← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 60

Sashe 39

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

IYABO: Ina kan sallaya hannu da kaina a sama ina roƙon Allah ya kawo mun sanadin komawata ƙasata najeriya kar in mutu a wulaƙance a inda rayuwata bata da amfani. Yaya Hamma na tuno da ƙoƙarin da yayi akaina domin in haƙura da tafiyar naƙi. Haka zalika Burodami Debisi yayi ƙoƙarin hanani tafiyarnan idanuna sun bushe gani nake tafiyar itace mafita. Ashe rabon shan wahala ne, ko da wannan ciwon bayan aka barni ai na horu. Fati ce ta shigo ita da Sima ɗan daudun ƙawarta. waya take yi sai larabci take yi, wasu zantukan ina fahimtar me take cewa wasu kuma bana ganewa. Na fahimci da namiji take magana, kuma maganar haɗuwa suke yi. Data ajjiye wayar sai na dubeeta nace. Faty na lura kamar mu,amala da maza shine sana'arki ko?" Na ƙura mata idanu ina karantar yanayinta. Sima ya tafa hannaye yace. "Yau ni naga jar jaraba ido da ido, Iyabo kike ko wa?" Ni dai ban tanka shi ba. Ido cikin ido tace Faty tace." "Ƙwarai da aniya. Jikina shine jarine, babu kasuwanci mai ci a ƙasarnan sama da wannan. Kema kuma dama ce da zaki tara kuɗaɗen da ko kin koma Najeriya ba kiy babu talauci. Kin ganni ina da gidajen da ake mun haya. Mijin da zan aura dawowata kawai yake jira. Na tuttura dilolin kayayyaki gida Najeriya dana koma nima na zama daga cikin waɗanda za a dama dani, hatta kayan kitchen ɗina da kayan ƙyale_ƙyalenmu na mata duk nayi ma kaina. Hmmm Iyabo nima da wanke_wanken na soma. So uku ina zubar da ciki a wannan ƙasa, na farko yaron gidan aikinane yai mun ciki, na biyu Ya Babana ne yai mun ciki ( Ya Baba kamar uban gida ake nufi). Na ukun abokin yaron gidan aikina da yaro daga Canada yai mun ciki. Wuya babu irin wacce ban sha ba a gidan aiki. Wasu fa har rasa rayukansu suke yi. Kema in baki haƙura da gidan aiki ba, wallahi sai aikin gidan larabawa ya nakasa miki jiki, baga irinta nan ba, ciwon baya ya soma kama ki ba, duk da ciwon bayannan suke komawa najeriya su zamema danginsu layabiliti. Tun kafin ki rasa lafiyar ƙafafu a mayar dake Najeriya hajaran majaran ba lafiya ki zame musu nauyi, ke baki tara kuɗi ba, su ki cinye musu nasu gara ki haƙura da wannan aikin." Wani zumm naji a jikina tamkar an jona mun shokin wallahi. A dibibice nace. Duk a gidan aikin kika haɗu da wannan ƙaddarar? Amman Faty me yasa baki koma Najeriya ba? Wannan rayuwar ai ba mai ɓullewa bace, babu yadda za ayi ka saɓi Allah kuma kaga haske a gaba. Ni dai da in bi maza gara in koma Najeriya a nakashe, ke koma in mutu, sai dai ai mun da ƙarfin tsiya. Kema ina mai baki shawarar ki tuba, daga ke har Sima" Hawayene ya zubo a idanunta sai girgiza kai take yi. Sima kuwa dariya da wata girgiza yayi ya bude jakarshi ya zaro hanbaki mai ruwan toka ya sake shafawa. Kullum bakinshi da wannan janbaki kamar akuya ta dumbuji gari. Faty ce kawai tace. "Ni zanfita sai gobe zan dawo. Ƙila in na dawo in tsokata miki kaɗan daga cikin rayuwata. Zaki fahimci neman kuɗi ya wajaba a gareni. Karki mance ina binki kuɗin abinci. Akwai laban da cake in zaki ci gasu can" Ta nuna mun inda cake ɗin yake da bakinta ta fuce abunta Sima na biye da'ita. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke, haka na kwana ina tubka da warwarar tunani, hankalina tuni ya daɗe da komawa gida. Sai kuma inna tuno da irin rayuwar da Dadana take yi a gidan azzalumin mijinta sai inji na ɗan samu ƙwarin guiwar zama in nemi kuɗi da GUMIN HALAL ( BATUL MAMMAN) In na tuno baƙar azabar aikin gidan larabawa da furucin ire irensu Faty sai inji zuchiyata ma ta tsinke. Washe gari da safe sai ga Hajiya ta leƙo dakin. Wani kallon wulaƙanci ta watso mun. "Ina dai fatan ba kin dawo bane da zummar kinbar gidan aikin ki ba ko? Dan ƴan gidan aikin ki sun kira suna tambayar yaushe zaki dawo. A tsorace nace da'ita. Bani da lafiya ne shi yasa na dawo. Da zaran jikina ya warware zan koma kan aikina" "Ya dai fi miki. Me yake damunki da baki iya zuwa mun gaisa ba?" Na kwashe labarin yadda nake ji na bata. Abun mamaki sai ta kwashe da dariya harda buga ƙafarta. Lokaci guda kuma sai ta saki tsaki tare da cewa. "Aikin banza. Da wai me kuka ɗauka, da kun shigo ƙasar kun zama masu arziki ko me? Hatta karuwan cikin gidannan da kike ji da gani suna shan wuya. Ki tambayi tantiriyar ƴar barikin data baki mafaka zata baki labarin da yadda ta soma. Ko da yake ƙila nemanki take yi ko shi yasa ma ta ajjiyeki" Tana gama faɗar haka ta saki labulen ɗakin ta barni ina shurɓune majina. Da ƙyar na miƙe a daddafe na gyara ɗakin, bayan naci kukana na ƙoshi na gode ma Allah. Baya da ƙafafu sun matsa mun, ban ɗaki na shiga na ɗan gargasa jikina da tawul, na shafe jikina tas da man zafi. Sai na ɗan bibbi bango na fita domin in samar ma cikina ɗan abun da zanci. Fitata ke da wuya, sai ga wata ƴar matashiyar budurwar da ba zata haura shekaru goma sha bakwai, sha takwas ba. Idanunta a kumbure bakinta da hancinta sai jini da majina da yawu ke dalala. Faɗi take. "Ku taimakeni bana gani. Mutuwa zanyi. Na roƙe ku ku mayar dani ƙasata najeriya na gaji da wannan azabar." Yib sai ta runtuma a ƙasa take sai ba numfashi. Hankalinmu ya tashi ainun duk muka rufu a kanta masu kuka nayi, masu salati nayi, masu cewa a kira gidansu a sanar musu halin da take suna yi. Ni dai ruwa na nemo na sheƙa mata sai ta sauke ajjiyar zuchiya ashe suma tayi. Tiri_tiri kuma suka jata zuwa ɗakinta dai. Yarinyarnan ashe gidan da take aikine, mijin matar ke kwanciya da'ita shine matar ta kamasu cikin dare. Shine tai mata irin wannan kafirin dukan. Ita ko Hajiya dawa Allah ya haɗata bayan mu. Ashe duk haya_hayar da muke yi tana. Ɗakinta bacci take yi. Tana tashi ta dira a wuyanmu ta inda ta tsikara ba tanan take ja ba. Duk mu kai tsit kowacce tayi tsamo_tsamo. Muna cikin haka yara da manyan da suka mayar da kansu fasiƙai dan cimma buri, huɗu daga cikin waɗanda suka fita kwanan gida suka shigo, ciki harda Faty da Sima. Shigowarsu ce yasa Hajiya ta sarara mana. Abinci na siya tuwo miyar kuka mai tsadar gaske. Komai fa akwai na gida najeriya takari ke siya, akwai maza da mata takari sosai, to su suke sayen wannan abinci. Su kansu masu abincinnan Hajiyoyin kansu ne in suka dawo gida Najeriya. Ina zaune ina cin tuwona, na dulmiya tunanin ko a wanne hali Dada take oho. Sai naji maganar Faty. Ɗagowa nayi ina lashe hannuna ina kallonta du a lokaci guda " "Nace zan ɗan tsokata miki labarina. Amman a dunƙule zan baki" Ajjiyar zuchiya na sauke nannauya. Ina jinki Faty. Nace da'ita tare da bata hankalina baki ɗaya. Tsulum Sima ya shige banɗaki da ɗaurin ƙirji yanata yauƙi. "Mahaifina mai auri saki ne. A iyakar tasowata matan da mahaifina ya aura sunfi ashirin. Yara a gidanmu kuwa kamar bakin masallacin juma'a. Rashin tasowarmu da iyayenmu Mata, sai ya gurɓata rayuwarmu musamman mu matan. Sai mu fita a lokacin da muke so. Ke in kwana bakwai zaki yi bakya gida babu mai tambayar dalili. Ba lalle ne ma a lura bakya nan ɗin ba. Yawo na dinga yi kwararo_kwararo domin samun na abinci da suturar arziki a matsayina na matashiya. Tun tasowata na riga na saba da kula da kaina a matsayina na mace, Babanmu iyakar abinci kaɗai yake iya bamu, shima sau biyu kuma marar daɗi. A shekara sau ɗaya rak yake mana sutura kala ɗaya rak. Ke zaki sai sabulun wanka dana wanki, ke zaki sai man shafawa, man goge baki, ke zaki biya kuɗin kitso, kayan kwalliya, turare. Ke komai da kika sani, ki faɗamun me zai sa ba zamu saba da kuɗi ba. Me yasa idanuwanmu ba zasu buɗe ba? Ita ko mahaifiyata tana can tana auren wani marar mutuncin yana mata gashin ƙuma. Itama bata samu kulawa ba, balle ta kula dani. Yaran data haifa acan ma a ƙarƙashinta suke ita ke ɗawainiya dasu har mijin ma. Kinji somi_somin taɓarɓarewar rayuwata. A wannan yawon ɓel_ ɓel Allah ya haɗani da wani ɗan shaye_shaye harda ƙaddarar aure da yaro ɗaya tilo. Kullum sai ya jibgeni babu ranar banza, matan banza har gadon sunnah ake shigomun dasu. Uƙuba muraratan. Ana cikin haka Allah da ikonshi sai ya sakeni akan karuwarshi, yace in musu girki ni kuma na dire nace banyi. Sai ya sake ni. Na tattare kayana na koma wannan rayuwa ta gidanmu, ko da aka ganni a gida babu wanda yace dani ƙala. Nima nayi banza da kowa. Gaga_gaga naita faɗi tashin neman na tuwo. Har sanadi yasa na tawo wannan ƙasa ta dalilin ƙawata. Labarin zamana a gidan Larabawa ban ɓoye miki komai ba. Naso in tuba in nutsu, amman abun yaci tura ni kuma idanuna ya bushe akan kuɗi da son ceto mahaifiyata da ƙannena da Babanmu ba ɗaya ba. Alhamdulillah yanzu su suna cikin farin ciki, kullum mahaifiyata a cikin sanyamun albarka take. Wannan shine zan iya baki a taƙaice." Girgiza kai nake ta yi, sai jujjuya labarin nake yi a ƙwaƙwalwata, ina mamakin uba irin na su Faty. Dada ce ta sake faɗi mun a raina. Amman in sha Allah da GUMIN HALAK zan kula da mahaifiyata da nawa ƙannen. Faty haƙiƙa kinga jalala." Ta ɗaya ɓangaren sai Gwadabe da yarana suka faɗo mun. Allah sarki yanzu nasan Gwadabe yayi aure, ko wanne irin hali yarana suke ciki oho. Nisawa nayi na ce. Haƙiƙa Faty kin taso a wata iriyar mummunar rayuwa. Ƙaddararki baƙar ƙaddarace. Amman fa babu wata hujja da zaki kafa domin ki saɓi Allah. Zina haramun ce, bai kamata ki kula da iyayenki da kuɗin zina ba" "Dakata Iyabo. Duk abinda kika gani a ɗakinnan, ko kika ci, hatta alfarma
Chapter 39 · 0% Book details