ba, yaje wajen ƴan uwanshi ya bisu kab aka rasa wanda zai taimaka musu. Hawayene yaji suna zuba a idanunshi shaa. Da sauri ya goge yana dariya kamar mahaukaci. Ko da yayi salllama a gidan Bara'u, Sakina ce ta fito. Tayi mamakin ganin irin ramar da Gwadabe yayi. Bayan sun gaisa ne take cewa. "Gashi yana gona. Amman bari insa Shehu yayo kiranshi. Ka shigo daga tsakar gida" "Nagode Sakina" A sanyaye ya shiga tsakar gidan. Ya zauna akan taburmar daya samu a shimfiɗe a baranda yayi saroro dashi. Ruwa Sakina ta kawo mishi, sai da yasha sannan yace. "Ina yaran ke kaɗaice a gidan?" "Sun
Chapter 21 · 0% Book details