← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Saukar ruwa masu sanyin gaske da taji a jikinta ya tilasta mata tashi a hargitse tana kwalla ihu kamar zautata sai ta ɗibi hanya ido a rufe zata arta bayan ta diro daga kan gadon amma sai ta ji an riƙeta gam.
"Wayyo Allah Sarki zoka ceceni ankawo min farmaki, wayyo karka tafi ka barni dan Allahhhhh...."
Ta faɗi tana watsal-watsal da hannuwanta tana son kwacewa, zazzafan marin da aka sauke mata ne ya tsaida ita cak, sannu a hankula ta soma buɗe idanuwanta, dishi-dishi take ganin mutanen ɗakin, sai da ta kwashi sakanni kafin ganinta ya saitu, sai faman haki ta ke ga jikinta sai ɗigar ruwa ya ke kamar wacce aka tsamo daga kogi.
Ɗaya bayan ɗaya ta dinga bin ƴan ɗakin da kallo ƙirjinta na hawa da sauka da sauri, yayinda idanuwanta suka fallasa asirin zuciyarta tsoro ɓaro-ɓaro ya bayyana a cikin su, sai kawai ta rintse su da ƙarfi wani abu me kama da zafi na dukan zuciyarta, muryarta da alamun kuka ta soma furta.
"Mafarki, yauma a mafarki na ganshi mi yasa?."

Ta yi tambayar tana tuhumar kanta yayinda ta fizge hannayenta da ƙarfi ta fice daga ɗaki tana fashewa da kuka me sauti.
Ƙur matar da ke zaune ta miƙe ƙafafuwa ta kafe ta da ido tana kallon yanda jikinta ke amsawa da kukan da ta ke yi, kamar ba zata tanka ba sai kuma ta kalleta tare da janyo hannayenta ta rungumota jikinta, tana jin tausayin yarinyar na ratsata bayanta ta soma bubbugawa a hankali, yayinda hayaniyar da mutanen gidan ke yi kamar kasuwa ya hanata yin magana, saboda batada murya me sauti.

Ta ɗauki lokaci me tsayi tana kukan badan wani abu sai dan yauma abin da ta gani ba zahiri bane, sau dubu zata kwanta sai tayi wannan mafarkin da jikinta ke sanar da ita gaskene, amma kuma tashin ta da mutanen gidan ke yi a kullum na sakata baƙin ciki, a ganinta da ace sun barta basu tasheta ba da wataƙila mafarkinta ya zama gaske, amma sau dubu zata kwanta sau dubu zasu tasheta.

"Innalillahi! Mamman kaga yanda ta kumbura maka haɓa, lallai kaji dukan manya."
Wata mata ta faɗi tana riƙe haɓa cike da jimami, yunƙurawa wanda aka kira da Mamman ya yi ya tashi tsaye, hannunsa akan haɓarshi da ke luguden azaba, kanshi tsaye ya yi hanyar ficewa daga ɗaki yabar sauran matan na shewa, wasu na masa dariya wasu na jajanta masa, waɗanda ke dariyar basu tsagaita ba sai da suka daina ganin wulginsa, sannan mutanen suka soma firfitowa kowa da abin da yake faɗi.
"Oh Najla shikenan tashin ki a barci ya zama annoba ko ince bala'i, yo annoba ka bala'i manah ayi mutum ƙarfi uwa doki, aiko wallahi kinji kunya ko aure kika yi ba lallai kibar wannan ɗabi'ar ba."

Sake fashewa da kuka wacce aka kira da Najla ta yi, bata kuma tsagaita ba sai da ta yi iya yinta, hawaye face-face a kan farar fuskarta manyan idanuwanta suka ture zuwa launin jah amma ba sosai ba, tsabar dagaske take kukan harda majina akan fuskarta, haka mutanen gidan suka dinga faɗar albarkacin bakunansu akanta, babu me faɗar alkairi sai faman kira mata bala'i suke.

Cikin sanyi matar ta sake janyota tare da soma goge mata hawayen idonta tana faɗi a tausashe.

"Haba Gimbiya taya za ki dinga asarar hawayenki masu tsada, hakan ai ba girmanki bane kiyi shiru ki daina kuka, suma basu fahimce ki bane shiyasa suke hantarar ki amma ni nasan ba hakanan kike doke-doke idan kina barci ba, kiyi haƙuri kinji ƴata wata rana sai labari Allah dai ya cika maki burinki."
Babu kunya Najla ta amsa da "Amin". kuma bata daina kukanba.

"Yauwa Sarauniya yanzu miƙe ki je kiyo alwala kiyi sallah kinga gari ya soma haske."
Matar ta faɗa tare da ƙoƙarin tada ita tsaye, har bagan babban baho na ruwa ta kaita sai da ta cika mata babbar buta sannan ta aje mata ta juya ta koma wajen zamanta murmushi shimfiɗe akan farar fuskarta, yayinda wani abu ke motsi a zuciyarta, wani abu wanda daidai da rana ɗaya bai taɓa barinta ta sararaba, ita ɗin me raunice amma bata bayyanar da rauninta ba saboda batason gundurar mutanen da ke baibaye da ita cikin aminci da girmamawa, a kullum rana tana saka rai da abin da batada yaƙinin faruwarsa sai de kallon fuskar Najla kawai na sanyaya ranta gami da bata ƙwarin gwuiwa, sannan jikinta na bata samun sauyin al'amurra daga ɓangarenta, iya mafarkanda tun wanzuwarta a gidan Najla ta soma yi na ɗisa ayar tambaya a zuciyarya, sannan tanada fata akan mafarki duda ba lallai fatanta ya tabbata ba amma tanaji a jikinta akwai wani abu me girma wanda take da alaƙa da shi da mafarkin da Najlar ke yawan yi.
Tazbihi taci gaba da yi a fili fuskarta ɗauke da mirmushi tana fatan tayi wani abu da zai zama na alkairi tsakaninta da al'umar gidan.

Siririyar tattausar muryarta ce ta katseta daka tunanin data nitsa a ciki.
"Umma matsa min kusa da ke zanyi sallar."
Najla ta faɗa da sunanda ta laƙaba mata shi tun zuwanta gidan, sunanda ke sake haddasa danƙararriyar ƙaunar Najlar a zuciyarta, sassanyar murmushi ta sakar mata sannan ta janye ƙafafuwanta ta matsa sosai daidai wajen da ta tabbatar zai ishi Najlar yin sallar.
Itama Najlar Murmushi ta sakarwa Ummar sannan ta tayarda sallah cike da nutsuwa, harta gama idanuwan Ummar na kanta tana kallon yanda take nutsuwa sosai a wajen ibada duda tana da rawar kai sosai amma idan tana aikin ibada zaka sameta da nutsuwa.

Bayan ta gama azkar ta yi addu'o'i masu tsayi sannan ta shafa, sai ta cire hijabin jikinta tare da watsa kyawawan idanuwanta akan Ummar, da siririyar muryarta me taushi ta ce.
"Ummana ni kaɗai ina kwana fatan kin tashi garau, yau a gidannan ke kaɗai zan gaisar."
Ta yi maganar tawa watsa ma wata matashiya za zata girme mata a shekaru wani kallo me kamar harara.
"Lafiya ƙalau Sarauniyar Ummanta fatan Gimbiyar Sarki ta tashi cikin ƙoshin lafiya?."
Kyakyawan murmushi wanda ya bayyanar da kyawawan jerarun ƙananan haƙoranta ta saki, sannan ta tanƙwashe ƙafarta tare da faɗin.
"Gaskiya Umma kina kashe ni da ƙauna wallahi, in sha Allah idan na auri Sarki ke zaki zama Fulani a fada, wato muƙami na daban zan saka a baki hatta wanka ba zan bari kiyi da kanki ba sai de asamu me yi maki, su Uwale ko sune ƴan shara da wanke-wanke."
Ta ƙarashe faɗar maganar tana kafe Matar da ta fito daga wani ɗaki hannunta na riƙe da babbar roba.

"Kan uba, dan ubanki ni ce zan zama ƴar wanke-wanken wallahi ƙarya kike yarinya shairin mafarke-magarken da kika saba yi me kama da bugun iska ne ke gaya maki ƙarya, yo Allah na tuba kama da iska mana abu yaƙi ci ya ƙi cinyewa kullum jiya i yau, inaji kwanyarki ta soma taɓuwa gaskiya bari Mamman ya wartsakw daga jinyar haɓarshi da kika nakasta ya je ya taho da Malam na lungu naga ya kamata ayi maki ruƙiya."
Uwale ta faɗa tare da wucewa abinta tana kaɗa musu mazaunar.
Still Fuskar Umma da murmushi ta ke kallonsu, idan da sabo yaci ace ta saba da halayyar mutanen gidan da kullum cikin drama suke, baga manyan ba baga ƙananan ba......✍🏻

Dan Allah Masoya a tayani da share🙏🏻🙏🏻

A daidai nan zan ɗisa aya . ku kasance tare da ni taku har kullum me son ganin farin cikinku.

MARYAM STAR⭐⭐ YAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪✍🏻

https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 10
"Wallahi Allah Uwale da gaske nike bada wasa ba sai na saka ki wake-wanke kona rana ɗaya ne idan na auri Sarki."
Uwale da ta shige madafa tana fama da hayaƙi bata ce komi ba ta cigaba da aikinta.

"Haba Gimbiyar Sarki mi ya yi zafi har haka Uwalece fa matar Kawunki."
Tunzura ɗan mitsitsin bakinta ta yi gaba sannan ta ce.
Chapter 11 · 0% Book details