Sashe 17
Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Baba Fhatsima"
Lallai hausawa sun yi gaskiya da suke cewa magaji mafiyi. Ita kanta Baba Fhatsima tana mamakin yanda Hadiza ta xama kwafinta a kishi. Komansu iri ɗaya ne ta ɓangaren kishi babu inda ta barota saima finta da tayi. Ita kanta da ba dan ta kai zuchiyarta nesa ba, da kuma tunanin goben yaranta ba, da a lokacin da malam zai ƙaro Aure da tuni ta bar auren kwata_kwata. Har gobe zuchiyata tana azabtuwa ainun da zaman kishin da Malam ya haɗata yi da sauran matanshi. Duk da tasan cewar ita da Tasi'u sune fitulun dake haska gidan malam, hakan bai hanata kishi ba. Iya rigima Malam yake kiranta a duk sanda ta murɗa kambun kishinta ta juya mishi baya.
Ajjiyar zuchiya ta sauke a daidai shigarta ɓarayin da turakar Malam take. A zuchiyarta take roƙama Hadiza Allah ya bata haƙuri da juriya. Ɗayar zuchiyar tata tana cike da tausayin Hadiza a bisa dakon nauyin kishi da zata ɗauka na iya tsawon rayuwar duniyarta.
Da sallama ta shiga falon na malam, yana zaune a kujera mai cin mutum uku Amaryar Malam tana gefenshi tana kiciniyar cire mishi babbar rigarshi. Baba Fhatsima ta haɗiye wani yawu mai kauri, tare da yin wuf ta yi ƙasa da idandunanta. Kunya da nauyin Fhatsima suka kama malam. Cikin dibibicewar data mugun ƙular da Amaryar Malam yace.
"Uwar gida sarautar mata, farar mace alkyabbar mata, zo ki zauna Fatsima" Ɗan siririn ɓoyayyen tsakin da a iya kunnen Baba Fhatsima ya sauka Amaryar Malam tayi. Kujerar gabaki ɗaya ta sauka ta barma malam da Baba Fhatsima, ta koma kujera mai cin mutum guda ta kumbura tai suntum. Murmushin takaici Baba Fhatsima tayi, a zuchiyarta tace.
"In banda maza da faɗuwar girma ni Fatsima da yaushe zan haɗa gado da yarinya ƴar cikina? Amman su maza basa ko jin kunya, da nauyin manyan yaransu. Wacce iriyar taɓarace Malam bai yi ba lokacin da ludayin Amaryarshi ke kan dawo? Murmushi ta kuma yi mai cike da fassarori da dama.
"amarya ina ganin sai kin tashi kin kirawo mun Asshi, da Suwaiba Lokaci yana ƙurewa ya kamata ace sun hallara" Ba dan ranta yaso ba ta fita ta bar Malam daga shi sai Baba Fhatsima ba. Tana fita Malam ya dubeta yace.
"Fatsima bakya tsufa ke dai. Wazai ga Tasi'u yace ke kika haifeshi?"
"Hmm Malam Baka rabo da daÉ—in baki, koma kince borin kunya" Da Malam da ita da tai maganar suka kwashe da Dariya. Shi yana dariyar yanda akayi ta É—agoshi. Ita tana mai dariyar kaji kunya. A haka matan Malam suka shigo suka iskesu.
"Au aini naga kamar Amaryar Malam itace da girki ko? In ba ɓatan lissafi nayi ba. Ta faɗa tana kallon Amaryar Malam data cika tana shirin fashewa. Suwaiba ta taɓe bakinta tace.
"Girkinta ne, kin mance ita ta wuni tana hidimar yara?" Malam ne ya dakatar dasu ta hanyar cewa.
"Yanzu zaku zauna kuji dalilin kiranne ko kuwa zaku tsaya bin ƙididdigar waye me kwana waye marar kwana ne. Wai shin me yasa ke Asshi baki da aikin daya shige na ta da tarzoma ko da yaushe?" Zama ko wacce tayi a kujera. Amaryar Malam ta je ta zauna a kusa daf da Malam. Bai dai ce da'ita uffan ba. Takaddu dunkulallu ya ciro daga aljihun rigarshi ya zube a ƙasa.
"Ko wacce ta ɗauki ɗaya ta riƙe a hannunta kafin in gama bayani sai ku buɗe. Sai da kowacce cikinsu ta ɗauka sannan Baba Fhatsima ta ɗauka a ƙarshe. Malam yace.
"To wannan ƙuri'ace nayi muku kamar dai yadda nake yi a ko wacce tafiya in ta taso mun. Kuma tunda nake yin wannan ƙuri'ar duk wacce ta ɗauki tafiya bana sakewa da'ita nake tafiya. To a wannan karonma wata tafiyace ta taso babba a gabana ta banbanta da duk tafiye_tafiyen dana saba yi a baya. Naba ko wacce dama ta buɗe takaddarta duk wacce ta ɗauki tafiya to Allah ya ciyar da'ita. Sannan ku sani babu zalunci ko son kai a cikin wannan lamarin Allah shine shaidata. Bismillah ko wacce ta buɗe.
Nan da nan ko wacce ta shiga kiciniyar buÉ—e takaddarta tare da zabarin ganin ta É—auki tafiya
Domin tafiya da malam ana samu alkhairi sosai, kuma macce tana samun lokacin kanta dana mijin nata, soyayya ake darza tsantsa. Cikin sa'a Baba Fhatsima ta samu tafiya. Har cikin ƙasan ranta tayi farin ciki sosai, dan ta jima sosai rabon da ta samu damar tafiya tare da Malam. Kuma a halin yanzu tana cikin yarda dashi. Baba Asshi tafiyar da yayi na ƙarshe wacce ba'ayi wata ba sai yanzu, tare da'ita akaje. Amaryar Malam kuwa sai da ta samu takaddar tafiya sau huɗu a jere ras, Suwaiba ta samu sau biyu a tare. Wannan karon kuma Allah ya ciyar da Baba Fhatsima.
"Malam nice na samu tafiya" Bai san sanda murmushi ya subce mishi, farin ciki ya bayyana s fuskarshi ba. Malam har tsaiwar dare yayi kan Allah ya dafa mishi Baba Fhatsima ta samu wannan takadda ta aminci. Kawar da kai Baba Asshi tayi gefe, tare da taɓe bakinta. Malam kuwa yace.
"Masha Allah dama kina da paspo ta kwana gidan sauƙi sabida haka ki soma shirin keta hazo" murmushi Baba Fhatsima tayi mai cike da danƙararriyar soyayyar Malam da take ta farfaɗowa.
"Allah ya nuna mana lokacin malam. In ka bani dama sai in koma ɓarayina" Kai ya gyaɗa.
"Ki isa cikin aminci Fatsima uwar gida ran gida" Ai fitar Baba Fhatsima sai tarzoma ta tashi, daga ƙarshe dai fatattakarsu Malam yayi. Amaryar Malam dake da kwana itama ta bisu tana kuka wai ta yafe kwanan ma baki ɗaya.
A wannan daren zukata da yawa a cikin tunani suka kwana, ko wanne da abunda yake tubkewa da warwarewa haka garin ya waye kamar yadda aka saba.
Gwadabe:.
Tun asuba yake kiran wayar Shafa amman wayar har zuwa lokacin a rufe take. Gashi yana son zuwa ganin Hadiza yaga ya ta kwana. Duk da Auwala ya kwantar mishi da hankali a daren jiya.
Tashi yayi jiki a saɓule ya nufi cikin gidan. Yau matan Malam babu wanda ya amsa gaisuwar su Auwala ma balle kuma Gwadabe wanda yazo dandalar arziki. Sai Baba Fhatsima ce dake zaune a dokin ƙofa tana siyan lalle da gishirin lalle akan wata yarinya tace.
"Gwadabe yau makara kayi ne sai yanzu ka samu shigowa?" Da biyayya ya zube ya gaisheta, ta amsa cike da fara'a.
"Ka shiga Hadiza na ciki, da zazzaɓi ta kwana, likita ma Matar wanku zata kaita" Kai ya kuma saukewa harda sosa kanshi.
"Subhanallaah Allah ya bata lafiya, bari in dubata" Ya faɗa da kunya. Shiga yayi ya samu Hadiza a zaune tana shan kunu. Ƙurama juna idanu su kayi na daƙiƙu. Ita ta rigashi sauke ido.
"Ina kwana Yaya Gwadabe?" Bai samu damar amsawa ba, waje ya samu ya zauna a ƙasa ƙur idanshi a kanta.
"Ina roƙon Allah yasa ba maganata ta jiya bace sanadiyyar ciwonnan naki ba Hadiza?" Bai jira ta amsa shi ba dan bai tambayeta yana nufin saita amsaba ya ɗaura da faɗin.
"Wallahi ba dan Baba magaji ya tozartaki ko ya ƙasƙantar da darajarki bane yasa yai miki zaɓin Gwadabe ba. Nima ba dan tayin da yaimun bane yasa na amsheki ba face kin yi mun kuma naji zan iya rayuwar aure dake. Yanayinki da zubinki yana mun kama da na matata Iyabo sosai. Ki fahimceni auren zumunci cike yake da tarin hikimomi.
Itama fa bawai ina nufin bana sonta bane A'a itama inai mata kalar nata son daban. Hatta tsohuwar matata gurbinta shine a ƙasan zuchiyata. Ki kwantar da hankalinki kinji?" Tunda ya soma magana zuchiyarta ke lugude. Musamman da taji matsayin da Iyabo ta wawashe a rayuwar Gwadabe.
Sai Allah ya sadamu ranar Monday da izinin Allah danjin yadda zata kaya.
Ki faÉ—i abinda kika É—auka na darasi a wannan labarin duk da bamu yi nisa ba.
[8/9, 6:47 PM] +234 803 969 6400: https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
NAMA YA DAHU..
ROMO ÆŠANYE
BOOK 2
5
*Ina kuke mata ƴan ƙwalisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haɗaɗɗun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
_Assalamu Alaikum barkanmu da juma'a. Iyabo tana godiya a bisa karɓar labarinta da kukayi hannu bibbiyu_