Sashe 24
Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
7 Ajjiyar zuchiya na sauke. Uwani duk abinda kika faɗa gaskiya ne akan Yaya Hamma. Amman a jikina gani nake yi tunda bai furta mun kalmar soyayya ba har mu kai bankwana, to bazai furta mun ba. Kar ki manta kasarfa zamu bari, tunda muka shigo garin Kano ya dace ya fallasamun asirin zuchiyarshi ko?" Dariya Uwani tayi mun. "Iyabo manya. Maganarki haka take. Amman in kin lura Hamma baƙauyene cikakke, babu wayewa a tattare dashi. Ni nafi tunanin ya rasa ta yanda zai furta miki kalmar so ne. Amman a shawarce kar ki bari zuchiyarki tayi zurfi a soyayyar Hamma. Kar mu dawo kiga saɓanin abinda kike tunani azo a samu matsala. Shekara uku ba kwana uku bane. Kuma ƙila mu wuce tsawon wannan shekarun." Haka mu kaita tattauna zantuka ni da Uwani. Dare ya ratsa sararin samaniya sosai. Ma'aikatan cikin jirginne suka soma rabon ruwa da lemo, da soyayyen cincin, da naman kaza. Sai shillawa muke cikin gajimare. Awannmu 6 da minti ashirin muka ji jirginmu ya sauka. Dukkanmu muka cika da murna a tunaninmu mun iso Makka ne ashe ba haka bane, itofiya muka iso. Hajiya Salamatu ta sanar damu zamu kwana a Airport zuwa gobe jirginmu da zai ƙarasa damu saudiyya zai zo. Ta ɗaura da cewa. "Ni daga nan shine iyakata daku. In kuka sauka a Makka Hajiya Mangala zata turo duk a ɗauke ku. Allah ya ba da sa'ar abinda aka fito nema." Daga nan muka ɗunguma inda zamu kwana. Anan muka rarrama sallolin da ake binmu a filin Allah. Washe gari duku_duku jirgin da zai mayar da Hajiya Salamatu zuwa Najeriya ya tashi dasu, cike da fasinjojin Najeriya. Mu kuwa a gantale ga baƙar yinwa haka mu kai ta zama a wannan fili. Gashi cikinmu babu wacce take da kuɗi, ruwa ma sai da mu ka roƙa aka bamu, shima wasu basu samu ba. Sai kusan magriba aka sanar mana jirginmu yazo. A madadin Makka, sai akace ai dama Riyahd za'a kaimu. Haka aka ɗuramu a jirgi. Daga itofiya zuwa Riyahd Awa 2 da minti hamsin da huɗu ne ya kaimu. Aka sauke mu a filin jirgin. King khalid international airport. Tun daga sakkowarmu jikina ya mutu. Bani kaɗaiba duk tawagarmu jikinsu duk a mugun mace. Bayan mun je ɗakin ɗaukar jaka, daga nan aka nuna mana ƙofar fita, duk muka fito yu. Titine shimfiɗaɗɗe, sai tsirarin motoci masu shige da fice jefi, jefi. Ga wutacen lantarki masu haske kamar rana. Dan ko allurarkace ta faɗi zaka ganta kamar ba dare ba. Wata farar Hajiya ce ta nufomu tana murmushi, tasha gwala_gwalai haƙorin makka har guda shidda ne reras a bakinta. Da isowarta sai muka ji tayi Hausa raɗau. "Kune mutanen Hajiya Salamatu kano to jidda?" Kusan dukkanmu muka haɗa bakin wajen amsa mata da. "E mune Hajiya" Dariya tayi tace. "Masha Allah komai yayi kalas. Yalla ga mota bus ku shiga muje" mota muka shisshiga kowa ya zauna, iyakar galabaita dai munyi. Yinwa kuwa ba a maganarta. "Uwani nifa jikina ya mutu tunda akace Riyahd za a kawo mu. Domin ba haka mu ka yi da Hajiya Salamatu ba." Buɗar bakin Uwani tace. "Karma kiji komai Iyabo da Makka da Riyahd duk abu ɗaya ne. Kuma ƙila tana nufin a makka za a sama mana aikin wanke_wanken tunda mu ba zama mu ka zo yi ba." Sai data faɗi haka sai na ɗanji sanyi. Duk da dai zuchiyata a cike take da tsoro ainun. Tafiya kuwa tun anayin ta marmari, har abun yazo ya gunduremu, tun cikin dare muke sharara gudu bamu muka isa inda zamu je ba sai da asuba. A ƙofar wani babban gidan bene motarmu ta tsaya. Muka sassauko kowa a wahale, wasu tsofaffi daga cikinmu sai taimaka musu muka yi suka fito tsabar jigata duk sunyi fitsari a jiki. Hajiya Mangala ce ta fito daga cikin motar ta ta nufomu. "Yalla muje ciki, kun sha hanya, a yi wanka a karya sai kowacce ta kwanta ta huta kuma" A baya muka bita zuwa cikin gidannan. Ko wacce na faman tiri_tiri da kaya. Ni da Uwani ne kaɗai bamu da wasu wadatattun kaya, a jaka ɗaya ma muka haɗe kayan. A bene na shida muka tsaya. Mu dai duk inda Hajiya Mangala ta ɗaga ƙafarta anan muke sa tamu ƙafar. Wasu ɗakuna ne a jejjere reras a wani dogon falo, ko wacce ƙofa da number a jiki. Ɗaki na ashirin daga nan ta soma. "Mutum goma goma zaku shisshiga, daga wannan ɗakin zuwa har inda zai isheku. Amman wannan me lamba ashirin ɗin mutum biyu ake bukata. Ke da ke ku shiga nan tunda kune a tsaye a wajen." Ta nuna ni ni da Uwani muna tsaye riƙe gam da hannun juna. "Amman kafinnan ko wacce ta bani fasfo ɗinta da wayar salula in tana dashi. Ko wanne ɗaki akwai land line da zaku kira ƴan uwanku na Najeriya." Nan Uwani ta zaro wayarta ta miƙa, muka haɗe fasfo muka bata, na sanar mata bani da waya. Duk da haka sai da tasa wata mace ta caje kayanmu, ta caje jikinmu, hannunta har cikin wando, har ƙasan mama sai da ta ɗaga, da gashin kai. Tana gamawa damu muka shige wannan ɗaki da sallamarmu. Wallahi Allah sai da gabana ya yanke ya faɗi. Siririn gaske ne ɗakin, iyakar tsayin katifa, babu masaka tsinke. Ga mata nan su takwas a kwance ko wacce a karamar katifa irinta ƴan makaranta. Ragowar katifu biyun kuma jakunkuna ne akai a jibge. Daga bakin ƙofarnan da yake da ɗan sararin da muke tsaye, babu inda zamu ɗaga ƙafarmu mu ajjiyeta sai dai a katifar mutane. "Uwani na shiga uku, kinga wani ɗaki kamar kwanciyar kabari. Kafin uwani tayi magana aka buɗe ɗakin. Wannan matar data caje mu ce. "Dama nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Ke Ƴar ɗas, ƴar ɗas kina jina fa" Wacce aka kira da ƴar ɗas ta tashi zaune tana miƙa. Ni dai in ba gizo idanuna yake yi mini ba sai naga kamar namiji, akwai dai gashi a kanshi, amma ƙirjinshi babu komai a shafe, duk da akwai ƙunƙumar macce wacce bata da nono, kuma macece, inta haifu sai kan nono ya bulloƙo ta shayar da jaririn, to ina tunanin ko Ƴar Ɗas ƙunƙumace. "Oh ma'aikin Allah na Madina ni Ƴar Ɗas. Yanzu Taraliya duk illahirin jama'ar dake ɗakinnan saini kika ga damar tasa, sabida riƙaƙƙem iskanci? To gani gani" Magana take yi da lanƙwasa, gata da yanga" Wacce ta kira da Taraliya tace. "Baƙi mu ka samu, kisa waɗancan matan su kwashe kayansu a kafinsu, zasu kwanta su huta" Ƴar Ɗas tai mana kallon uku saura kwata tace. "Bayin Allah maraba da zuwa. Ke waccan tsalllako ga katifa can. Kiyi watsin ruwan tsarki da kayan da kika gani a katifar. Ke kuma ga bayan gidaa bayanki, faɗa ki shilla wanka, inba haka ba zafi ne zai kasheku" Dariya Taraliya ta saka tace. "Baki da dama yar Ɗas" Itama dariyar tayi tace. "To ai gani suke daɗi muke ji in mun baro gida Najeriya. Tunda sun shigo sai du a haɗu aci wuyar tare ai. Duk wacce ta kwace ta tafi Najeriya ta ba da labari" Take naji wani zum_zum. Tsoro ya kuma shigata. Ina tsaye Uwani ta shiga tsallake matan dake kwance. Aiko ta faɗi akan wata mace tim, ga uwani ba kaɗan ba. Matarnan ta saka ihu da kururuwa. "Haba baiwar Allah wannan ai iskanci ne, ji yanda kika faɗo mun so kike ki karyani?" Cike da fitsara take maganar gata yarinya ƙarama. Kiyi haƙuri baiwar Allah " Na faɗa ina daga tsaye. Ta bani amsa da cewa. "Babu komai. Sannunku da zuwa baƙi" Da ƙyar Uwani ta yinƙura da rarrafe ta isa waɗannan katifun biyu ta ajjiye jakar kayanmu ta zauna. Ƴar Ɗas ta dubeni tace. "Wannan tsaiwar ta babu gaira babu dalili dame yayi kama. Kin zo kin tsaya mun a ka, sai in tayar miki da aljanu Allah. " A tsorace na shige ƙofar dake kusa dani. Wani bayan gidane tsukukun gaske, komai dai tsab, ga ruwa a fanfo ga bokiti. Tuɓewa nayi na shesshiƙama jikina ruwan sanyi, dan a jiƙe kayana suke da sufa sharkab. Jiri da ciwon kai na yinwa duk yabi ya addabeni. Alwala na ɗauro na fito kayan dana cire su na mayar na saka hijabina na fito. Ƴar Ɗas tana zaune tana kallon ƙaramin mudubi na hannu. Uwani tsallako kije kiyo wankan" Uwani da tayi jigum tace. "Faɗuwa zanyi matsawar ban saka abinci a cikina ba. Bani da nutsuwar wanka, ki ƙyaleni kawai" Kai na girgiza dan nima yinwar shirin kayar dani take yi. Kafin ince wani Abun sai ga Taraliya ta buɗe ƙofa ta miƙo mun gurasa guda huɗu a hannu, da wani romon miya. Nasa hannu na karɓa ina jujjuya abincin. "Ku biyu ke da abokiyar tafiyarki. Ku yi da jiki maza, zaku fita yanzu da Hajiya Babba" Danƙarewa nayi a tsaye mamaki na neman ruguza nutsuwata. Da ƙyar naja ƙafata na tsalllaka na samu uwani. Loma shida gurasarnan tayi mun. Jima nayi kamar yinwar na sake tsokanowa wallahi gashi ko ruwa ba'a bamu ba. Sai Ƴar Ɗas muka roƙa ta bamu gora ɗaya ƙarama. Uwani daure ki je ki watso ruwa, ana binmu sallah fa, kuma kinga ance zamu fita." Uwani dai bata ce komai ba ta tsallake matan dake ta bacci hankali wance. Ƴar Ɗas dan Allah inane gabas, sannan a ina zanyi Sallah?" A yangance Ƴar Ɗas ta ce. "Ga gabas kin ganta. Batun inda zaki yi sallah kuma katifarki zaki jingine a bango kiyi sallah. In baki da dadduma sai ki shimfiɗa ɗankwalinki" Harna rama sallolin da ake bina hawaye bai dena zuba a idanuna ba, zuchiyata ta karaya ina hango mana wahala da wulaƙanci a gabanmu. Uwani itama katifar ta gingine ta soma rama sallolinta. Bata kai ga gamawa ba Taraliya ta leƙo kiranmu. Uwani bata idar da sallah ba Taraliya" "Tayi sauri ta sallame, dan Hajiya Babba ba'a ɓata mata lokaci. In ranta ya ɓaci baku ba cin abincin rana a cikin gidannan" Uwani tayi Sallama, ta dubi Taraliya tace. "Akwai sallar isha a kaina ban rama ba fa" Ƴar Ɗas tace. "Shawara ki tashi kuje, in kun dawo kya rama. Ba a yin musu da duk umarni. Ke wata