← Book details Mummunan Zato Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 24

Sashe 10

Mummunan Zato Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uncle ya yi zaraf ya ce, "Likita dama in mata suna da ciki suna fashin sallah ne?" Likitan ya zauna ya yi mishi dogon bayani tare da tabbatar mishi cewa akwai matan, kuma itama hakanne ya faru gareta, duk da yanda yake jin tsanarta cikin ranshi amma wani sashen na zuciyarshi na murna da wannan labari.
warai ya so ya tafi da ita gida, amma sai Alhajinmu ya ce ya kai ta gidanshi can gurin Hajiyarmu, duk da ba taga canjin komai daga gare shi ba,ta ji da
in yanda ya amince da cikin koda suka dawo har yanzun Hajiyarmu bata sakar mishi fuska ba, ya fito ya nufi gida.

Hajiya Jummai ta
osa ya shigo domin ta ji me yake faruwa, da kanta ta taka har gefen A'isha, amma bata nan lamari fa zaya jagule mata in bata yi Sa'a ba,ga Hadiza kuwa murna ce fal zuciyarta,tasan
arshen A'isha ne ya zo,wa ya sani ma ko tun jiyan ya dan
ara mata saki?

Inji Tabawa, Hadiza ta ce Allah yasa hakanne.

Lokacin da maigidan ya dawo bai ce komai ba, Jummai kuwa ta yi ta maza ta daure bata ce mishi komai ba har sai da ya yi wanda ya zauna cin abinci, ita kuma tana kusa da shi tana zuba kissa da salo,can ta ce waini Alhaji daga masallaci ina ka nufa?

Ya dubeta, gidan su Alhajinmu naje.

Suna lafiya?

Ya ce lafiyarsu lau, suna gaida ku." Ta yi shiru don tana son sanin ta ina zata fara batun A'isha?

Can sai ta kira Uche wanda yanzun ta
auke shi zuwa sasanta, ta ce shirya breakfast ka kai wa A'isha ko?

Uche ya ce to zaya tafi sai Alhaji Saddi
ya ce bata nan,da sauri ta sha mur sai ka ce gaske,bata nan ina ta je Alhaji kada dai ka ce min ka saki yarinyar nan?

Ya dubeta dama na ce miki zan saketa ne?

Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a'a, ya ce to
yamin wannan tambayar, kiyi harkar gabanki wannan ba matsalarki ba ce,ta karkata kai Allah ya baka ha
uri ni kaina bazan so ka rabu da ita ba,dama ganin yanda ranka ya
aci ne.

Ya mi
e tsaye ya nufi
akinshi ba tare da ya ce mata
ala ba.

Lamarin fa ya dagule wa Jummai lissafi,in maigidan ya yi kamar zaya juyu son rai sai kuma ya mur
e, tana fa so ta san shin ina aka
wana ne batun cikinnan?

Dole ta je gurin Malam yau saboda ya yi mata bayani filla-filla, Lallai kam zata ga boni in har su Hajiyarmu suka ji batun ciki.
akin A'isha yana daf da na Hajiyarmu,tuni tasa aka gyare shi A'isha tana ciki a
wance tunanin rayuwa kawai take yi, ashe akwai wani lokaci da zai zo Uncle
in ta ya juya mata baya?

Musamman irin wannan lokacin da ya kamata ace ya jata a jiki,ya so ta ya riritata, amma ba komai ta sani jarabta ce ta Ubangiji yana jaraba bayinsa ta kowace hanya, ta yarda itama yana jarabata ne don ya gwada imaninta, Uncle kuwa tana ta
ara ba shi uzuri ba ta so ta tsane shi.

Yau
wananta uku a gidan tana cin gya
a dafaffiya da ta ce tana so Hajiyarmu tasa aka dafa mata, Nafisa ta shigo da sallama tare da
ar tsokana tana cewa mai ciki Uhum ga ni nan tafe, A'isha ta yi murmushi ta ce Anty Nafisa ce yanzun?

Ta zauna tare da
iban gyadar tana cewa tun
azun na zo ina gurin Hajiyarmu ne, A'isha ta ce ina yini?

Suka gaisa ta ce Yaya Bebynmu?

A'isha ta yi
an murmushi ta juya zancan da cewa yau fa sauran sati
aya mu koma makaranta, Nafisa ta ce har an gama yajin aikin?

A'isha ta dubeta da sauri ba yajin aiki mukayi ba.

Nafisa ta ce to tabbas ni naji da kunnena makarantarku suna barazanar tafiya yajin aiki,in har ba a biya musu bu
atunsu ba.

A'isha ta ja tsaki, Allah yasa kada a tafi.

Nafisa ta ce amin, Brother ya zo kuwa?

A'isha ta yi guntun murmushi, ina ganin abubuwa sun mishi yawa ne shi yasa, Nafisa ta kalleta cike da tausayawa,ke dai A'isha ba
ya son laifinsa ne, amma in yana gari kullum sai ya zo gidan nan, yanzun dan kina nan ne shi yasa ya daina zuwa.

A'isha ta ce to ni me zan ce?

Nafisa ta ce, Allah duk da ke ma shiyasa yake miki wannan abin,ni duk son da nake maka wallahi in ka taka ni zan nuna maka kuskuran yin hakan.

A'isha ta ce to Anty Nafisa kin san ko na mishi wani laifi ne?

Ai da baya min haka, sai in ga tamkar nayi butulci in har na manta irin rainon da Uncle ya yi min a baya.

Nafisa har da tagumi tana kallonta, kafin ta ce A'isha ke kam ban ma san irin ki ba,ko son shi ne ya yi miki yawa?

Oho, A'isha ta yi guntun murmushi, sannan ta ce ke ba ki son Uncle Bello?

Nafisa ta ce so kai amma fa bashi zai hana in ya min wula
anci in kasa ramawa ba.

A'isha ta tsura ma
asa idanu,son kawai take ta tuno ta ya ya zata iya yin sa'insa da Uncle
inta?

Ko rama wula
ancin da ya yi mata?

Nata ganin yana mata hukunci ne sakamakon wani laifi da tayi mishi, damuwarta
aya shine ya sanar da ita wannan laifin ko zancan ciki ta mishi uzurin rashin sani ta kalli Nafisa tare da girgiza kai ni kam Uncle yana da wata irin
ima a idona,ba zan iya
ata mishi rai matsawar ina sane ba, kuma ko yanzun nasan duk yanda aka yi ina da laifin da nayi mishi mai girma,tsaki Nafisa ta ja sannan ta fita daga
akin,yarinyar ba zata gane cewa maza ba'a musu haka ba.

Daren ranar Alhaji Saddi
ya zo da daddare falo ya samu iyayan nashi cikin girmamawa ya zauna ya gaida su, Alhajinmu ya fi sakar mishi fuska,shima
in ba kamar yanda ya saba ba, ita ko Hajiyarmu da
yar ta amsa kalma
aya daga cikin jerin gaisuwar da ya jero mata,nan ya shiga kame-kamen cewa ya yi tafiya ne shine dalilin rashin zuwanshi, sannan in ya nemi Alhajinmu a waya bata shiga,sai Alhajinmu ya canza maganar da cewa
azun kaga ba
i a Office
inka?

Ya ce ,eh sun zo mun kammala da su, zuwa satin sama zamu tura musu da ku
i in mun ga kayan nasu.

Alhajinmu ya ce, shikenan,ya yi
an jim sannan ya ce, A'isha na ciki?

Hajiyarmu yi tayi tamkar bata ji shi ba,isowar Uwani kenan ta dire mishi ruwa ta ce eh tana ciki,ya mi
e ya shiga, daidai lokacin da A'ishan ke kan sallaya hannuwanta a sama idanunta suna zubda hawaye,tana cewa ya Allah kai ne mahaliccina da kai na dogara, kai ne ka
ai zaka sama min mafita cikin lamarin nan nawa da mijina.

Ya Allah daidaitamu cikin gaggawa, Allah ka shafe wannan matsalar tamu,nan ta shiga kiran Ubangiji cikin sunayen shi ke
atattu,yana tsaye yana kallonta har ta shafa sam bata san da mutum ba, ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya shiga cikin
akin,ta bishi da kallo har ya zauna ta mi
e ta nufi
ofa,ya danne wani abu da ke taso mishi ya ce ina zaki?

Ta ce zan kawo maka ruwa ne, ya girgiza kai yanzun nasha a falon su Hajiyarmu, ta dawo ta zauna kan sallaya sannan ta ce ina yini?

Ya amsa cikin cijewa domin lokacin wani irin haushinta zai ce ko tsana ma?

Bai san ya ya zai kira abin ba, duk da
arin dannewar da yake yi fuskarshi ta canza, ya daure ya ce ya ya jikin?

Ta ce Alhamdulillah, ta sake duban fuskarshi gabanta ya fa
i saboda ganin irin yanda ya
aure, duk da haka ta daure ta ce, "Don Allah Uncle kayi ha
uri,bisa ga laifin da nayi maka,koda dai ban san laifin ba,ya mi
e tare da juya mata baya,ba abinda ya kawo ni yanzun ba kenan nazo ne na duba ki sannan ki min lissafin abinda ki ke bu
ata ke da Bebyn."
Ta tsura ma bayanshi idanu bata gajiya da yaba mishi cikin kowace Irin shiga, muryarta a sar
e ta ce sai dai ka tambayi su Anty Nafisa, ya juyo duk abinda suka za
a miki ya yi?

Ta ce eh, sai dai batun komawata makaranta, ya kuma dubanta yaushe ki ka dawo?

Ta ce, Uncle mu ba ayi mana hutu, ya juya baya domin in yana kallonta sai yaji ranshi ya fi
aci,ya ce makarantar ku sun tafi yajin aiki,ko dama ba a tafi ba bazan bari ki haihu can ba." Ya nufi waje ni na wuce hope ba wata matsala?

Ta ce babu,ka sauka lafiya, har ya kai bakin
ofa ta ce, "Na manta Uncle." Ya tsaya ba tare da ya juyo ba, ta ce wayata da kayana.

To, kurum ya ce ya wuce, don ya
osa ya bar
akin, haka kurum yake jin tamkar ya make ta,yana barin
akin sai ya ji shi sakayau, ga mamakinshi da ya fito sai yaga mahaifan nashi sun canza mishi, da alama shigarshi gurin A'isha ya yi musu da
i,nan ya nufi gidanshi.

Haka A'isha ta ci gaba da zama gidan surukanta gata na duniya tana ganin shi matsalarta
aya ce, Uncle
in ta wanda har yanzun yake nuna mata tsana da tsangwamma.
Chapter 10 · 0% Book details