← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 60

Sashe 58

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau monday tushen aiki. Ayau Angwaye zasu koma bakin aikinsu kasancewar yau satinsu guda tim da tarewa a É—akunansu. Wanda yayi dai_dai da kwanan Gwadabe huÉ—u a É—akin Shafa.
Tun asubar fari Gwadabe ya hura huta ya ɗaura ƙatuwar tukunyar maganinshi, yana dawowa Sallah ya sauketa. Shafa ta juye mishi ruwan wanka, shi yana shirin fita kasuwa ita kuma ya kwatanta mata yadda zata ƙulla mishi maganin nashi. Tana girkin safe tana ƙullin magani. Gwadabe shi kuma ya shirya tsab cikin kayan nema ya fito ya kama ɗaurin magani. Ita kuma Shafa ta samu damar kammala haɗa kayan karin kumallo a babban tire, ta shiga ban ɗaki ta watsa ruwa. Cikin kanƙanin lokaci ta shirya cikin doguwar rigar shadda mai ruwan ƙasa tasha surfana.
Tana fitowa Gwadabe ya kalleta yace.
"Kinyi maƙurar kyau Shafa. Ki kai abincin ɗakin Hadiza nima ganinan"
"Godiya nake yi mijina na kaina" Murmushi yayi mata yana son sanyin halin Shafa sosai. Tiran ta É—auka ta shige É—akin Hadiza, bayan matar Sabitu ta ja dogon tsakinta.
"Gwadabe kayi da jiki bakwai harta gota, Mammada fa harya fice yana jiranmu a ƙofar gida, kai kuma naga sai yanzu ma zaka karya" Cewar Auwala daya fito cikin shirin fita kasuwa"
"Bari kawai in musu sallama sai in fito mu tafi. Ko Æ´ar tsala naci acan in munje."
Miƙewa Gwadabe yayi tsaye da sauri. Bokitin maganin ya kinkimo ya fito dashi tsakar gidan, ya ajjiye tsumman da yake gammo dashi, ya samesu a ɗakin Hadiza.
Itama Hadiza taci ado yau da Atampa riga da zani, jakarta da mayafinta yana gefenta itama hutun da makarantar su ta bata ya ƙare yau.
"Barka da Safiya yallaɓai, lafiya ka tsaya a kanmu sai binmu da kallo kake yi?" Cewar Hadiza da take magana a ɗan shagwaɓe. Yana matuƙar jin daɗin shwagwaɓar Hadiza da yadda take taimakonshi akan shimfiɗa wajen tayashi cimma manufa. Saɓanin Shafa da take kwanciya kamar ruwa sai inda aka juyata"
"Kunyi kyaune. Nake mamakin ni Gwadabe mahaƙin gwal, mai saida maganin basir nine da mata fella_fella haka? Allah nagode maka.
Kuyi haƙuri abincinnan bazai ciyu ba. Su Auwala ni suke jira, saina dawo zanci abincin acan.
Hadiza yau zaki koma bakin aikinki kema ko?"
"E hakane. Ni kaina jiranka nake yi dama ka shigo in muku sallama, inna tsaya yin breakfast a gida zanyi latti. To acan nake karyawa ina tafiya da filas É—in tea da abinci"
"To Shikenan tunda Hakane. Na soke karyawar safen. In yaso da daddare ma dinga haÉ—uwa, ni na tafi. Shafa ki yi haquri ki koma É—akinki da abincin"
Sam Shafa bata ji daÉ—i ba. Tana lure dama Hadiza bata son cin abincinta, kuma ita ta duba ta hanga bata ga ta inda Hadiza ta fita tsafta ba. Ba dai tasan irin daÉ—in girkinta ba wannan, tana jiran ranar girkintane taci taji"
Tiran abincin ta É—auka.
"To Yaya sai kin dawo"
Tasa kai ta fice. Tana fita Gwadabe ya jawo Hadiza dake tsaye jikinshi, ya cusa kanshi a kirjinta yana ajjiyar zuchiya.
"Uwargida a matse nake dake fa sosai. Ina mararin juyowar girki bazan ɓoye miki ba"
Idanu ya lumshe yana hasaso daren ƙarshe da yayi a ɗakin Hadizan.
Murmushi tayi mishi tace.
"Kamar yaune lokaci zai zagayo, harma ya wuce. Haka zakaita zagaye har abada, tunda burinmu mu dauwama tare da kai har abada" Ba shiri dole ya saketa ya fice, ta biyo bayanshi suna dariya.
Gwadabe ya suri bokitin maganinshi ya fita. Auwalane ya ɗaura mishi aka suka nufi hanya, Allah cikin ikonshi kafin su isa inda zasu hau abun hawa Gwadabe yana taɓa ciniki babu laifi. Acan inda ake aikin haƙon zinare kuma tas maganinshi yake ƙarewa sakamakon maganinshi yana da kyau, kuma masu saye sun shaida yana musu aiki. Gashi yana gaba_gaba wajen haƙon zinare, Gwadabe namijine mai zafin nema da zafin nema babu wasa a lamarin aikinshi.
Haka rayuwar dai taita garawa yau mun wayi gari Gwadabe ya gama kwananshi na ƙarshe a ɗakin Shafa, ya fita da safe inya dawo a ɗakin Hadiza zai ya da zangonshi. Sannan yana fitowa Yaya Tasi'u ya bashi takaddar samun aikin Shafa, a wani asibiti zata dinga ba da kati. Gwadabe yayi murna sosai kuma ya yaba da ƙoƙari da kulawar Yaya Tasi'u gaya.
Mutuniyarku Hadiza yau wayar garin tayi tamkar anyi mata bushara da gidan aljanna dan daɗi. Tana cikin farin ciki ta tafi makaranta. Hatta ƙawayenta malamai sun gano farin cikin da take ciki.
Sadiya uwar zolaya, bayan Hadiza ta fito daga aji ta dawo ofishin malamai dan tanaso ta karya kafin lokacin komawarta wani ajin yayi tace.
"Waini Hadiza ko Gwadabe yayi muku wata gagarumar kyautace yau ɗinnan? Hatta kwalliyar da kika caɓa naga ta dabance, harfa taku kika canja." Dariya gabaki ɗaya matan cikin ofishin suka saka. Hadiza saida ta tura wainar ƙwai bakinta kana tace.
"Sharri dai da sa ido Chima in ba haka ba wacce canja tafiya nikam zanyi? Kawai dai yau nice da girki shine naketa nishaɗi. Kuma inata tunanin wanne irin abinci zan tari Oga dashi, tunda mu kai aure baici abincina ba, in banda farar shinkafa dana dafa muka ci da Miyar da Balaraba ƴar ƙanwar Baba ta soya. To Ku bani shawarar abinda zan girka, da irin wankan da zan fella Sadiya kune masu kishiya, bani labarin yadda kike tashin kan abokiyar zamanki ran girkinku?"
Wata dariyar mugunta Sadiya ta shiga yi har tana tuntsurawa.
"Wallahi har kin tuna mun da Safara'u. Ranar girkina sam bata da sukuni, kalar tausayi take zama. Gashi Sanusi shi ƙa'idarshi a turakarshi muke zuwa cin abinci. Gaskiya kusan kullum da jan idanu take fita in ranar girkinane" Hadiza tayi shewa tace.
"Shegiya ƙawata. Bani sirrin mana nima in ƙara da nawa. Kinsan Allah inason mijina sosai, kuma in na kalli Shafa a kullum sai inji kamar ma in shaƙeta uban kowa ya huta. A kallon da nayi mata lokacin biki, banyi tunanin zafin kishina zai iya sauka a kanta ba, danni na raina yanayinta kuma nasan ƴar ƙauyece duk da tayi karatu. Ashe wallahi kallon tsoro nayi mata itama akwai kaya. In ta shawo wankannan suka shigo mun ita da Gwadabe kuma naga hankalinshi a kanta. Kinsan Allah kamar in zazzagama kaina fetur in ƙone haka nakeji dan kishi."
Dariya suka kwashe dashi. Barira tace.
"Ni uwargidanmu batta da son girma amman bata da damuwa. Amman Nabila itace take neman É—auramun hawan jini a baya. Sai da Sadiya ta bani maganin damuwar da Nabila ta so É—auramun. Shawarwarine nagartattun da dabarun yadda zaki zama wata ta daban a zuchiyar oga, da kissar danne kishi. Kinga da É—an abu kaÉ—an Nabila zata yi, kawai sai inji kishi kinsan Allah bana sanin sanda nake lailayon mata uwar ashariya. Kinga ina girma a wagga lamari?"
Dariya suka kwashe dashi. Ƙararrawa aka buga dole Hadiza na jin daɗi ta tafi aji dan ba yara darasi. Data dawo suka ɗaura, Sadiya ta zauna ta karanto mata abubbuwa masu girman gaske ( Sannu a hankali zaku jisu a aikace cikin labarin) Waɗannan maganganu su suka sake buɗe kan Hadiza tayo farin ciki gaya. Ana tashi ta wuce wata ƴar ƙaramar kasuwa dan yin cefanen naman rago ta siyo, sai bushasshen kifi, da cefanen tumaturi da su tattasai, attaruhu. Albasa an kaita dashi kusan rabin bihu ma. Sai kankana kwallo daya da lemun tsami manya na nera hamsin.
A gajiye ta shigo gidan, babu kowa a tsakar gidan ɗakinta ta buɗe ta shiga. Ta ɗan kwanta ta huta bacci ya ɗebeta zuwa la'asar. Da sauri ta miƙe ta fito, daidai Shafa ta fito daga banɗakinta da halamun alwala ta ɗauro"
"La Yaya yaushe kika dawo?"
"Na dawo bayan azahar, nayi tunanin ko bacci kikeyi shi yasa ma ban tasheki ba ni kam. Kinga bacci nayi yanzu na farka" Shafa tace.
"Ai kuwa bacci nima na tashi yanzu. Dan ɗazu naso yin baccin amman an ɗanyi rikici a gidan akan shanya abinda ya hanani baccin kenan" Haɓa Hadiza ta riƙe.
"Akan shanya kuma, to dawa dawa su kai faÉ—an?" Shafa tace.
"To matar wancan ɗakin na gaba can, da matar ɗakin dake kallo nakine. Sunyi faɗa sosai harda fashe bokatai fa" Baki Hadiza ta taɓe.
"To Allah ya kyauta, bari inyi sallah " Tayi wucewarta banɗaki, Shafa itama ta shige nata ɗakin. Tana idar da Sallah ta sauya kayan jikinta zuwa wata ƴar doguwar riga mai sauƙi haka, ta fito domin soma girki. Matan gidanma kaf ɗinsu suna kitchen anata ɓuruntu. Gida ya kaure da ƙamshi kifine, kazane kowa dai da abinda yake girkawa. Sanwar miya Hadiza ta tsayar. Tana tsintar waken da zata zuba a miyar. Baba Suwaiba ta fito tsakar gidan tana sababin danme za'a hana surukarta shanya.
"Ke Fatima ki fito fitsararriya kwashasshiya fito inji me kika taka" A madadin ita ta fito sai Sabitun ya fito da kanshi. Rashin kunya yayi mata, dama basa ganin kowa da gashi a gidan. Nanfa rikici ya ɓalle rikicin da sai da Malam da Baba Fhatsima suka yo tattakin shigowa. Daidai Baba Suwaiba tayi ɗamara ta nufi Sabitu da duka.
Chapter 58 · 0% Book details