← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 60

Sashe 11

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai naga kuɗine. Bayani yaimun akan siyar da shanunshi da yayi, duk dan kada in tafi. Ni kuma naƙi karɓa fur, na bashi hakuri tare da yi mishi bayanin na riga nasa Hajiya Salamatu ta kashe kudinta da ɓata lokaci. In nayi mata haka ban kyauta ba. Dole babu yanda ya iya haka ya mayar da kuɗin aljihun ƴar shararshi, tare da sauke kanshi ƙasa kawai. To ya akayi_ya akayi labarinnan ya je kunnen matar Yaya Hamma sai Allah. Nan ta da bori Boɗɗo na bani labarin irin rikicin da su ka yi ita da Yaya Hamma. Har sai da Yafendo ta shiga cikin lamarrin. Kuma jin abinda Yaya Hamma ya aikata yasa Yafendo ta fusata itama. Kun dai san fulani da maganar Shanu, dan tsabar ɓacin ran da Yafendo tayi ƙwace kuɗin tayi a hannun shi Yaya Hamman, tare da gargaɗin koma me zaiyi mun yayi mun ni ƴar uwarshi ce. Amman bata yadda ya sake taɓa shanu ba, waɗannan shanu gadon_gadone da suke fatan ƴaƴansu Hamman da jikokinsu, da haularsu masu zuwa suita gadansu. . Ana saura sati guda in tafi, sai Yaya Hamma ya soma rashin lafiya. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Tun yana zuwa kiwo har dai ya dena. To dake a ɗakin Yafendo yake jinyar tashi, ana saura kwana biyu in tafi sai na je dubashi. Ina shiga sai Hama ta bar duk abinda take yi ta dawo ɗakin Yafendo ta zauna. Harma tana shafan sumarshi a gabana dan inji haushi, shi kuma kunyata tasa ya ture hsnnunta. Ai ko abun ya mugun sokar zuchiyata ta yadda ni kaina sai da nayi mamakin yanda naji sautin kishin mutumin da bai buɗe baki ya furta mun kalamin so ba. Sai dai iya so da kulawa a aikace yana nuna mun. A furucine bai furta ba, kuma na fahimci nauyi abun yake yi mishi. Kunya da kawaici irin na fulanine ya hanashi furta mun yana sona. Shigowar Yafendo da fura a hannunta ne yasa Hama tashi ta dawo ƙasa ta zauna. "Jabu ga fura ki sha" Ta miƙo mun. Hannu biyu nasa na amsa nace. Use Yafendo. "Hama kin baro aikin ki kin dawo kin zauna? Maza tashi ki koma kan aikin ki, kinsan zaki je tallan nono fa" Har cikin ranta bata jin daɗin wannan katsalandan da Yafendo tayi mata ba. Amman ni kuma kamar in goya yafendo haka naji" Tare suka fice ɗaki ya rage daga ni sai Yaya Hamma. Shi kuma fishi sosai yake yi dani duk fa akan tafiyar tawa ne. Ni sai tafiyar ta fitar mun akai, kuma nayi mishi rantsuwar da ace da kuɗina akayi mun komai da tuni na fasa. Amman yanzu in nace na fasa hajiya Salamatu ba ƙaramin bacin rai zata nuna ba, kuma ƙila ita kanta uwani in ja mata. Yaya Hamma ya jikin naka?" "Da mutuwa ma zanyi kila hankalinki sai yafi kwanciya ko?" Sai naji faɗuwar gaba har idanuna suka kawo ruwa. Cikin rawar murya nace. Ko kusa bazan ji daɗi ba. Kayi haƙuri tafiyar da zanyi ta dole ce, kuma bazan shige shekaru uku ba zan dawo. Kuma ina fatan in dawo in sameka a cikin aminci. Ɗan murmushin gefen baki kawai yayi mun. "To ki shirya tare zamu tafi kanon. Bazan dawo ba har sai jirginku ya tashi. Idanu na zaro nace. Ka rufa mun asiri kar kasa matarka ta bindigeni. Kai da baka da lafiya kuma sai in ɗaura maka wahala? Wallahi ka barshi. Hararata yayi mai cike da tsantsar so. "Ai ratayayyen hakkine a kaina inga tafiyarki." Shiru nayi zuchiyata na doka mun tambura. To Allah ya baka lafiyar Yaya Hamma. Ni zan zo in wuce" Sallama nayi mishi na fito da furata a hannuna a ɗakin Boɗɗo na shanye furata. Washe gari Dada ta kawo mana ziyara da su Cubu dan muyi sallama. Tayi mun nasiha mai ratsa zuchiya sosai. Nayi kuka kamar raina zai fita. A daren na kasa baccin kirki. Ina kwance Daso ta shigo ta tsaya a kaina. "Sai ki tashi Yaya Hamma na kiranki. Jabu wallahi kiji tsoron Allah kinzo kin samu mutum da ƴar matarshi suna soyayyarsu gwanin sha'awa. Amman kinzo kin raba wannan soyayyar da shaƙuwa, kin hana Yaya Hamma ya samu lokacin kan shi balle ita Matarshi ta samu lokacin shi itama" Tashi tsaye nayi ina jujjuya maganganun da Daso ta fesomun. Kai kawai na girgiza tare da cin alwashin sai na jero mata waɗanda suka fi wanda ta faɗa mun zafi. Ficewa nayi na barta da ƙunan zuchiya. A zaune na sameshi yana zane a ƙasa da tsinke. Zama nayi a gefe nace. Barka da zuwa Yaya Hamma. Yaya jikin naka amman?" "Jiki da sauƙi Jabu. Ya shirin tafiya? Nasan dai an gama komai ba tun yau ba. Ke naga zumuɗin tafiya ki barni kike yi" Sai naji duk jikina ya mutu. Shine yake ganin kamar ina zumuɗin in tafi in barshi. Amman har cikin jikina inajin zafin kewarshi tun yanzu, bansan kuma ya abun zai zama in na tafi ba. A ranar dai hirar batai armashi ba jikkunanmu a mace mu kai sallama. Harna taka zan shiga gida ya kira sunana. "Jabu" Cak na tsaya. A hankali na juyo muka zuba ma juna idanu na mintunan da bazan iya faɗar adadinsu ba. Ya kasa ce mun uffan. Fitowar Jatau ce ta katse komai. Bai samu damar faɗa mun abinda yasa ya kirayi sunana ba, Jatau ya tareshi da zantuttuka. Cikin na shige na barsu nan. Ina shiga na harari Daso nace. Gobe zan bar garin. Kinga hakan zai baki damar cusa kan ki a wajen Hamma. Kinga in da rabo sai in dawo in sameki kina goyon ɗanku na biyu ke da shi." Ina faɗin haka ta kalleni tace.."haka kika ce mun Jabu?" Ƙwarai kuwa haka nace. In kin isa ki maye gurbina a zuchiyarshi in zaki iya Ni kin ganni nan tafiyata tafi komai mahimmanci a wajena" Kwafa tayi tace dani. "Zan baki mamaki Jabu, zaki san nima macace wacce Allah ya horema duk abun alfahari kinsan dai na fiki kyau nesa ba kusa ba, in banda ma namiji da gane_gane ko me ya gani a jikinki oho" Ni ban ma sake bi ta kanta ba. Itako sai mita take yi da fillanci. Ina kwance shiru duk kewan yarana ya kamani, dama Baban yaran. Can kuma sai Hamma ya fado mun, da kuma alwashin da Daso taci mun. Da irin wannan tunani bacci yayi awon gaba dani. Asubar fari na yi wanka tsab. Ana fitowa masallaci na suri kayana a jakar leda na fito. Na yi sallama da kowa da kowa. Ana cikin haka Yaya Hamma ma ya shigo. Muna fitowa Boɗɗo da mijinta na isowa suma. Sai da suka rakamu fa har Girai kana suka dawo mu kuma muka shiga cikin gari, Yaya Hamma ya samu a motar Kano. Sassafe motarmu ta hau kwalta. Sai da tafiya tayi nisa Yaya Hamma yace. "Inaso ki mun wani alƙawari Jabu. Nasan kina da riƙon alƙawari na san hakan silar shaƙuwarmu. To ki mun alƙawarin da kika tabbatar zaki cika mun shi. Kar ki yaudareni in yayi miki tsauri ki ce mun ba zaki iyaba" A sanyaye nace dashi. Faɗi alkawarinka a shirye nake da in cika shi. Matsayinka ya wuce hasashenka" Daɗi yaji sosai. "Ki mun alƙawarin ba zaki wuce shekaru ukunnan da kika ɗebarma kanki ba. sannan ki mun alkawarin ba zaki kula samari ba dan Allah. Sannan ki mun alƙawarin ba zaki dawo kiji ke kinfi ƙarfin zama tare damu ba. Bi ma'ana kar ki sake halayyarki, sannan ki mun alƙawarin riƙe mutuncinki" Shiru nayi mishi ina murmushi kaina na ƙasa. "Au ke dariya ma na baki ko? Kin kyauta ai" Ɗago kaina nayi na kalleshi. Yaya Hamma na karɓi duk alƙawarurrukanka. Allah yai riƙo da hannayena in cika maka alkawarurrukanka. Amman ina da taambaya..." "A'a Jabu ".. yayi saurin dakatar dani ta hanyar ɗaga hannayenshi. Ba shiri na yi shiru da bakina. "Ni dai tunda kin ɗaukii dakon alkawarina ai Shikenan. Ni kuma zan yi zaman jiran dawowarki, tare da miki fatan samun nasara kuma" Daga haka kuma mu ka ɓige da hirarraki, ya dinga bani labarai dangane da al'adun Fulani. Ni kuma dama na kasance ma'abociyar son tarihi ce da duk abinda ya shafi gargajiya ta ko wanne ƙabila. Allah cikin ikonshi da amincewarshi muka isa garin Kano. Kai tsaye gidan Uwani muka ya da zango. A gidanta muka ci abinci. Yaya Hamma ya fita zuwa masallaci dan rama sallolinshi, nima na rama nawa sallolin. "Baki ga yanda kuka dace ba wallahi. Ashe kyakkyawane Yaya Hamman naki. Kuma na lura gaskiya yana tsantsar sonki. Munafuka kema fa kin soma sonshi. Ni dai amman bana bayan wannan soyayyar ruga ba wajen zamanki bane" Dariya mu ka yi dukka. Hakane Uwani wallahi na tsunduma cikin sonshi. Shi kuwa dama ba'a magana dan shi ya koya mun yanda zan so shi. Sai dai fa akwai kura Uwani" Sai da ta gama dariyarta tas kana tace mun. "Ƙurar me kuma Iyabo, akwai wata matsalar ne?" Nace da'ita. E to akwai matsala ta ɓangaren matarshi, da ɓangaren yarinyar ƙanwar Dadanmu Daso wacce nake gidansu a zaune. Matsalolin du manya ne daka iya dakile soyayyarmu. Matarshi tunda aka kai mata gulmar ana ganin mijinta a wajena, sai ta tayar da ƙayar baya, kullum cikin fitina dashi take. Ke har shanunshi daya siyar ya bani kuɗin ban karɓaba sai da su kai rikicin da har mahaifiyarshi ce ta shiga. Ƙanwata tana Aure a gidan Uwani tana auren ƙanin shi hamma ɗin. Sai suka tsiri zaman doya da manja. Ita kuma Daso ko tsaiwa da zaurawa bata son yi kwata kwata duk sabida da shi. Akwaifa wani abokin mijinta mai rasuwa da yake tsantsar sonta. Yarinyarnan fur ta dire wai bata sonshi. Ni kumaa a jiya ta caccakamun magana akan wai Hamma na zaman soyayya da matarshi ni nazo shiga tsakani na hana aci soyayyarnan yadda ya dace. To kinsan mu mata, saina caccaka mata nawa maganganun nace ta aurshi in dawo in samu tana goyon ɗansu na biyu. Ita ma cikin fishi sai tace zan gani. To jiya da ƙyar nayi bacci Uwani " Dariya muka dinga yi ni da Uwani. "Ni dai shawarar da zan baki wallahi ki raba kanki
Chapter 11 · 0% Book details