← Book details Mummunan Zato Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 24

Sashe 6

Mummunan Zato Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi
ar dariya cikin kissa sannan ta ce "Uncle
ina kenan,kana ganin in da zaka zo kullum zaka gundure ni ne?" Cikin mamakin ta ya ce, Beby sai ina ga tamkar ba ke ba, Beby da ba ki iya gaya min yanda ki ka damu da ni ba, da zaran abubuwa sun yi sau
i za ki ganni." Ta ce, to sai da safe, ya ce zan zo miki cikin mafarki kinji, ta ce sai na ganka.

Sai ta samu kanta da sumbatar wayar tare da saurin kashe wayar.

Sautin kiss
in ya daki dodon kunnanshi ya ratsa dukkan jikinshi.

Ha
a ta saukar mishi da kasala,yana jin ba za ya iya ci gaba da aikin gabanshi ba, dole ya rufe komai ya tashi.

Ita kuwa juyi ta yi tana jinjina ma
arin da tayi tasan in a gabanshi ne duk da Anty Maimuna tana bata
arfin gwiwar ta ringa mishi hakan ba zata iya ba.

Washegari wuraren
arfe shida lokacin ta fito daga lakca don ranar uku da mintuna suka shiga, ta bu
e gidanta ta shiga dama ta riga ta yi abincinta, magriba kawai zata yi sannan ta ci.

Zaman ta kenan sai ta ji ana
wasa mata gida ta je ta bu
e.

Wasu
ammata ta gani su uku, suka nuna mata wani gida kusa da nata,ga gidan mu nan munce ne bari mu shigo mu gaisa, cikin fara'a A'isha ta ce ku shigo ta matsa suka shiga.

Abinka da wayayyun
an boko,nan suka sake, ita dai taje tayo sallah ta basu abinci suka ci har suna santi, nan suka sanar da ita sunayensu.

Saliha da Amina,Kiristar kuma Linda
ar kaduna ce,su kuma biyun nan Sokoto suke,suma course
in da take yi shi suke yi.

Tana zaune dai ta ma kasa cin abincin don bata sake da su sosai ba,su ne dai sukayi tamkar dama sun santa, sai ta ji ana bugun gida, ta kalli agogo cikin zuciyarta ta ce to ko wanene kuma,
arfe ba
wai da rabi,ta fita tun kafin ta bu
e ta ji
amshinsa, cikin hanzari ta bu
e tare da cewa, Uncle tafiyar dare?

Jawo ta ya yi zuwa jikinshi ya rungume, tare da fa
in I miss You Beby, ta amshi Jakar hannunsa "zo mu je Uncle kai ka
ai ne?

Ya ce ni da Jabiru ne, sai da na kai shi masauki sannan nayo nan.

Anan nayi magriba da isha'i, suna shiga falon ya yi turus yana kallon
an matan da ke zaune, fuskarshi da alamun tambaya, ta ce ma
otana ne suka shigo don mu saba,ta dube su ga Uncle
ina, nan suka shiga gaishe shi kafin suka mi
e suka ce sai da safe A'isha Mustapha, ta ce na gode.

Ya zauna nan ta shiga rawar jikin kawo mishi wannan da wancan,shi kam duk in da tabi kallonta kawai yake yi yana sonta.

Yana cin abincin suna hira tana mishi mitar zuwan ba zatan da ya yi mata, gashi bata mishi wani abu na musamman ba, ya ce shi ai ita ce ta musamman
in shi, cikin
wanaki ukun da ya yi a Sokoto ya kuma yarda A'isha ce kurum ta dace da rayuwarsa.

Haka ya taho da kewar ta itama tana kewarshi, haka abubuwa suka yi ta faruwa lokaci ya dinga zuwa yana wucewa, Uncle yana ziyartar A'isha duk bayan mako
aya ko biyu.
watsam!

Wannan zuwa ya sameta ta tana fashin sallah, kuma ranar ta fara, da
yar ta lallasheshi ya yi
wana biyu tare da gamsar dashi ta hanyar wasu
an dubarun nata.

Wani sabon al'amari tun daga lokacin sati na hu
u kenan rabonshi da Sokoto, sannan wayar ma yanzun ba kamar da ba, kullum uzurin yake bata wai abubuwa sun mishi yawa gashi ana gyaran gida, daga baya ma in ba ita ce ta kira shi ba shi kam baya da lokaci.

Abin ya soma ba wa A'isha tsoro,nan gefe kuma ga wata matsala da ke damunta.

Motsi cikinta ke yi,ta sa rai ya zo ta sheda mishi, amma shiru suna daf da fara jarabawa abin ya matsa mata don haka ta kira Nafisa ta sheda mata,Anty Nafisa ta ce baki gaya ma Uncle
in ki ba?

A'isha bata son saurin tona cikinta nata ganin gaske ne uzuri ya yi wa Uncle yawa ne, shi yasa har yanzun bai zo ba,ba zata yi saurin kai
ararshi ba, ta ce abubuwa sun yi ma Uncle yawa bana son na gaya mishi zaya tada hankalinshi, ya ce zai bar aikin gabanshi ya taho.

Nafisa ta ja tsaki,wane abubuwa ne suka mishi yawa baya ga komai da ya tsaida, Ya shiga harkar yiwa Jummai gini.

Gabanta ya fa
i ta ce gini kuma?

Nafisa ta ce bai sanar da ke ba kenan?

A'isha ta ce, yace min dai yana gyaran gida.

Nafisa ta ce, to ai gyaran kenan, Jummai ya fafaramma gini irin ku
in da yake narkarwa a ginin sai kin gani yanzun ya gama kayan da za'a zuba ma daga (Chaina) za'ayo Odar su, A'isha ta ce to Allah yasa alheri." Nafisa ta ce,au!

Ke bakiji haushi ba?

Ta ce, to in naji ma Anty Nafisa ya ya zan yi?

Tsaki Nafisa ta kuma ja,ke tafi can ke dai son miji ya yi miki yawa,ba ki iya ganin laifin shi.

A'isha ta yi
ar dariyar takaici, sannan ta ce to in ma naga laifinshi me ganin laifin za ya maganta min?

Nafisa ta ce shi kenan mu dai mun ga laifin shi gidaje nawa gareshi cikin Katsina da kewayenta?

Ya maidata wani mana za'a tsaya
arnar dukiya,kin san Allah, Alhajinmu da Hajiyarmu sun ji haushi, harkokin shi ma fa ya
i ya maida hankali sai ka ce yau ya soma gini.

A'isha ta ce Allah ya
yauta kuyi ha
uri kada suyi fushi da shi,tamkar Nafisa ta shiga ta waya ta doddoke A'isha don haushi, ta kula A'isha ba zata ta
a ganin laifinshi ba, don haka sai ta canza zancan da cewa,ki je asibiti mana?

A'isha ta ce nima tunani na kenan, sai kuma naga ni ba ciwo cikin ke min ba, kuma ba wani guri ne ke min ciwo ba a jikina, sai naje na cewa Likita ina jin motsi?

Nafisa ta ce kin ji irin haukan naki ba?

Ki je ki yiwa Likita bayani,in yaso ayi miki (Scanning) a ga me ke damunki,in bai ga komai ba a koma Islamic." A'isha ta ce, shi kenan zan je, ki gaida min su Hajiyarmu."
Lamo ta
wanta tana tunanin me ya shiga kan Uncle ne?

Don kawai yana yiwa Jummai gini sai ya share ta?

Zata ce kada ya yiwa Jummai gini ne?

Ba tare da ta gansu ba?

Ha
a ranta fa ya
aci sai dai bata son ta nuna ma
ar uwarshi ne.

Ta kira wayarshi abin al'ajabi ya
auka, har sau uku, sai ta tura mishi da text cewa,in ta mishi laifi ne don Allah ya yafe mata, rashin sa ya saka ta cikin damuwa,don Allah yaushe zai zo?

Sa
on na isa sai kiranshi har tana murna ga zatonta sulhu zaya nema, sai kurum ya ce "ke kin fa matsa min da yawa......
######
[12/19, 22:33] Ummi Tandama
Page 5*
Ban cika son mace mai jarabar tsiya ba, duka-duka yaushe ne ban zo ba na shekara ne?

Kin dameni don Allah daina kirana in na matsu zan neme ki da kaina." Kan A'isha ya yi matu
aurewa,bakinta yana rawa ta ce, "Yi ha
uri Uncle nima ba wai na ce kazo ba ne,na zaci na maka laifi ne shi yasa." Tsaki ya ja kafin ya kashe wayar, wannan lamarin ya firgita A'isha sosai, baiwar Allah ranar sai dai bacci
arawo, amma bata runtsa ba.

Ma
otanta su kansu cikin
wanaki sun fuskanci tana da damuwa koda suka tambaye ta sai ta ce musu bata jin da
i ne.

Anty Maimuna ma ta matsa mata dason sanin damuwarta, amma A'isha sarkin zurfin ciki ta yi
ememe ta ce zuwan jarabawa ne.

Yanzun suna karatu ba dare ba rana,Anty Maimuna ta ce to Allah ya taimaka.

Cikin haka ne A'isha ta samu ziyartar asibiti inda ta samu ganin Likitan mata.

Bayan ta gama mishi bayani ya tambaye ta ko tana da ciki ne?

Ta shaida mishi ita kam bata da komai,don haka ya bukaci ta
wanta kan gadonsu na likitoci don yi mata (Scanning).

Bayan ya gama bai ce mata komai ba, sai da ya fitar da sakamako ya dube ta, "kina da miji?" A'isha ta ce "Eh." Ya mi
a mata sakamakon, tana bu
ewa idanunta na sauka kan (EDD) ta maimaita kalmar a fili (EDD) kuma?

Ta dubi Likitan ta ce,kana nufin ciki ne da Ni?

Ya ce wata ba
wai ta zaro idanu tare da
ora hannunta kan mararta, sannan ta ce Likita ka kuwa duba sosai?

Ya yi
an murmushi,a katin ki naga cewa ke
alibarmu ce amma kin kasa gane kina
auke da ciki,kina nufin ko ka
an ba wata alama da ki ka gane kina
auke da ciki?" A'isha ta girgiza kai tare da cewa, "Ina al'ada duk wata sannan wata bakwai
in da ka ke magana nayi
ari lokacin wata uku."
Ya zuba mata ido, "Ya ya abin ya faru wancan lokacin?

Ta bashi labarin a ta
aice, ya ce to wankin cikin da baayi miki ba shi ne dalilin da ba a wanke
an ba, Allah ya sa zaya taka doron
asa, sai dai zaya iya kasancewa watannin cikin ya koma baya.

Yanzun dai cikinki wata bakwai da sati
aya.

Jugum A'isha ta yi tana tunanin wannan lamarin na Ubangiji,lallai wannan shine mafi girman abinda ya fi bata mamaki,iyaka tsawon rayuwarta, sannan ta yi murna mara adadi kuma ta san wannan labarin in ta bawa Uncle shi zai kawo karshen rashin jituwarsu, ko ta ce fushin da yake yi da ita, wanda bata san silarshi ba.
Chapter 6 · 0% Book details