← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 60

Sashe 31

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baba Magaji"
Yana zaune a bayan mota, sai tunanin irin furucin Babala na rashin albarka yake yi. Abu biyu sune suka tsaya mishi. Na farko cire Gwadabe daga cikin ahalinta. Na biyu kiranshi da tayi ba adaliba wannan ya taɓashi, hakan yasa ya sake ɗambar ganin kan gidanshi ya haɗu, duk da shi kanshi ya sani abune mai kamar wuya"
Basu suka isa MaraÉ—i ba sai wajajen goman dare.
Da sallama suka shiga gidan, matan gidan sai hada hadarsu suke yi a tsakar gidan, ko wacce kaji muryarta ta to da yaranta take hirarta. Sannu da zuwa suka yi mishi, rannan nashi a mugun murtuke ya wuce ɓarayinshi. Yana wanka Baba Fhatsima ta shigo, yana jin shige da ficenta, ɗaure da babban tawul ya fito. Idanu ya zuba mata tayi kwalliyarta sai wani dattijuwar kyau take yi. Ajjiyar zuchiya ya sauke, Fhatsima tana daga cikin matan da kallonsu ke kawar da damuwa, gami da mantar da ɗa namiji inda ya dosa.
"Maraba da dawowa ranka shi daÉ—e babban malamina" Zama yayi a kusa da'ita.
"Barka Fhatsima da fatan na sameku lafiya? Na yi ma Allah godiya daya kasance lura dani a cikin wannan daren yana hannunki, ƙila da sai dai a wayo gari zuchiyata ta buga. Dan kece kaɗai mai iya mallakata" Farin ciki ne ya lulluɓe illahirin jikin Baba Fhatsima. Abinci ta zuba mishi suka dawo falo. Yana ci tana mishi taɗi ananne ta sanar dashi zuwan Altine ƙaunarta da da Balaraba
"Allah sarki Altine uwar zumunci yanzu harta zo dan ayi komai tare da'ita. Yaya mijin nata da surukanta?"
"Suna lafiya dukkansu. Ina ruwan Altine daru, ko ɗazu sai da su kai ƴar hayaniya da sahibarka Asshi" Murmushi yayo yana ƙoƙarin karantar yanayinta. Kishinta na mallakar kai yana burgeshi, tana da tsantsar kishi, amman kishin da bai rufe mata idanun da zata cuta ma abokan zamanta ba daidai da kalma. Kishin da bai gusar mata da nutsuwa da kamalarta ba. Yanzu ambaton ashshi kawai da tayi, sai da hancinta ya ɗanyi wani doro, wanda da wannan doron hancin Malam ke gane tana yanayi na kishi. Ɗauke tunanin nata yayi ta hanyar cewa.
"Hmm kinsan yanda muka kwashe da shashashar yarinyarnan kuwa?" A nutse ta kalleshi tace"
"Da naso ne ka nutsu tukunna ko zuwa da safe saimu tattauna, domin sake maimaita maganar a cikin yanayin fishi ka iya haifar da wani fushin." Da wannan Baba Fhatsima ta rinjayi mijinta.
Ta ɓangaren angwaye kuma sun sake zage damtsen neman na tuwo, biki sai ƙaratowa yake yi gida yayi kace kace. Gwadabe bai san halin da ake ciki ba, domin Baba Fhatsima ta ba Malam shawarar ya rufe zancan har sai zuwa bayan biki sai yai mishi bayani a tsanake. Gidan Amare yayi shar dashi ya ɗauki fenti gabaki ɗaya harda cikin gidan malam. Yara kuma sun gwangwaje iyayensu da gyaran daƙuna suma dai sun zama amare a wajen Malam. Malam da kanshi ya tusa angwayennan gaba ko wanne ya zaɓi ɗakinshi duk zubinsu iri ɗayaa ne babu wani bambanci, Gwadabe dakunan matanshi suna jere, a kusa da ɗakin Sadiƙu, kafin ɗakin Gwadabe kuma ɗakin Auwala ne. Key Malam ya miƙama ko wanne. Su Tasi'u da Jamilu su zubin ɗakunansu yafi yalwa, kuma ɗakuna uku ne a ciki kasancewar suna da yara maza da mata. Malam ya basu umarnin ana biki saura sati guda su dawo wannan ɓarayin amare su shigo su samesu a ciki. Haka dai akaita shidimar biki. Ana saura sati guda ɗaurin aure baƙin nesa suka soma cika gida. Su Anty Badi'a kuma suka ƙaura izuwa sabon gida. Nan malam kuma yasa aka fente dakunan da suka tashi wanda Tasi'u ya fita yace Baba Fhatsima ta koma ciki. Wanda jamilu ya fita kuma yaba Baba Asshi. Nan Suwaiba da Amaryar malam suka shiga tashin hankali da tunane tunane dan su a tunaninsu tunda dai su da sauran mammora a jikinsu su ya dace ace Malam yaba waɗannan ɗakuna ba matanshi tsofaffi ba.
Ta bangaren Amaren gidan malam su su huɗu sai gyaran jiki aketa faman yi musu. Magunguna kuwa a dama musu wannan da madara, wannan a dama da Nono haka dai aketa faman yi musu. Hadiza dai tunda baƙi suka cika gidan nasu bata saka gogan nata a idanunta ba, wayarma ba kasafai suka fiye yinta ba. Ita dai sai tsuma kanta take yi, burinta ta zama sarauniyar zuchiyar Gwadabe. Kuma kasancewarta bazawara harda yara yasa tafi ƴan matan kannenta shirya kanta. Ƙawarta Hassana itace take ta bata dabaru da sirrin zama da kishiya, sakamakon ita a gidanta itace ta uku. Hadiza ta ɗaura ɗamarar yaƙi da jahilin kishi, ta ɗaura ɗamarar bama Gwadabe farin ciki, da kiyaye dukkannin ɓacin ranshi. Amaryarshi kuma tsakaninsu gaisuwane, dan bata jin zata wani iya zaman hira ko wani sakin fuska da kishiya. Kowacce dai ta iya allon ta ta wanke.
Kasancewarta Amaryar ƴar gida har an mata jerenta tsab, ta samu kaya fiye da aurenta na fari, ɗakinta yayi matuƙar kyau. Tun kafin gida ya cika da mutane Baba Fhatsima da Goggo Altine su ka zaunar da Hafiza sukaita karanta mata karatu masu amfani ( gaba cikin labarin zamu ji me suka faɗa mata a aikace a gidan Gwadabe) Duk abinda suka faɗa mata tayi ram dasu a ƙwaƙwalwarta sai jujjuyasu take tana farin ciki. Harma Allah _Allah take a soma wasan.
Rana bata ƙarya Allah ya kawo mu ranar biki. Tun ranar Monday aka soma shagulgulan da suka shafi al'adu, ta ɓangare Amare da angwaye. Ta bangaren ƴan Takai. Goggo Iyatu, da Goggo Rahila Matar ƙanin Babansu Gwadabe ne a manya suka tawo. A yaran mata Laila tazo, sai Abuwa matar Ɗan Goggo Hajiyayye matar Ƙanin mahaifin su gwadabe, ita tsufa ya kamata Abuwa ke wakiltarta zuwa duk wani sha'ani na dole. Babala dai dasu Yaya Hambali da matansu ko ƙeyarsu babu. Gida ya kacame da sha'ani. Mayu da ɓarayi sun samu abun nema, kowa sai farauta Laila kuwa duk abinda taga anyi wasarere dashi saita adanashi, ta sake ta shiga jami'a sosai. Duk wanda yai wasarere da jakarshi, akwai Laila da ire_irenta da yawa a gidan biki su zasu adanama mutum kayanshi hausawa sukace mai son abinka ya fika dabara.
Amare sai kyau suke sha, su saka wannan sutura su canja. Hadiza tayi kyau fiye da aurenta na fari, domin yanzu tafi sanin kanta fiye da baya, a baya akwai ƙuruciya. Amman a yanzu tasan cikakkiyar darajarta ta ɗiya mace.

GWADABE:
Ranar da aka ɗaura aurensu Hadiza da safe, Gwadabe nata shirin kama hanyar Najeriya shi da Baba Magaji. Sai ga Auwala ya shigo ɗaki ya sameshi sun sha uban ankon farar shadda mai maiƙo.
"Ango mijin Hadiza. Malam ne yace in yi kiranka zaku yi magana" Murmushi yayi mishi yace.
"Ango mijin Zakiya bada kan ka a sare kaje gida kace ya faÉ—i" Dariya suka saka dukkansu. Hularshi ya É—akko yasa suka fita tare. Ratsa mata Æ´an biki sukayi, sai nunasu akeyi gwanin sha'awa duk kaya iri guda suka saka harda su Yaya Tasi'u. A zaure suka samu Malam da aminanshi dattijai biyu.
"Gwadabe tafiyarmu Najeriya an fasa. Yanzu haka maganar da nake maka an ɗaura auren naka acan Tamu da Bara'u su suka tsaya akan komai, yanzu aka ɗaura auren. Sun kirani suna hanyar tawowa da Amarya, motar kaya kuma tun jiya da rana ta kamo hanya. Babu mamaki zuwa rana ka gansu. Na sanar ma Fhatsima Dangin amarya da masu jere suna hanya. To sai ka zauna a cikin shirin tarbar amaryarka" Murmushi Gwadabe yayi, kanshi na ƙasa sai godiya yake yi ma Malam kawai, domin bashi da bakin gode mishi, yayi mishi komai a rayuwa. Sallamarsu Malam yayi suka fice waje wajen abokansu.

Hadiza:
Ta bangaren Hadiza tunda Malam ya sanar ma Baba Fhatsima Amaryar Gwadabe suna hanya. Sai cikinta ya ɗuri ruwa, har wani zazzaɓi taji yana shirin sakko mata. Goggo Altine ta dubi Baba Fhatsima tace.
"Zuwa bayan la'asar sai a shigar da ita gidanta tunda itace uwar gida, yana da kyau Amarya tazo ta sameta a ɗakinta. Dan haka bari in fita in sanarma da su Hadizan Zendar." Wani sanyi Hadiza taji ya kwaranyi daga kanta zuwa ƙirjinta.
Kafin azahar masu jere suka iso motar jere daban, motar iyaye daban. Sun samu tarba ta arziki an taresu da kaji da farfesu, da tuwon ɓula ( tuwon ruwa) Ana idar da sallar La'asar aka fito da Amarya Hadiza. A zaure suka yi kaciɓus da Malam yana tsaye yana jiran fitowar tasu. Tsugunnawa Hadiza tayi tana hawaye a gaban Malam.
"To Hadiza ina fatan wannan fitar da zaki yi daga gidanku yasa fitace ta har abada sai dai zuwan daÉ—i in sha Allah
MRS BUKHARI
Chapter 31 · 0% Book details