Sashe 3
Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a ƙofar gida, zaman me kake yi a wajen?" In ji Daso kenan. Dariya yayi mata kawai kafin yace. "Tunda dai Allah ya ƙaddari ganawarmu ai shikenan. Babu gaisuwa sai tuhuma ko? Da fatan kun tashi lafiya" Muka amsa a tare, sannan mu ka gaisheshi cikin girmamawa. Gidansu Yaya hamma muka soma zuwa. A ɗakin Yafendo muka zauna, a gurguje mu ka gaisa na sanar mata inaso zanje birni amman kwana biyu zanyi. "To Allah ya dawo dake lafiya. Hamma sai ka kaita har tasha ka tabbatar motarsu ta tashi kafin ka dawo. Allah ya tsare. Hama da Boɗɗo suna garken shanu kuje ku samesu ko? Ke kuma Daso kizo in kin taso tallan Nono zamu yi magana muhimmiya dake" Kan Daso a sinne ta amsa da "To Yafendo" A garken shanu muka yi sallama da Hama da Boɗɗo. Sai adda'a su ke yi miki, daga nan sai wajen Dada. Ni da Daso ne muka shiga, Yaya Hamma fur yaƙi shiga yace Baffa faɗane dashi bai fiye son baƙi suna shigar mishi gidanshi ba. Mu ma muna shiga ya taremu harda sanda kamar zai dokemu. "Kai ku tsaya nan kar ku sake ko taku ɗaya a wajen" Ya faɗa da fillanci, Daso ce ta fassaramun abinda yace. Wannan kalma daya faɗa kamar ance Dada ta fito ta duba sai firit ta fito daga bukkarta. Su Cubu kuma da su Yusufu suna tsakar gidan, suna aikin dafa madara. Da sassarfa ta iso inda yake tsaye. Wallahi ɗaga sandar shi yayi kamar almara sai ya kwaɗa mata a goshinta jini ya yayi tsartuwa har a hijabina" Cikin hargagi yake yi mata magana da fillanci. Hannunta ta dafe da goshinta ta yi saurin juyawa, na fahimci umarni ya bata. Yusufu da Cubu ne suka yi kanta Cubu ta riketa zuwa ƙofar bukkarta. "Ku je Jabu. Zan dinga zuwa dubaki. Na mancene ban sanar miki ba ya kafa dokar kar ƙafarki ta tako mishi gidanshi" Da yarbanci tayi mun Magana. Ajjiyar zuchiya na sauke ina hango irin yadda sandar ta sauka a goshinta, ba tare da wani babban daliliba, ko da dalili addini ya bada umarnin a daki mace har a zubar mata da jinine? Ko da ma suna da ƙarancin ilimin addini, rayuwarsu a kiwo da tallar Nono take ƙarewa. Ji nayi na sake jin ƙarfin guiwar hukuncin dana yanke dan cire Dada a cikin wannan uƙubar. Hawayen daya zubomun nake shirin gogewa Baffa ya ɗaga sandarshi ya sauke mun a kafaɗata, zafin ya ratsa dukkan ƙasusuwan jikina kau,. Kafin in tantance tsakanin mamaki da tsoro naji Daso tayi ihu ta jani mun rufa waje a guje. A guje muka wuce Yaya Hamma. Sai biyo mu yayi da sauri yana tambayar ba'asin abinda ya haddasa gudun. Daso ce ta bashi labarin abinda muka tarar. Ni kam hawaye kawai nake sharewa ina kallon mayafina da jinin Dadana a jiki, sanadiyyar zuwa ganinta kawai aka zubar mata da jini. "Jabu kiyi haƙuri. Mu kanmu mun rasa yanda zamu yi mu tsamo Dada daga cikin halin da take ciki a wannan gidan. Amman abinda nake so dake shine dan Allah ki taya ta da adda'a, kuma zan baki shawarar kada ki sake zuwar mishi gidanshi, Dada zata zo har inda kike ta dubaki. Kar hakan yasa in kika tafi ki ƙi dawowa, hakan ka iya jefata a halin da yafi wanda take ciki yanzu. Zamanki tare damu zai iya kawo mata sauƙi sosai, kece babba ke zaki dinga rarrashin ƙannenki, kinga Boɗɗo kullum a cikin kuka da damuwar da Dada take ciki take." Ajjiyar zuchiya na sauke kawai nace. Babu komai, nagode da shawara. Daso ku koma daga nan ni zan tafi" "A'a ai kinji abinda Dadanmu tace dan haka har sai na tabbatar da fitar motarku a tasha. Daso ki koma gida ke" A wajen mu kai sallama da daso. Ni dai har muka gama wannan gwajab_gwajab ɗin fita zuwa gari hankalina baya ma tare dani. Wai duk haka Aure yake cike da ƙalubale kowa da irin nashi? Oh ya Allah ka kawo mafita a zamantakewar aure, ya Allah ka ba ma mata mafita. Har muka shiga cikin babbar tashar Adamawa babu wanda yace da wani ƙala a tsakanin ni da Yaya Hamma, dukkanmu sai tubka da warwara kawai muke yi, tare da karanta wasiƙar jaki. "Fullo Kano ne, ko Kaduna, ko Zaria ga motar Haɗejiya?" Cewar ma'aikatan tashar da suka nufo kanmu har suna rige_ rige. "Kano zata je, nawa ne kuɗin motar?" Cewar Yaya Hamma, tare da cusa hannu a aljihunshi. "Nera dubu da ɗari biyu zata biya" Kuɗin ya zaro ya kirga ya basu, ni kuma ya miƙo mun dubu da ɗari biyar. Ƙin karɓa nayi, ya dubeni rai a ɓace yace. "In baki karɓaba zaki barni cikin damuwa, da kokontan dawowarki rugar mu. Ni kuma dana tuna zaki iya ƙin dawowa, ko zaman rugarmu ya isheki take sai inji fargaba ta dirarmun. Jiya ɓarawon baccine ya ɗebeni shima cike da mafarkai akan tafiyar taki. Ungu kuɗinnan ko tsaraba kya yi musu" Nagode sosai Yaya Hamma, in sha Allah bazaan wuce kwana biyun ba. Kuma dan Allah ka je ka dubo Dada, ko a ɓoye ne ka kai mata magani, kai mata bayani kwana biyu zanyi" Yaya Hamma bai bar tasharnan ba har sai da ya ga fitar motarmu. Sai da motarmu ta yi nisa sosai na dena hango hannun Yaya Hamma a sama yana yi mun Adabo., ban dena waige ba har sai da na dena hango shudiyar rigarshi, Ajjiyar zuchiya na sauke na lumshe idanuna ina tunano yanda Baffa ya kabɗama Dada sanda. Wannan dalilin ne yasa kullum in zanga Dada sai in ganta cikin rashin guzari da rashin walwala, kullum cike take da tunani. Ta haɗu da azzalumin miji mai kafiya, tallar Nono ya cinye mata lafiyarta da kuzarinta. A shekarunta ya kamata ace tana zaune a nutse yaranta na hidinta mata, ba wai tai ta fita tallar nono, kuma mijinta na cin zarafinta harma da fitar mata da jini. Wallahi da Baffa zai iya amincewa in fanshi tallar Nonon Dada, da tuni na famsheta na zama ƴar tallar Nono kamar yadda ya zama al'adar matan fulani musamman mazauna rugage. Ya zame mun dole in yi duk abinda ya dace dan ganin na kawar ma da Dada Ƙwallar data daɗe tana zuba a idanunta. Gaga_gaga haka mukaita cin hanya, azahar, la'asar sai dab magriba muka shiga garin Kano, a unguwa uku muka sauka, ina fitowa titi na samu Bus har ƙofar layinsu Uwani. Na ko yi sa'a tana gida, tana tsakar gida tana kwasar tuwo Hafizu kuma yana shanya kayan yara a igiya. Tana ganina ta sau marar hannunta ta miƙe a zabure. "Iyabo kece haka afujajan?" Tana faɗin haka na fashe mata da kuka a tsakar gidan kamar ƙaramar yarinya. "Uwani jata kuje ciki maza" Cewar Hafizu. Hannuna Uwani ta ja muka shiga ciki, wallahi na fi minti talatin ina kuka take zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni. Uwani da Hafizu suka rufu a kaina suna ta rarrashina da ƙyar na haɗiye kukan nawa bakina na ambaton Allah. Ganin na ɗan samu nutsuwane Hafizu ya fita ya bamu waje. "Kawata lafiya kuwa kinga yanda ki kai baƙi kika rame kuwa? Gabaki ɗaya kin koma wata ƴar ƙauye, meke faruwa haka?" Cikin shessheƙa nace. Labarin da tsayi Uwani, amman bari in rama sallolina sai mu tattauna tunda abinda ya kawoni wajenki kenan" Ina gama faɗar hakan na miƙe jiri na kwasheni na fito tsakar gidansu dan kama ruwa da alwala. Uwani kuma taci gaba da aikin tuwonta, ina kan yin alwala yaran Uwani suka shigo gidan da sallamarsu. Matar gidan buɗar bakinta tace "Wannan wacce iriyar rashin tarbiyyace zaku shigoma mutane gida da gudu, kalan ku zubar mun da miyar da ko kayan ɗakin uwarku in an siyar bazai siya miyar ba?" Yaran su kai turus, ni dama nasan irin matsalolin da Uwani take fuskanta a gidannan shi yasa ban yi mamaki ba, gashi uwani ta kasance kamar zawayi wajen rashin haƙuri ai kuwa nan ta tanka. "Maman Shamsu kenan. Baƙin cikin ki takashinki zai koma da izinin Allah. Ni Uwani nafi ƙarfinki, kuma in mijinki yafi nawa mijin kuɗi, ai ni na fiki more aure tunda mijina bai taɓa zagin iyayena ba. Kuma bai taɓa korata da watan azumin ramadana ba, dan haka ki iya bakin ki" A mugun zafafe Uwani tayi maganar cike da hargowa. Yaran na kaɗa ciki dan gudun kar su kantamo kalmomin da suka shige shekarunsu. Da Uwani da maman Shamsu sun ci uwar sabada har sai da mazajensu suka dawo daga masallaci suka raba wannan ja'iba, dan wallahi na kasa riƙe Uwani sam, har zani Maman Shamsu ta fincike mata ya rage daga ita sai gwari na tsuma ( siket ɗin ciki). Ɗayar matar gidance ta ɗaukoma Uwani zanin ta ɗaura. Baban Shamsu cikin son bin goyen matarshi ba tare da bin ba'asin abinda ya faru ba yace. "A ɗayan biyu ya kamata ko ku ku bar gidannan, ko kuma mu tashi mu bar muku gidan. Wannan bala'in yayi yawa dan watarana wannan jarababbiyar karyar matar taka zata iya illatamun mata'" "Karya kace mata Ƙasimu? Uwani ba karya bace tunda bata leƙen mazan mutane in sun shiga bayan gida. Uwani Iyabo ku shige ciki kar ku tanka musu" Shigewa mu ka yi mu ka barma Hafizu faɗan. Matan gida sai ihu suke yi. Nifa harna rama sallolina ba'a dena gwabza habaice_habaice ba. Wannan ta jefa ma wannan, waccan ta rama, Uwani na tsaye a bakin ƙofa riƙe da labule sai ɓarin zance take ta faman yi. Yara kuma sai cin tuwonsu suke yi a yinwace." Uwani dan Allah ki rabu da Maman Shamsu ki shigo mu tattauna matsaloli" labulen ta saki muka shige uwar ɗakinta duk muka yada zango a kan katifa" Wai Uwani me matarnan take nufi dake ne haka?" "Sharri mana, baƙin ciki take yi mini. Jiya jiya fa na kamata tana barbaɗa mun garin magani a ƙofar ɗakina, kinga ɗauki babu daɗin da mu kaita yi kuwa? Mune har gidan mai unguwa fa. Amman kinga ta sake takaloni" Ajjiyar zuchiya na sauke . Labarin duk matsaloli na ba uwani, da ƙudirina da dalilin zuwana wajenta" "Lallai rayuwar mata cike take da ƙalubale mai tarin yawa. Wata matsalarta uwar miji irinki,