← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 26

Sashe 8

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Muhaseen ya soma buɗe idanuwansa da suka yi masa nauyi, hasken da ya shiga idon nashi ne ya tilasta ma shi sake rufesu, sannan ya sake buɗewa a hankali komi ya soma washewa, baya jin ciwon komi hatta zafin jikinshi duk babu, sai de yanajin jikinshi yayi ma shi nauyi sosai, idonshi bai sauka ako ina ba sai akan Saleem da ke zaune a ƙasa gabanshi barbaje da takardu ga kuma loptop har biyu yana aiki, gaba ɗayanshi a hargitse ya ke aiki kawai ya saka a gaba, wani irin kallo Muhaseen yake bin Saleem ɗin da shi, kallo me cike da ƙauna wacce haɗuwar jini ta asassa, a hankali ya yunƙura tare da tashi zaune, ya fizge ƙarin ruwan da kuma jinin, ya zura tausasan takalman da aka aje a ƙasan wajen, sai da yai dagaske sannan ya iya tashi tsaye, baice komi ba ya juya ya soma tafiya sannu a hankali ya buɗe ƙofar ya fice, direct toilet ya shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala ya gabatar da sallah azahar ya zauna yana tazbihi, a rikice Saleem ya buɗe ƙofar ɗakin da yake ganinshi a zaune ya saka shi sakin nannauyar ajiyar zuciya gami da dafe goshinsa, idasa shigowa ya yi jikinshi a mace da tsantsar kulawa a muryarsa ya ce.
"Sarki ka bani tsoro wallahi, na duba banganka ba alhalin nasan kana kwance, taya har ka tashi ban saniba?."
Ya yi tambayar duda yasan cewar ba amsa shi zai yi ba, dan magana na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da keyiwa Muhaseen wahala sosai, bai gajiyaba ya kuma faɗin.
"Yanzu ya kake jin jikin naka, ko a sake kiran Doctor ya zo ya sake dubaka?."
Lumshe idanu kawai ya yi, yanajin yanda maganar Saleem ke ƙara mashi nauyi a kah.

Saleem dayasan ba amsa zai samu ba sai kawai ya haƙura yacigaba da zama yana yiwa Muhaseen kallo me cike da tausayi, sun kwashi tsayin mintuna a wajen, kafin Saleem ya tashi ya wuce.

Muhaseen duda baya jin ƙarfin jikinshi haka ya hau shiri cikin suit kalar kofi masu duhuwa, sosai kayan suka amshi jikinshi suka zauna ɗas gwanin burgewa, ramar da yayi ta sake fito da zallar kwayun shi, wayoyinsa ya ɗauka tare da danna kiran number Saleem yana fitowa, a main falo suka ci karo da juna shi da Saleem ɗin dake ƙoƙarin zuwa ganin kiran Muhaseen ɗin, wani kallo me cike da tuhuma da zallar Mamaki Saleem ɗin ke jifar Muhaseen daya sake tsuke fuska alamar ba warfi.
"Follow me🚶🏻‍♂."
Ya faɗa a gajarce tare da soma turawa drivera message akan su shirya za'a fita yanzu, kafin su fita haraba tuni an jere lafiyayyun motoci su kaɗai ake jira su isa, suna zuwa babu jimawa aka bubbuɗe musu cike da girmamawa, yayinda Muhaseen ya kame a gidan baya shi kuma Saleem yana a gaba kusa da driver kasancewar mota ɗaya suke hawa, kuma idan Muhaseen ɗin na buƙatar wani abu shi yake sabarmawa ta hanyar message.
Yauma a STAR GOLD Company suka fara isa, saɓanin Muhaseen yau Saleem ne ya binciki komi, sosai yasha mamaki ganin yanda al'amurra suka wakana kafin zuwansu, rasa ta inda zai fara yayi, domi daga safiya zuwa lokacin ansamu asarar kaya masu ɗinbun yawa, musamman ɗanyen gold, kuma sunyi missing ɗin babban business a ranar,sai a lokaci ya gane abin da yake saka Muhaseen zagewa wajen saka ido akan komi, wato harkarce dole sai tsayayye kuma jajirtacce me juriya, daga ƙarshe dai dole ya haƙura da wasu abubuwan ya turawa Muhaseen bayanai ta email yasan ida ya sami kanshi zai bibiya kuma yanada tabbacin sai ya gano daga inda matsalar ta ke........

MARYAM STAR⭐⭐⭐WRITER.......✍🏻
Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 7

Ƙur Muhaseen ya ƙure allon computer gabanshi, yana lissafa adadin kuɗaɗen da idonshi yaga fitarsu daga asusun company yayinda ya shiga cuɗa yatsun hannuwansa cikin juna, yanajin yanda nauyin kansa ke ƙaruwa, Fawas shine sunanda ya shiga zagaye a kwanyarshi yayinda a zahiri ya shiga sarrafa computer yana ganin yanda aka goge du wa ta kafa da za'a iya samun bayanai akan fitar kuɗin, dama yasan hakan zata faru yasan hakan zai kasance a rana ɗaya da bai samu zuwa office ba, sai de bai yi tunanin komi zai tafi haka cikin sauri ba duba da yinin ranar be kai da ƙarewa, lumshe idanuwansa ya yi tare da soma juyi akan kujerar office ɗin yana jin ɓaci rai na baibayeshi, cire glashin daya suturta sauyin launin idanuwansa ya yi, sannan ya shiga yin typing ya tura gajere saƙo zuwa ga ofishin Finance manager wato Fawas, cikin abin da bai wuce mintuna biyar ba Fawas ya bayyana a gaban Muhaseen, a zahiri babu wa ta alama dake nuni da tashin hankalin da yake ciki, amma kuma abaɗini gaba ɗaya ya gama tsurewa dan yasan waye Muhaseen da kuma abin da zai iya yi.
"Sir gani na zo."
Ya faɗa ganin ko ɗago kai Muhaseen bai yi ba bare kuma ya kalleshi, gaba ɗaya ya juya baya yana juyi akan kujera, sun kwashi mintuna ahakan Muhaseen bai ce komi ba, yayinda tsoro da fargaba suka ci gaba da sakaɗar Fawas ta ciki, a zahiri kuma sai ƙara tsumewa ya ke.

Sai da Fawas yaja da baya a tsorace lokacin da Muhaseen ya juyo tare da watsa ma shi jajayen idanuwansa, bai kuma jinkirta ba ya ɗora da faɗin.
"A yau cikin ƴan mintuna ƙalilan kuma a yanzu ina so adawo da kuɗaɗen da ɗanyen gold ɗin da suka ɓata, idan ba haka ba ka gaggauta wajen kai kanka ga hukuma sannan ka biya ka amshi takardar sallamarka dan banada buƙatarka."
Daga haka kuma yaja bakinshi ya tsuƙe gami da sake lumshe ido yana sauraren bugun zuciyarshi.
A saɓule Fawas ya fice dan baiga wargin da zai tsaya musu ko roƙo ba, yasan aiwatar da abin da aka umarceshi wajibi ne, idan ko ba haka ba to kuwa yasan abin da zai biyo baya ba mai yuyuwa ba.

"Shut up Fawas, bakada amfanin komi har yau banga abin da ka cinana ba tun fara aikinan naka tayaya zaka zo da wannan banzan batu, ina nan ina farin ciki ka fara aiki yanda ya dace amma kuma shine zaka zo min da wani zancen banza ba za'a dawo da kayan ba nace ba za'a dawo da su ba, ya daɗe bai yi ma ka du abin da yaga dama ba."
Cewar Alhaji Bello daya bayyana agaban screen ɗin loptop cikin hargagi.

Kuka me ƙarfi Fawas ya fashe da shi cikin magiya da roƙo ya soma faɗin.
"Na shiga uku Daddy wallahi zan iya rasa raina akan wannan al'amarin dan girman Allah ka rufamin asiri ka dawo da kayan banyi tunanin zai zo aiki a yau ba sai bayan da na aiwatar da komi sai kawai gashi ya zo yanzu haka ya bani lokaci akan nemo inda kayan da kuɗin suke duda bai nuna min yasani na aikata ba amma nasan gab yake da yin komai akan dukiyarsa."
"Kai dallah shashasha ka rufe min baki, wallahi sam baka da wani amfani banga amfaninda turaka aikin nan yai ba saima ƙara damalmala komi da kake yi, tayaya ƙananun ma'aikata masu ƙaramin muƙami zasu fika iya aiki, kullum sai sun bada result me kyau, amma kai, kai Fawas banga wani amfani da kake yi a wannan aikin ba."
Yana gama faɗin hakan ya datse kiran ranshi a mugun ɓace, yayinda Fawas yabi bayan kiran hankali a tashe dan yasan babu kamawa sai ya kwashi kashinshi a hannu.

"Sarki a kwai damuwa a wannan company ɗin, abubuwa da dama sun cakuɗe, na rasa ta inda zan fara ko in haɗa meeting muji daga inda matsalar ta fara?."
Ya yi maganar yana goge gumin da ya taru a goshinsa.
Kai kawai Muhaseen ya jinjinawa Saleem, cikin ƴan mintuna aka sanar da taron meeting gaba ɗaya ma'aikatan STAR GOLD kowa da irin abin da ya zo a kanshi lokacin da aka sanar da taron, yayinda hankulan marasa gaskiya ya tashi sosai da sosai, masu gaskiya kuma hankulansu a kwance, cikin ƙasa da mintuna ashirin kowa ya hallara a makeken holl ɗin da ake meeting, sai da komi ya kintsu sannan Muhaseen ya fito cikin takunsa na ƙasaita me jijjiga zukatan munafukai, tsayuwarsa ma irinta zaratan jarumai ya yi duda babu ƙarfin a jikinsa, idanuwansa a daɗe cikin glass ya ɗaga musu hannu alamar amsa gaisuwar da suka miƙa ma shi a jimlance, a taƙaice ya ce.
" Du wanda yasan ansamu matsala a wajen aikinsa ko wani abu na company ya ɓata yai gaugawar soma bincike daga a gano masu yiwa company zagon ƙasa idan ba haka ba akwai hukunci tsattsaura tare da kora, na baku daga nan zuwa anjima kafin a tashi, zaku iya tuntuɓar Fawas idan ansamu bayanai ko wani abu, fatan alkairi."
Yana gama faɗin hakan ya soma takawa cike da ƙasaita ya fice daga wajen gaba ɗaya.
Mutuwar zaune Fawas ya yi a wajen, gaba ɗaya ya rasa abin yi hankalinshi idan ya yi dubu ya gama tashi, sai ɓarka zufa ya ke daga zaune.

Bin bayan Muhaseen Saleem ya yi suka fice, a ranshi yana jinjinawa ƙoƙarin da Muhaseen ke yi wajen warware matsaloli cikin sauƙi, basu sake jimawa ba suka wuce gidan, a canma sosai Saleem yai aiki gaba ɗayanshi a gajiye ya ke amma bai son tsayawa dan yasan muddin ya tsaya Muhaseen ɗin zai ce zaiyi......✍🏻

DAN ALLAH ƳAN UWA A DINGA TAYANI SHARE NGD SOSAI🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Ayi haƙuri page ɗin babu yawa, saboda nayi busy wallahi.

MARYAM STAR⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪

Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀
Chapter 8 · 0% Book details