← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 60

Sashe 19

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

BABA FHATSIMA
A hotel ɗin dake bayan harami aka sauke Malaman da aka zaɓe aka biya ma aikin umara su da iyalinsu. A baya malam ya samu ire_iren kyautuka irin wannan, kujerar aikin Hajj ma da suka yi da Baba Fhatsima na farko wani ɗan siyasa ne Babba ya bashi, a sakamakon adda'a da malam yake taimaka mishi dashi, kuma yana ganin buɗin haka. Sun je umara da dama, gashi a wannan karon ma Allah ya nufa da'itan za'a sake komawa.
Zaune take akan kujerar dake ɗakin hotel ɗin. Tana jiyo zubar ruwan wankan malam a ƙasa. Zuchiyarta sai take jinta fes Kamar babu wata damuwa dake ƙunshe a cikinta tsawon shekaru. Tunani ta faɗa mai zurfi. Tana tuno lokacin da suka sauka a wannan hotel da suke ciki a shekarun baya. A lokacin Malam yana ji da'ita yana girmamata fiye da tunanin me tunani. Bata mance wasu kalamai da malam ya faɗa mata a ranar da suka shigo makkah da daddare bayan sun gabatar da mu'amalar aure ba.
"Fhatsima samunki nasarane babba a cikin rayuwata. Wallahi Fatsima jina nake yi tamkar wawa soko muddin bana tare dake. A duk lokacin dana kalli ƙwayar idanunki su kaɗai ka iya sauke mun dukkannin damuwata, duk girman matsalar da nake ciki. Ƴan siyasar da muke mu'amala dasu da dama sun sha bani ɗiyoyinsu in aura. Amman Fhatsima nasan ni naki ne ke kaɗai bazan iya haɗa soyayyarki da ko wacce mace ba a faɗin duniyarnan da muke ciki ba."
Fitowar Malam ita ta katse mata zaren tunaninta ta dawo duniyar mutane. Ido malam ya zuba mata ƙur, jin kaifin idanunshi yasa ta ɗago kai suka haɗa idanu. Amman me sai malam yaga kwantaccen hawaye a guraben idanun Fhatsima. Zama yayi a kusa da'ita ya kama hannunta dukka biyu, ɗumin tafukan hannun juna ya ratsasu sosai. Ƙunshinta yake bi da kallo yanda aka jera salateb ( suffa,) akayi ado dashi cikin hikima, lallen ya sake fito da kyawu da hasken hannun nata.
"Fhatsima wannan lallen nawa ne akayi mun?" Ya faÉ—a a mugun raunace dan ji yake kamar yayi kuka. Shi kaÉ—ai yasan irin gasuwar da ruhinshi da gangar jikinshi take yi. Itama a sanyaye tace.
"In ba kai ba Magaji wa zanyi ma lalle uban ƴaƴana?" A sanyaye cike da kunya yace da mamaki ya dubeta dan yasan in tana cikin yarda dashine har take iya kiranshi da Magaji a keɓe, amman dama a cikin mutane da cikin fishi Malam duk take kiranshi."
"Fhatsima yau ni kika kira da uban Æ´aÆ´anki, kuma kikace domina kikai wannan lallen?" Murmushi tayi tace.
"Magaji ai har yau har gobe ruwa na maganin dauɗa" Farin cikine marar misaltuwa ya lulluɓeshi.
"Fhatsima nayi kewar kasancewa tare dake, nayi kewar rashin samun cikakken lokaci kamar yadda kika sabarmun, nayi kewar kulawarki, nayi kewar tausasamun da kike yi Fhatsima. Na sani ni nayi kuskuren ruguza amincin dake tsakanina dake. Wanda in kin tambayeni dalili bani dashi wallahi. Nayi nadamar komai, ina takaicin faruwar komai Fhatsima. Hawayene tab a guraben idanunshi, yana ta girgiza kai irin na kaico.
"Magaji cutuwa iya cutuwa nayi, tun daga lokacin da abubbuwa sukaita faffaruwa dauriyaa kawai nake yi, da ba a iya hawan jini abun zai tsaya ba, numfashina zai rabani dashi, in Barka a duniya da matan naka na so" ÆŠan murmusawa yayi kawai. Baice komaiba ta É—aura da cewar.
"Na fuskanci wulaƙanci da matsi wanda ni kaina bansan ina da irin wannan haƙurin ba. Soyayyarka data yaranmu ce kaɗai tasa naci gaba da rayuwa da matanka. Burina shine ace da kaina naba ɗiyoyinmu tarbiyya a bisa doron alƙawarin da nayi maka tun kafin aurenmu. To Alhamdulillah na sauke nauyi"
"Gashi ƴaƴan da suka fito a ɗakinki sun kasance sanyi da hasken idaniyata Fhatsima. Sun kasance abun alfahari kuma jagorori. Wannan kaɗai wata babbar nasarace a gareki, kuma hakan ya ƙara tabbatar dake a matsayin shugaba kuma uwar gida a gidan Magaji. Ko wacce mace da ƴaƴanta, dani kaina Magaji a cikin rigar alfarmarki nake Fhatsima " Idanu ta ƙura mishi tana mishi dariya shima dariyar yake yi.
"Magaji kai da kaya mallakar wuya ne. Kuma ba'a hana ma ba da rago fata, tuwo baya canja sunanshi. Yarannan baka ragesu da komai ba tun yarintarsu har zuwa yanzu da nake wannan maganar.
Fatana Allah ya haɗe kan iyalin naka baki ɗaya. Duk da kai da kan ka ka farraƙa haular gidanka, kasan....."
"Ya isa Fhatsima kar ki rusamun farin cikin dake ƙunshe a raina" Ya katseta da hanzari.
"Inaso ki tsaya mun kuma ki taimaka mun ke da Tasi'u da Jamila mu haɗu mu haɗa kan iyalinmu. Abinda ya wuce ya wuce, kece zaki taimaka komai ya gudana. Sannan haɗe yaran da matansu ni inata jaddadawa kamar zai iya gyara lamarin. In kan yaran ya haɗe, dole iyayen su shafa ma kansu ruwa. Asshi ce dai nasan zata ba da wahala. Ammam fa a shirye nake tsab da in rabu da duk matar da zata kawo mun taurin kai. So nake in gyara abinda na ɓata tun da rayuwata kar in bar baya da ƙura." Ajjiyar zuchiya Baba Fhatsima ta sauke. Yayin da take hasko abubbuwan da suka zama sune sababin faruwar waɗannan matsaltsalu na gidan Malam. Gani take yi kamar yanzu suke faruwa.
"Baki ce uffan ba Fhatsima" Ya jefeta da tambayar.
"Malam a ɗayan biyu ne wannan haɗe yaran da kai da Tasi'u kuke ganin zai yi tasiri wajen kawo soyayya da shaƙuwa a tsakankanin yaranka. Hakan zai iya faruwa, ko kuma hakan ya sake farraƙa kan yaran, ko da ta Hanyar matayensu, ko ƴaƴan da zasu hayayyafa. Malam wannan lamarin babbane. Amman mu dage da roƙon rabbil izzatu. Gamu a ƙasa mai tsarki mu dage da adda'a Allah yasa hakan ya zama matattakalar da zamu hau tsanin da zai wanzar da farin ciki a tsakanin Ahalinka. Sannan sai ka sanya dokoki masu tsanani, kayi ƙoƙarin dogewa akan dokokin. Kar ka faɗesu ba tare da ka basu mahimmanci ba, wannan raunin naka yana ɗaya daga cikin abinda ya soma kawo rarrabuwar kai a tsakankanin Ahalinka."
A taƙaice dai sun jima sunata tattauna yanda za'a ɓullo ma lamarin. Sun yi adda'a sosai. Malam da Baba Fhatsima sun sasanta kansu sai ɓarzar Amarci ma suke yi abinsu. Sai yanzu ne Malam ya dawo cikin nutsuwa da hayyacinshi. Ya saki ajjihu wajen ganin ya kyautatama Baba Fhatsima, duk da ragowar mata da ƴaƴanshi ma bai barsu a baya ba.
Chapter 19 · 0% Book details