Sashe 48
Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ta inda za'a haɗa Uwani da kishiya irin wannan ba. Ko da yake ita mace duk lalacewarta da ƙauyancinta tana da tata baiwar da Allah ya huwace mata. Dan a hakam saita zama zarah a zuchiyar Hafizu. Shigowar su Hafizu da sib me murfi huɗu ce tasa na dawo hayyacina. Amarya a ara mana tsintsiya dan Allah " Ɗan murmushin yaƙe tayi tace. "Wallahi gidan bani da tsintsiya. Nima da tsumma nake sharar ɗakina" Ai sai na rike baki tsintsiyar laushi ta nera goma ace ta gagari yarinyar mace. Kuɗi na ciro na ba Ummi nace. A siya tsintsiyar laushi data zabori, sai abun kwashe shara, da kwandon shara. Ki siyo kwandon sharar babba da ƙarami, a siyo omo." Nan da nan ummi taje ta siyo dake layin cike yake da shaguna. Tas muka wanke ɗakin muka koro ruwan tsakar gida. Amarya ta bamu tsumma muka goge ɗakin. Muka shirya ɗakin Amarya tas da taimakon Hafizu sai ɓare_ɓare yake yi har ciwo yaji garin shigar da madubi. Amaryarshi sai harara take doka mishi. Ummi nasa ta share tsakar gidan ya dawo saiti, nasa suka wanke ƙazamin banɗakinsu mai zarni da warin masai. Bamu muka bar gidan ba sai biyar na yamma. Zuwa bayan Isha na raka uwani gidanta. Muna shiga ɗakin ta kalli ɗakin ta sharce hawayenta tace. "Iyabo ni kam zan sai gida madaidaici kamar wannan ni da yarana saimu koma. A ɗakinnan ta ina zan soma kasuwanci, banga inda zan ajjiye dilolina in sun ƙaraso ba. Nifa Iyabo haƙurin da zanyi a gidannan na kafin a samamun gidane in siya" Dafata nayi. Uwani babu laifi dan kinyi hakanma. Nima kuma na goyi da bayan ki sai gidan naki ki ware kan ki. Ni zan tafi ƙauye gobe sassafe, in dilarmu ta iso nasan zaki karɓo mana ki ajjiye mun tawa a wajenki. Ni kaina jikina yana bani zanje in tarar Yaya Hamma ya cika gidanshi da Mata, uwani gashi Allah ya jarabceni da tsantsar sonshi. Tsaki tayi tace. "Ni bawai Hamma bai cancanci ki soshi bane. Ni gani nake kashe rayuwarki kawai zakiyi in dai Hamma kike son ki aura. A wannan ƙungurmin ƙauyen kike sha'awar rayuwa alhalin na ƙauye suke fitowa birni Iyabo. Kiyi nazari, ki kuma auna Hamma da Salim, sannan ki yi nazari mai zurfi kafin ki je ki faɗa abinda zai zame miki matsala. Rayuwarki ce kece zaki zauna" Da wannan mu kai sallama na koma gida. Nima da wannan nake cewa daku sai gobe in Allah ya ara mana rayuwar.