Sashe 46
Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
IYABO:. Lalubo lambar Yaya Hamma nayi a wayar Faty na danna kira. Nan take zuchiyata ta shiga harbawa fafafat, ina jiyo motsin sonshi a zuchiyata. ( M Farida Ana magana )Sau uku ina gwadawa number bata ma shiga, kamar ma layin a Æ™asa yake baya cikin waya. haka dole na haÆ™ura, na bari zuwa wayewar gari, in sake jarabawa ko Allah zaisa in dace. Bacci a ranar lafiyayye muka samu mai nutsuwa. Bayan munyi sallar asuba ma bacci muka sake komawa ba mu muka tashi daga baccinnan ba sai azahar, ni dai akwai gajiya marar adadi tattare dani, haka ma Uwani. Faty kuma dama ita É—abi'ar baccinta kenan. Alwala muka É—auro bayan duk munyi wanka. Kayan jikinmu muka mayar dan kayanmu na cikin mots ba'a sakko dashi ba. Ina sallah Salim ya shigo, abinci ya kawo mana da burosai na goge baki da makilin. Kafin in idar ya fice. Ina idarwa ya sake shigowa da wata zungureriyar leda shaÆ™e da dogayen riguna da takalma harda agogo, da tarkacen kayan kwalliyan mata harda turare. Ya miÆ™o mini, nasa hannu na karÉ“a ina mai mishi godiya. Sai cewa yayi dani da harshen larabci. "Ki shirya zan gabatar dake a wajen dangina. Kakata ma tana nan sai su ganki" Na dubeshi, sai yayi mun murmushi. "Tuni labarinki duk ya karaÉ—e familyna. Na faÉ—a miki sonki nake yi da aure ba da shashsnci ba. Tun rabuwar dake zuchiyata bata huta ba wajen begenki da mafarkin mallakarki" Ya sake faÉ—a. sai na gyaÉ—a kaina nace mishi. I am coming ( ina zuwa) shiga uwar É—aki nayi na tarar da Faty tana waya. Uwani a falo na barota. Faty wai ashe da gaske salim yake yi aurena yake so yayi? Kinga fa kaya ya bani wai in saka mu sauka Æ™asa zamu gaisa da iyayenshi. Sai ta zare wayar a kunnenta tace. "Kwarai kuwa. Komai a rayuwa yana da sanadinshi. Da kina Najeriya babu dalilin da zaisa ku haÉ—u da Salim har ya soki, tunda baisan hanyar Najeriya ba." Faty akwai Matsala ne akwai É—an uwana da mu kai alÆ™awai dashi kafin in baro Æ™asata" BuÉ—ar bakin Uwani wacce shigowarta kenan sai tace. "Akwai dai wanda kika É—afa sonshi a ranki dai banza. Yanzu haka yama mance dake. Babu mamaki in mutumin Æ™auyene kije ki iskeshi da mata huÉ—u ma, kinga babu wajen zamanki a gidanshi ai. Yanzu kamar wannan bawan Allah yaji sonki kina neman kisa Æ™afa kiyi fatali da damarki. Wai Iyabo a Æ™auyen Æ™ayayau É—innan kike so kiyi rayuwa, kina É—aukar tallar nono aka? Ke sha'awar rayuwar kenan kike yi. Koko sabida fari, gashi da tsawon Hamma ke ruÉ—arki? Duk da dai nasan ba hakan bane tunda Salim ya kere Hamma a komai. Amman dai Iyabo Allah ya wadaran wannan zuchiyar taki ta gaban Æ™irjinki" Ta Æ™arashe zancan ta tana hararata Turus nayi ina kallo da sauraren Uwani da take ta balbalin faÉ—a kamar Uwata. Faty ce ta katse hirar da cewa. "Yanzu dai ki shirya kije ki dawo mayi magana. Uwani mu karya kafin ta dawo" Ni dai a tsorace du nake. Doguwar baÆ™ar riga na saka mai shegen kyau, da takalmina baÆ™i mai tsini, na yane kaina da mayafin rigar tare da feshe jikina da wani turare mai ruwa ja. A tsaye a inda na barshi na sameshi. Ba sai mutuminku ya nemi lalacewa dan kallona ba. Ni kuma sai kunya ta kamani a raina sai nake ayyana. Wannan kallo da yake yi mun kallon yaudarace kawai, su da suke da haske da kyau, matansu Allah ya basu diri da cikar Æ™irji. To ni meye a jikina na kallo da har za'a shagala in ba É“aka_É“akan mazaunai ba? Ashe shi yasan dalilin, tare da larabawa masu auren É“aÆ™aÆ™en fata, da turawa masu auren baÆ™aÆ™e su bar kyawawan fararen matansu. Haka muka gangara a jere muka tadda ahalin gidan a daining table babba suna cin abinci. Da ganina wata tsohuwa ta iso inda muke ta riÆ™o hannuna har gaban daining É—in. Zaunar dani tayi a kujerar kusa da wani tsoho. Shima Salim ya samu waje ya zauna. Jikina yana É“ari na gaishesu da larabcina irin nami na Æ´an koyo. Da soyayya gami da fara a suka amsa mun. Ya dinga nuna mun Æ´an uwanshi, yayye da Æ™annenshi. Ga mahaifiyarshi da mahaifinshi, sai kakarshi da mijinta, sai kuma Yarshi Sarla da mijinta Umaid. Ni dai duk ina zaune a mugun takure, su kuma sai jana da hira suke yi. Mahaifiyarshi ta tambayeni asalina. Ban É“oye mata komai ba kama daga yarena, izuwa aure da nayi a baya da adadin yarana. Duk da haka sun yi na'am dani. Abu guda dana fahimta da larabawa ko basason abu. Muddin yaransu ya nuna Yana so, to suma zasu koyi son wannan abun. Suna da son yara, su kuma yaran sai suke Amfani da hakan wajen tursasama iyayen son ra'ayinsu da yarda dashi. Gurasa da nono aka zuba mun sai shayi, a kunyace na É—an cakala Salim yace in tashi ya mayar dani. Sai mahaifiyarshi tace ba za'a yi haka ba. Ya É—aukemu daga É—akinshi ya dawo damu wani É—aki dake kusa da nata, É—akin Æ™anwarshi dake karatu a landan. Haka kuwa akayi, É—akin yafi nashi kyau da kuma yalwa. "Ku shirya zuwa dare sai mu fita daku kuyi siyayya, ku ga gari kuma." Cewar Salim bayan mun samu keÉ“ewa nake sanar mishi ni Najeriya muke son komawa, zaman bautar da muke yi ya ishemu. Anan yai mana alÆ™awarin zaiyi mana cuku_cukun visar da zamu koma, zaima biya mana, amman in mishi alÆ™awarin zan bashi damar kafa soyayyarshi a zuchiyata dan shi da gaske aurena yake son yi. Tuni na amince mishi da hakan magana ta domin Allah ba har cikin zuchiyata ba amma. Da daddare ya fita damu zuwa wani super maket babban gaske na suturu masu tsada da masu arha duk gasu nan. Mu ka dai tsittsinci abinda ba a rasa ba haka. Ya biya komai muka sake nausawa zuwa zagayen cikin gari. Ni dai banyi Æ™umun baki ba nace mishi ni kam inason yin Umara. Ranar juma'a yai alÆ™awarin zai kaimu da izinin Allah. Ai kuwa hakan akayi. Daga umara muka shiga kasuwar DOGON GIDA dake Makka. Anan muka ga dandazon maza da mata na Najeriya iri iri. Ga gumama a zube a Æ™asa, ga sababbi, zannuwan gadone, takalma. Komai da komai dai. Nan Faty ta dinga kutsawa damu. Siyan kaya muka dingayi. Ni da Uwani mune harda maÆ™ala haÆ™ori makka bibiyu a bakunanmu. Adai taÆ™aice mun kaso kuÉ—i masu yawa, daga haka muka koma Jidda, nanma suna da babbar kasuwa Faty ta kaimu, ni har dilar zanin gado, da kayan mata dogayen riguna da takalma na siya za a É—auro mun a jirgin kaya. Æangaren kayan kitchen hatta plate da cokali saida na siya, na sai manyan kuloli kala biyu, masu filas na shayi. Uwani kuma dila biyu na zannuwan gado da dilar Kayan sawan yara ta siya. Daddumai, da carbi, bagaruwa, dabino, ruwan zamzam kuwa sunfi komai yawa a tsarabarmu. Naima Dada tata tsarabar, naima Iyaa Debisi nata daban, naima Yaya Hamma nashi daban shima. Su BoÉ—É—o kuma saina isa Najeriya zansan mai Zan cire musu dai, ragowar kuÉ—aÉ—en muka canjasu zuwa kuÉ—inmu na Najeriya.. Duk wannan siye_siyen da taimakon Salim, da taimakon mahaifiyarshi danta bani kuÉ—i a gaskiya masu kauri. Suna da wani irin karamcin da a É—an kwanakinmu a gidan Salim harya soma samun gurbin zama a zuchiyata. Kwananmu takwas a gidansu Salim Allah ya kawo lokacin dawowarmu Najeriya, mahaifiyarshi da danginshi su kai mana goma sha tara na arziki, har zoben gwal yarshi Sarla ta bani É—an Æ™arami na maÆ™alashi a hannuna. Duk tarin kayayyakinmu mun É—aure zasu tawo a jirgin kaya wanda akace bazai wuce wata É—aya ba zai iso. Sai Æ´an akwati da jakunnanan kaya, da jakar hannu kawai muka riÆ™e. Har filin jirgi Faty ta rakamu, Salim shima yana wajen tare da Yarshi. Sai sake jaddadamun yake yi akan in riÆ™e mishi alÆ™awari, sannan zai biyo adireshin gidanmu na Kano dana bashi yazo a kawoshi har Æ™auyanmu nanda sati biyu in ya rage abubbuwan dake gabanshi. Sarla itama sai sake roÆ™ona take yi akan kar in yaudaran mata É—an uwanta. Zai zo da kanshi neman aurena. Ni dai duk sai jikina yayi sanyi tuÉ“is, har na soma kokonton wanda zan É—auka da wanda zan ajjiye. ( To masu karatu wannan zaÉ“i ayi daku. Ku wa kuke ganin ya cancanta Iyabo ta É—auka Hamma ko Salim?) "To Faty Allah ya sada fuskokinmu da Alkhairi. Zamu dinga waya in sha Allah. Da haka mu kai sallama da juna. Muna hawayen farin cikin komawarmu Æ™asarmu Najeriya. Faty tana kukan sabo, Salim da Sarla suna cikin alhini da fargabar kar in yaudaresu. Da misalin Æ™arfe Taran safiyar ranar laraba jirginmu ya tashi daga king Abdulaziz Airport jidda. Tafiyar awa biyar da minti hamsin da biyar ce ta sauke mu a Airport na Legos Murtala Muhammad. Kai tsaye daga Airport muka wuce tasha. Wata sassanyar iskar Æ´anci na kaÉ—amu zuchiyoyinmu cike da farin ciki marar adadin kwatance. Tiket muka siya, motarmu sai Æ™arfe biyar na yamma zata tashi tafiyar ta dare ce. Masallaci muka samu mu kai Sallah. Uwani muje mu nemi abinci mu ci yinwa kamar zata kasheni" Na faÉ—a ina riÆ™e cikina. Wani É—an Æ™aramin gidan cin abinci muka shiga. Abinda suke siyarwa tuwon eba da miyar ganye, sai sakwara da miyar egusi. Sakwarar muka siya da nama gunduna_gunduma. Muka ci mu kai Æ™at, kana muka koma masallaci, mun bar motar da zamu shiga anata lodin kaya. Bayan la'asar muka shisshiga mota kowa ya zauna a muhallin zamanshi. Gaga_gaga sai gamu a Kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika da misalin Æ™arfe shiddan Asuba, garin da duhunshi a lokacin. A tasha muka sallaci asuba. Uwani gidanki kika nufa ko gidan Hajiya?" "Gidan Hajiya dai zanje, in yaso shi Hafizun yazo ya sameni a gidan, zan aika Habu ya nemoshi" Mota muka shiga har zuwa bakin layinmu. Muna sauka sai gamu ga Lekan da abokinshi suna atisaye. A guje Lekan ya karaso. "Ahh Antimi Iyabo. Okaabo" Farin cikine ya lulluÉ“eni marar adadi. Jakunkunanmu suka kinkima, abokin Lekan yabi Uwani, ni kuma Lekan ya bini. A kofar gida muka samu Iyaa Debisi tana shara, ga shago harta