← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 60

Sashe 30

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

TAKAI TA KAWO TA SABA DA SAUKAR BAƘI
Babala tana zaune a tsakar gida, ta jiyo yaran gida na yima Baba Magaji sannu da zuwa. Sai taga akwatuna Bara'u na shigowa dasu.
"Kai Bara'u waÉ—annan famtimotan fa shi Yaya Magaji shine ya tawo dasu?" Murmushi Bara'u yayi yace.
"E dashi suka tawo. Kinganshi ma ya shigo" Yana kaiwa nan ya fice. Yaya Halima da Goggo Iyatu suka fito daga ɗaki riƙe da haɓa har Yaya Magaji da Jamilu suka ƙaraso.
"Maraba lale da zuwa, Jamilu yau kaine a cikin gidannan iko sai Allah. Wasa gaske Gwadabe naso ya dawo da tsohon zumunci" Cewar Babala data haÉ—e ranta tayi kicin_kicin.
"Baba ku shigo daga ciki, kunsha hanya, ga magriba tayi." Cewar Yaya Halima kenan.
"A'a Uwata bamu ruwa a buta kinji magriba ake kira, in muka yo Sallah mazo a tattauna a tsanake. Hambali bai ƙaraso bane, na kirashi shi da Harisu nace duk mu haɗu anan." Goggo Iyatu tace.
"Yanzu fitarsu masallaci kuka iso" Ruwa aka basu a buta su kai alwala tare da tafiya masallaci. Tare suka dawo dasu Yaya Hambali. Abinci aka dire musu. Baba Magaji da ya kai loma bakinshi bayan an gaggaisa sai ya soma jawabi.
"Wannan fantimotin auren Gwadabe ne, da Shafa ƙanwar abokinshi Tamu, ƴaƴan mirgayi Hamisun Dogo. Da daddarennan nake son za'a kai kayan tare da sadaki baki ɗaya. Wannan dalilinne yasa nace Hambali da Harisu su tawo dan su jagoranci komai tunda sune manya."
"Kaga ni Yaya ban gane me kake nufi ba. Au jita_jitar da muke ta ji a gari akan Shafa Gwadabe zai aura ashe da gaskene itan zai aura. Ina batun Hadiza Æ´ar Fhatsima?"
"Du su biyun zai aura kuma rana É—aya da izinin Allah " Dariya Yaya Hambali ya saka.
"Ikon Allah waina kwance ya faɗi. In banda talaka da nemo wa kai jarfa ina Gwadabe ina mata har biyu Baba. A duba lamarinnan fa, kar a siyar da akuya ta dawo tana cin danga. Dan Gwadabe ba mai ƙashin ma arziki bane shi tun fil azal, duk abinda yaronnan ya taɓa sai ya lalace. Yanda Allah yaimun wannan sutura bana jin zan iya shiga wata hidimar Gwadabe, ko dan gudun kar jarfar dake bibiyarshi ta shafeni." Jim Baba Magaji yayi, yana kallon Yaya Hambali da maɗaukakin mamaki. Yaya Harisu yace.
"Ni kaina bazan iya saka hannu a duk wata hidimar Gwadabe ba. Yaron dake tafiya da bakin uwa" Jamilu ya buÉ—e bakinshi dan mamaki. Goggo Iyatu kuwa sai sharar hawaye take yi.
"Ohh Yaya Laila ce dai baka ƙaunar Gwadabe ya aura. Amman gashi ka jona mishi ƴarka kai. Yarinyata ta ƙi zaman aure, yanzu haka tana gida an sake sakota, bayan mijin yayi mata kafirin duka."
"Hmmm ni kam nama rasa ta cewa wallahi. Yaya Gwadabe kaima ɗanka ne. Kai kaɗai gayyane zaka iya zartar da komai. Gidansu Shafa ka sani. Allah ya sanya alkairi shine kaɗai abinda zance. Amman Gwadabe ai ya nuna mun bai haifu a cikina ba. Tunda ni ina matsayin uwarshi sai dai in ji ƙishin_ƙishin a gari zai auri ƙanwar abokinshi. Yaranshi duk ya tattare ya damƙa mishi. Gashi da ƴan uwa ya nuna baya ƙaunarsu. Damme zasu ƙaunaceshi shim...
"Ya isa haka nace" Baba Magaji ya dakatar da Babala da kakkausar murya.
"Lallai Babala ba zaki taɓa yin hankaliba har abada. Ke da kanki kike farraƙa kan yaranki. Shin me Gwadabe yayi miki ne a rayuwa haka. Ba dai akan Auren beyerabiya bane? To naga ya rabu da'ita. Na ɗauka ƙiyayyar zata tsaya a iya nan ki sama yaronnan albarka ko zai ga haske. Me yasa kika zame mishi baƙar uwa? To Shikenan ni zan tsaya mishi ayi komai.
Ku kuma" Ya nuna su Yaya Hambali yace.
"Kubi duniya a hankali. Ita dukiya baƙuwace. Kuma wanda Allah yace sai yayi arziki sai yayi. Ina jiye muku ranar da zaku kasa haɗa idanu da Gwadabe, ko kuma ranar da zaku kasa matsowa inda yake sakamakon ɗaukakar da zai samu. Jamilu ci abinci ka kinkimar mun famtimotinnan muje kai da Bara'u ku rakani na ishi Gwadabe uwa da uba. Ƴan uwanshi na can sun share mai hawayenshi, suna sonshi, kuma suna zumuncinsu. Akwai ranar ƙin dillanci. Yaya Halima ta buɗe baki zatai magana, Baba Magaji ya dakatar da'ita ta hanyar ɗaga mata hannunshi. Matan gida suka shiga tururuwar zuwa gaishe da Baba Magaji, daurewa yayi ya dinga fara'a dan kawar musu da tunani.
"Gida naga yasha gyara, waye yayi muku gyara haka"
"Ka ganshi É—an albarka wanda tun yana tsumman goyo yake samun tabarraki. Allah yayi mishi lifiÉ—i yayi gamdakatar da arzikinshi. Kuma ya ja Æ´an uwan nashi a jiki anata harkar arziki. Nanda wata biyar ma umara zamu dani dashi da matar tashi." Babala ce take magana da fara'a sai dariya take yi. Baba Magaji yace.
"Madallah Allah yaima dukiya albarka Hambali. Jamilu muje ko?" Tashi Jamilu yayi ya soma jan famtimotan zuwa waje. Yana jaye dasu Baba Magaji yana biye dashi a baya. A ƙofar gida suka tarar da Bara'u duk suka rankaya. Sun samu tarba ta mutunci gaya. Nan suka gabatar da sadaki da kayan aure.
"To nan da wata biyu dai muke so a ayi komai a gama. A duba, sabida tare muke son ayi komai a gama yarane kusan goma za'ayi bikin nasu tare" Ƙannen mahaifinsu Shafa ɗaya daga ciki yace.
"Allah ya nuna mana lokacin. Yaro yayi mana bayanin komai. Mu dama mun daÉ—e a shirye. Fatanmu Allah ya kai rayuwarmu" Nan su kai sallama da juna.
Ta ɓangaren Babala daren ranar kasa bacci tayi, ta saƙa wancan ta kunce wancan. Babu irin abinda bata hasaso a ranta ba dangane da irin abinda Baba Magaji yayi mata. Abun ya matuƙar ɓata ranta har kuma taci alwashin ba zata taɓa taka ƙafarta da sunan zuwa bikin Gwadabe ba. Kuma ƙafarta ba zata taka dan matanshi sun haihu ba. Kuma taci alwashin duk ranar da ya tako ƙafarshi yazo inda take sai tayi mishi tijara. Da waɗannan ire iren tunanin garinta ya waye.
Ta ɓangaren Baba Magaji ma, sai tunani yake yi, tare da jinjina halayya irin ta Babala Haka ta taso tun asali da wata iriyar baƙar zuchiya mai shegen riƙo da rashin yafiya. Uwa uba ga jahilci da zaman karkara dake ɗawainiya da rayuwarta, in banda haka taya uwa zata dinga adawa da gaba da duk ci gaban ɗan data tsugunna ta haifa, akan dalilin da ba dalili ba.
Ko washe gari kafin Baba Magaji ya tafi sai da ya sille Babala tas, itama kuma ta fusata dashi, dama a wuya take dashi nan tayi tsalle ta dire tace.
"Magaji dakata kaji, ba zaka zo har gidan mijina ka nemi tozartani a gaban ƴaƴana ba. Sabida haka kar ka sake tako ƙafarka kazo inda nake, ka soma gyara gidanka tukunna, ka dena rashin adalci a tsakankanin matanka tukunna kafin kazo mun da guntun wa'azinka. In aka sake faɗamun wani abu daya danganci Gwadabe ma Allah ya'isa ban yafe ba. Ka faɗa mishi matsawar ya tako Takai da zummar zuwa ganina nonona da yasha sai ya biyani. Haka in ya tako ƙafarshi yaje wajen ƴan uwanshi Allah ya isa ban yafe mishi ba ehe, kaje ka riƙeshi" Idanu Baba Magaji ya runtse. Yaya Hambali kuwa ya saki wata siririn murmushi, Yaya Harisu kuwa fuskarshi kadaran kadaham. Matan ƙannen mijin Babala nan suka shiga bata haƙuri tare da nuna mata rashin kyautawarta akan furucinta, gudun kar ta sake ɓalɓanta rayuwar Gwadabe da ci gabanshi. Amman suma sai ta dira a kansu. Baba Magaji yace.
"Ki rubuta ki ajjiye, daga Gwadabe har ni ba zaki sake saka kowa a idanunki ba. Jahilar kawai tur dake a matsayin uwa ga Gwadabe. Ki sani wata rana zaki shiga jerin masu layin son yin tozali da Gwadabe." Yana kaiwa nan ya ja hannun Jamilu rai a ɓace yana share hawayenshi. Itama ta shige ɗaki fuu su Yaya Hambali suka mara mata baya.
"Wallahi ina shirin taka mishi birki kenan kika tanka Babala. Akan mitsiyaci Gwadabe za a shigo har fadarki ai miki ɗiban albarka. Anya Baba Magaji yana ƙaunarku kuwa?" Cewar Yaya Hambali "
"Inafa yake ƙaunata. Ai Shikenan babu kare bin damo, yaje gashi ga Gwadaben, shima bai iya gyara gidanshi ba, ya kasa haɗe kan matanshi sai gidan wasu zai shigo ya gyara"
Chapter 30 · 0% Book details