Sashe 43
Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin gidan Malam
Anata hada_hadar ɗaura girkin rana. Yayin da baƙin da suka taso daga nesa suketa haramar komawa garuruwansu tunda dai biki ya ƙare.
Baba Suwaiba da Amaryar Malam suna dai cikin danginsu anata hada hadane. Amman zuchiyarsu a cike take tab da tsoro da fargabar Malam. Malam ya ɗauki zafi sosai, hatta gaisuwarsu yau Malam yaƙi amsawa abinda bai taɓa yi ba kenan. Kuma ya sake jaddada musu lallai su zauna da zaman shirin dole zasu tafi gidajensu. Kafin ace abinci ya nuna tuni rabi da kwatan baƙin biki ko wacce ta kama gabanta, sai tsirarin ƴan uwa da su kai ragowa su kuma sai zuwa gobe zasu watsr. A ɗakin Baba Suwaiba duk ƴan uwanta sun watse. Amaryar Malam kuma dama mutum ukune suka zo daga ɓangarenta, sai ƙawayenta na maƙota, kasancewar ba ita ke aurarwa ba. Ɗakin Baba Fhatsima ma Altine da Balarabane kaɗai su kai saura, sauran dangi su ana gama karin kumallo ma suka tattare yanasu yanasu suka kama gabansu. Ɗakin Baba Asshine yake cike da jama'a sosai dan su ko soma raguwa ma basuiba. Ƴan takai ma su Laila suna nan, sai su Ayashe, da dangin Amaryar gwadabe, da su Bara'u wanda su kuma gobe zasu kama hanyar suma.
DAKIN BABA FHATSIMA:.
Balaraba sai faman gyarama Baba Fhatsima ɗaki take yi, ko ina kaca_kaca shine take son ta gyara komai ta ajjiye a mazauninshi. Baba Fhatsima tana zaune sai ta dubi Balaraba tausayinta ya kamata. A ranta saita ƙudurce zata tuntuɓi Tasi'u da batun Balaraba ko Allah zaisa a dace yaji ya amince zai aureta a karo na biyu. Dan Balaraba yarinyace mai hankali sosai, kuma bata da wata makusa da za a ƙita dominta.
"Altine gobe Balaraba ba zata biki ba. In zaki tafi ita ki barmun ita. Akwai tunanin da nake yi ne. In hakan ya tabbata zaki ji, amman ki barmun ita gaskiya. Daga Balaraba har Altine wani daɗine ya lulluɓesu dukkansu sun gane inda ita Baba Fhatsiman ta dosa. Kuma shi kanshi Tasi'u ya nuna kamar har gobe yana jin Balaraba a ranshi.
"Shikenan Yaya Balaraba ai taki ce kumfi kusa, gata nan" Dariya Baba Fhatsima tayi tace.
"Balaraba ai zaki zauna tare dani ko? Duk da babu sa'anninki a gidan. In yaso dan kar kaÉ—aici ya dameki ba sai ki koma islamiyya ba?" Balaraba tace.
"Zan zauna Baba ba komai ai nanma gidanmu ne" Tana gama faÉ—ar haka ta fice É—akko abin kwashe shara.
"Shikenan Yaya Wallahi naso in ɗakkota in kawota wajenki ko wajen Yaya Dije. Acan gabana in banda kuka da damuwa babu abinda take yi. Kinga nan kuma birnice ai nima zanso tayi aurenta a birni. Inta koma islamiyya zata ƙaru sosai. Sai dai bata ɗebo kata da yawa ba" Baba Fhatsima tace.
"To in banda abinki ai da kin kawota. Batun kaya kuma Yayansu zai siya mata a É—iÉ—É—inka mata ta samu na cin zawarci. Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi. Kije ku duba abincinnan fa ko ya nuna. Kwanciya nake son inyi ko ina ciwo yake yi mun an sha kacaniyar biki. Da kuke_koken yara"
Ta bangaren Angwaye kuma, suna É—akinsu na samartaka suna zubar da zance gami da tsokanar juna.
Gwadabe dai Baya cewa uffan sai murmushi, jiya ya ƙara tabbatarwa cewar Iyabo na da wata baiwa da ba ko wacce mace bace zata iya samu ba. Rabuwarshi da Iyabo sai ya sake dawo mishi ɗanye. Har ya gama haɗa ƴan kayanshi da basu shige kala shida, da jakar magungunanshi baice komai ba. Bara'u kuwa ya ƙura mishi idanu yana nazartarshi, tuni ya bugo kuwa jirgin nashi, abotar wasan ƙasa ba abota bace ta wasa. ( Fatima Abdullahi Owuna zanso ace kina karatun littafin Hausa, da a daidai wajennan zaki tuno lokacin muna yara). Hannun Gwadabe Bara'u ya ja zuwa waje, Tamu dama baya ɗakin yana wajen Ayashe suna tattaunawa dangane da maganar barin toye da kahinde da Gwadabe yayi musu.
"Gwadabe wai shin duk zuƙa_zuƙan matannan kana nufin basu isa sun maye maka gurbin Iyabo bane? Ya kai da kake da Amare kana tunanin matar da ba mallakin ka ba. Babu mamaki Iyabo tana gidan wannan wan nata Debisi tana aurenta cikin kwanciyar hankali tama rufe shafinka, ta shimfiɗa sabuwar rayuwa. Matar da ko yaranta bata sake waiwaya ba shekara biyu fa."
"Sabida kasan naƙi jinin Debisi shine ma dalilinka na danganta Iyabo da aurenshi" Da gaske sai gabaki ɗaya ya hautsine. Bara'u kuwa mai zaiyi ba Dariya ba. Dole shima Gwadaben ya dara, tare da dorawa da faɗin.
"Kana ji. Aishi tunanin Iyabo tamkar numfashina yake. Zare tunaninta a gangar jikina daidai yake da zare numfashina. Bara'u Iyabo mutum ce harda ɓari kai shaidane kan hakan, kuma ta cancanci a dauwama ana tunanin ta tare da binta da fatan alkhairi. Fatana shine Allah yasa iyakar ƙarshen wahalar rayuwar Iyabo ya ƙare a gidana. ina mata fatan samun mijin da zai kula da'ita fiye da kima. Kai dai mu ture batun Iyabo mu dawo batun yara. Bara'u."
"Dakata malam dallah. Nina faÉ—a maka gaskiyar abinda yafi dacewa. Ka zauna da matanka a nutse ka gama gane kansu tukunna. Toye saiya gama firamare zai dawo hannunka zancan gaskiya kenan. Zuwa lokacin suma ko wacce da nata. Da yazo saiya faÉ—a sakandare kai mun wannan alfarmar." Dariya Gwadabe yayi yace.
"To Shikenan hakan za ayi duk yadda kuka ce. Shi Tamu yama ƙi yadda zai bani yaran. Naga Toye da Husna sunyi wani irin shaƙuwar data haure misali, ko hakan hujjane. Babu komai in suma sai sun gama firamare ɗin za a bani su duk babu komai" Ana haka sai ga Tamu ya shigo ɓarayin.
"Me ake tattaunawa aka wani ja gefe?" Cewar Tamu. Bara'u kuuwa yace.
"Maganar Iyabo muke yi daka ganmu" Ƙarasowa yayi kusa dasu yace.
"Baiwar Allah. Alkhairan Allah ya kai mata a dukkan inda take. Kai kuma Gwadabe Allah ya baka haƙurin rashinta. In sha Allah nan ba da jimawa ba Toye da Kahinde zasu maye maka gurbin Iyabo a zuchiyarka ta ɓangaren soyayya. Amman Ayashe ta ba da shawarar ka ɗan ƙara haƙuri yaran su sake girma ta yanda za a iya morarsu sai mu dawo dasu. Kafinnan sun samu ƴan uwa ma dayawa su kansu sai sunfi sakewa"
Haka dai wunin na yau shima ya mutu murus. Sai zuwa bayan ishane Gwadabe ya samu suka shigo cikin gidan. A ɗakin Hadiza suka ya da zanzo. Ɗakin yasha gyara sai ƙamshin turaren wutan Sandal yake yi. Ita kuma tana kitchen tana ƙoƙarin ƙarashe girkin dare. Kitchen ɗin Gwadabe ya bita bata san yana tsaye yana ƙarema ado da kwalliyarta kallo ba. Ɗagowar da zata yi zata buɗe kula babba danta zubo abincin harda su Bara'u carab sai suka haɗa idanu. A take suka sakarma juna murmushin so, Gwadabe harda lumshe idanu dan wani maganaɗisu ke ɗibarshi. Shi Allahn da yayi shi ya kasance mai son mace mai kwalliya da ado, uwa uba son ƙamshi. Kuma ya lura matan maraɗi ba baya ba wajen iya Ado.
"Sai yanzu kuka samu shigowa?" Ta tambayeshi cikin kulawa. Da kulawar shima yace.
"Muna kofar gidan tun yamma, gidanne cike dam da mata abinda ya hanamu shigowar kenan. Su Auwala duk tare muka shigo. Ba a kawo abinci daga cikin gida bane naga kina girki?"
"An kawo tuwon ɓula su ka yi ne, tunda naga kana da baƙi shine nace bari in dafa shinkafa fara da maka, tunda ina da miya sai ku haɗa. " Abincin ta zuba ta haɗa plate da cokula, ga ruwa a babban jug me kofuna shida. Gwadabe ne ya taimaka mata wajen shigar da kayan abincin..".
"Hadiza ki yi mun kiran Shafa tazo mu haÉ—u aci abincin. In aka kammala sai mu É—anyi muku nasiha" Jimm Hadiza tayi, ba ta dai ce komai ba, can sai tace.."
"Ina ganin kai yafi cancanta kaje ka kirata. Tunda rabonnu da kai tun safe" Bara'u daya cusa nama a baki yace.
"Nima abinda zance mishi kenan uwar gida. Kuma ko babu komai akwai iyaye a ɗakin a gaggaisa" Miƙewa Gwadabe yayi ya fice. Hadiza tabi bayanshi da kallo. Ji take yi tamkar zuchiyarta bafa zata iya jure zaman kishi ba. Su Bara'u suna ɗan janta da hira dan hila. Amman taƙi hilatuwa hankalinta na bakin ƙofa taga a yaya zasu shigo. Ga abinci ta zuba ita da Gwadabe ta saka cokula biyu. Shi yana gaba ita kuma tana bayanshi. Saye da materiyal ɗinkin riga da siket wuyan rigar kuma faralas ne. Sai mayafinta da babu ta inda ya dace da shigarta. A ƙasa ta zauna kamar yadda taga Hadiza a ƙasa. Ganin abinci a gaban Hadiza sai Gwadabe shima ya zauna a ƙasa kusa da Hadiza sai ya zamana shi da'ita suna fuskantar Shafa.
Mrs Bukhari