← Book details Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 60

Sashe 33

Nama Ya Dahu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gwadabe.
Ta ɓangaren Angwaye kuma tun da suka idar da sallar isha Malam yace su sameshi a turakarshi yanason tattauna muhimmin zance dasu. Hakan kuwa akayi, suna idarwa suka je suka samu Malam a turakarshi tare da matanshi duka. Ko wanne ya nemi waje ya zauna a gefen uwarshi, abokansu kuma suka wakiltasu dan siyo tsarabar amare.
"Toh Alhamdulillah an yi taro lafiya an watse lafiya, banda ƴan kunji_kunji na mata wanda ya zame musu al'ada. Ni abinda yasa na taraku a gaban iyayenku domin su zame mun shaida shine. A cikinku duk wanda ya nemi fitina ko tada tarzoma a cikin wannan gidan naku, haƙiƙatan zai fuskanci hukunci mai tsanani. Ya zame muku dole ku so junanku domin da hakanne matayenku zasu haɗe kawunansu ayi zaman lafiya. Matsawar matayenku suka fahimnci a tsakaninku ƙiyayya da rashin jituwane. To suma fa ba zasu taɓa haɗe kawunansu ba. In kuma basu haɗe kawunansu su ba, to haka zaku hayayyafa yaranku su taso babu jituwa a tsakaninsu, kamar yadda iyayenku su ka yi. Domin sune ummul aba'isin ɓata komai. So nake in gyara gidana dan gudun barin baya da ƙurar da in ta tashi ba a san adadin mutanan da zata tule musu idanu ba. Ku zaunar da matayenku ku fahimtar dasu mahimmancin ƴan uwansu. Ku umarcesu da zaunawa da kowa Lafiya. Tasi'u da Jamilu sun isheku a matsayin uwa da uba. Duk abinda ya taso ku sanar musu, zasu maganceshi sai in yafi ƙarfinsu sai mu ji a cikin gidan. Ina fatan kun fahimceni, kun gane inda nasa gaba ko?" Sabitu ne ya kalli Hannafi Wanshi, suka taɓe bakinsu carab a kan idanun Baba Fhatsima. Baba Asshi da Amaryar Malam da suka samu haɗewar kai a bikinnan suma suka wani ɓata fuskarsu. Itako Suwaiba sai kallon Malam take yi bakinta cike da abu faɗe.
"Fhatsima kece Babba da akwai abinda zaki ce ma yaran naki a gurguje?" BuÉ—ar bakin Suwaiba ta katse Malam ta hanyar cewa.
"Ai daka barsu Malam sun tafi abokansu suna jiransu, karfe kusan tara saura ai ya kamata su tafi ga iyalinsu. Duk abinda zamu ce ai mun riga mun faɗa musu tun ba yanzu ba. Ko ba gaskiya ba, Asshi, Amaryar Malam?" Ta tambayi su Baba Asshi da suka ji daɗin katse Malam da Suwaiba tayi. Su Gwadabe kuwa sai sunkiyar da kansu suka yi ƙasa dan yanda tayi maganar ba daidai bane ace tayi ma Malam a gaban yaranshi ba, domin Malam ya haifi waɗanda suka girme mata nesa ba kusa ba. Itako Amaryar Malam tace.
"Sosai kuwa Suwaiba. Ai duk wani huɗuba mun riga da mun yima yaranmu Malam. Itama Fhatsima tayi ma yaranta a ɗaki, sai nake ganin ba dole bane sai ta haɗesu duka an ƙara ɓata musu lokaci ba." Auwala da yake jin kamar dama ya kashe Amaryar Malam ya ɗago yana mata wani irin muzurai na ɓacin rai. Baba Fhatsima ce ta dubeshi ta tausheshi da idanunta, dan ta fahimci matan Malam ransu a ɓace yake da Malam ne akan ɗinkewarsu da tafiyarsu umara. Malam kamar ruwa ya cinyeshi haka yayi tsit. Ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige dan tsantsar kunyar da matanshi suka bashi a gaban yaran nashi. Da ƙyar da siɗin goshi ya yaƙi zuchiyarshi ya dubi Baba Fhatsima a karo na barkate.
"Me zaki ce Fhatsima ko kuwa kin basu izinin tafiyar kema?" Ganin ɓacin rai maɗaukaki a fuskarshi da muryarshi yasa tace.
"Abinda zan ɗaura muku akan abinda Malam ya faɗa daya ne. Kuyi ƙoƙarin ginin fondisho me kyau ga iyalinku dan gudun dana sanin data kasance ƙyayya maras amfani. Sannan ku sani hannu ɗaya baya ɗaukar jinka. Zanso ku kasance tsintsiya ɗaya. Banda tuna baya, gani ga wane akace ya ishi wane tsoron Allah. Ku je Allah yayi muku Albarka " Da Ameen su Gwadabe suka amsa, bacin su sauran yaran babu wanda yace uffan. Fuu suka fice, iyayen nasu suna a mugun fusace suka miƙe.

Malam:
"Ku dawo ku zauna ban sallameku ba" Malam ya faɗa da muryar da babu wanda yasan cewa shine mallakinta. Duk sai da suka tsorata da irin yanda Malam yake zurga_zurga a filin falon. Duk suna tsaye harda Baba Fhatsima wacce ta miƙe yanzu. Sarautar Allah suka zubama idanu. Malam baice komai ba, bashi da niyyar cewa uffan, sai kai mari da gwauro yake yi. Cikin ɗaga murya gami da tsawa_tsawa ya soma Magana.
"Ashe rainin da ku kai mun ya kai ku mun diban albarka a gaban ƴaƴana? Ashe rashin ɗaukata ba a bakin komai da kuke yi ba ya kai haka? Ashe ni bazan faɗa ku ji ba? Kaiconka Magaji da son ƙyale ƙyale yasa ka auroma diyoyinka iyaye maras tarbiyya. Allah na tuba ka yafe mun kura kuraina ya Allah. Suwaiba dake da Maman Inusa ( Amaryar malam) kuje gidan iyayenku har sai na nemeku" Kalmar data girgiza hanta da huhun matan Malam. Da sauri Baba Fhatsima tace."
"Kar kayi haka Malam. In hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemoshi. Me yasa zaka sallamesu alhalin gidan cike yake da jama'ar biki, ɗakunansu ma a cike yake da dangi na nesa. Kaima Allah ka yi haƙuri" Malam ya dubeta yace"
"Ki barsu su tafi Fhatsima. Bazan laminci rashin É—a a ga ko wacce mace a cikin gidannan ba. A tunaninsu damar da suka samu a baya zasu sameta yanzu ne? Ina ba wannan magajin da suka sani bane" Su Suwaiba dai jikin tatsaure yayi la'asar. Abun kunya ne ace yanda ta aurar da yara, yau a wayi gari wai malam ya korata gida. Itako Amaryar Malam kab danginta sun san itace tauraruwar gidan malam, yau sai ace a gabansu Malam yace ta tafi gida wannan abun kunya dame yayi kama?"
"Malam kaima Allah ka barsu su zauna a É—akinsu" Cewar Baba Fhatsima. Baba Asshi tama rasa ta cewa kallon Baba Fhatsima kawai take yi.
"Shikenan sun shiga rigar alfarmarki Fhatsima. Ku fuce ku bani waje. Ammanfa ku sani ana watsewa a gidannan. Kuma ku tattare yanaku_yanaku ku ficemun a gida, har sai zuwa lokacin dana ga dama nace ku dawo" Jikkunansu duk a mace suka fice ko tari an rasa wacce zata yi.
"Malam ka sassauta ma kanka dan Allah. Kayi haƙuri abi komai a sannu, in sha Allah gidanka zai gyaru ya zama kamar ko wanne gidan dake da tsayayyen uba. Ni dai a kullum ina sake jaddada maka ka zama mai magana ɗaya tak. Rarrabe magana itace ta soma kawo rabewar kai a gidanka, ka zauna kayi tunanin yanda zaka tanƙwara matanka. Korarsu bazai zama ya kawo gyara ba, sai sake rura wutar gaba da ƙiyayya." Da sauri ya katseta da cewa ."amman aya zata ji tsoro tunda taga an taune tsakuwa ma. Fhatsima abinda ya faru a baya kuskurene, a lokacin idanuna duk sun rufe bana ji baba gani, giyar ƙuruciya da lafiya na ruɗata. Dube ni a yanzu da ƙuruciya da ƙarfin nawa ya ƙare kuma na kasance cikin damuwa da hawan jinin da ni na saima kaina domin bazan ga laifin Asshi ko Suwaiba ba, sabida ni nace ina sonsu har suka amince mun. Kije ki kwanta babu damuwa, Nagode sosai Allah yai miki albarka. Ina mai daɗa baki haƙuri a bisa kuntata miki da nayi a baya, ruɗin sheɗanne" Ɗan murmushi tayi mishi tace.
"Da an taɓo maza sai kaji suna cewa ai ruɗin shaiɗanne, alhalin son zuchiya ke rufe muku idanunku, sai kun shiga matsala ku zama abun tausayi. Allah ya kyauta sai da safe" Ficewarta tayi ranta ya sosu ainun. Malam ya fama mata daɗaɗɗen mikin daya jima yana cin ƙasan zuchiyarta tsawon shekaru. Ta ga rayuwa ta shanye takaici kishiya da ɗa namiji samfur_samfur, sai da ta kasance fiye da mugiya dan baƙin jini a wajen kishiyoyi. Hawayenta taa share daidai isowarta bakin ƙofarta. Baba Asshi ta ja tsaki tace.
"Fhatsima dani kike zancan ni dake shege ka fasa. Asirinki akan iya Malam zai tsaya dama shi shanyayye ne. Amman ni Asshi naci dubu wallahi sai dai ceto" ÆŠan guntun murmushi Baba Fhatsima tayi. Ta tattako izuwa kusa daf da Baba Asshi.
"Asshi kenan. La haula maganin mai tsafi, nasha tabara na sha yasin. Ni Fhatsima a tarbiyyar da iyayena suka bani babu zuwa wajen boka. Da biyayya ake kwace miji, ba da boka ba. Na riga nayi tasiri a rayuwar Malam tasirin da babu wata mace data isa ta kamo rabin matsayina. Ai matar fari daban take, darajarta ta musamman ce" Tana kaiwa ƙarshe ta juya ta shige ɗaki ta bar Baba Asshi cike da tunani tare da zabarin zuwan wayewar gari, domin ungulu na son komawa gidanta na tsamiya, dan tana tunanin Baba Fhatsima zata rushe mata shirin da tai ta shiryashi sama da shekaru talatin.
Chapter 33 · 0% Book details