← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 26

Sashe 6

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MARYAM STAR⭐ƳAR BAIWAR 💪JAJIRTATTU WRITERS✍🏻
https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀
بسم الله الرحمن الرحيم.

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 5

Suhail jin saukar maganganun Binta ya yi kamar saukar ma shi, sai yaji a ranshi yau kaɗai, yau kaɗai yana so ya tanka, amma yanajin tsoron abin da zai biyo bayan hakan, sai de kuma bazai iya yin shiru ba, anzo matakin da sam bazai iya jura ba, a hankali ya buɗe bakinsa murya a tausashe cike da rauni ya ce.

"Umma! shin ko nayi ma ki wani gagarumin laifi ne lokacin da ina yaro, Umma ina jin zafin, inajin zafin maganganunki kamar ƙunar wuta, Umma mi yasa, dan kawai kin raine ni?."
Sai harshen shi ya sarƙe, zafaffan hawaye suka ɓalle ma shi zuciyarshi ta soma ƙuntatuwa.

"Suhail, tun yanzu har lokacin ya zo, ni zaka tsaya kana gayawa waɗannan maganganun, to kaje Allah ya isa ban yafe maka ba, da ikon Allah sai ka haɗu da jarabawar rayuwa dama ance tsintacciyar mage bata mage."
Gwuiwoyin Suhail ne sukai sanyi ƙalau, har ƙafafuwansa suka kasa ɗaukarshi cikin kyaurmar jiki ya soma faɗin.
"Dan Allah Umma dan Allah kiyi haƙuri, ki janye kalamanki a kaina tabbas na yi kuskure amma bazan kumaba, kaf duniyarnan bayan Allah bani da kowa sai ku."
Wani wulaƙantacen kallo Binta ta jefa ma shi, sannan ta tashi a mugun fusace ta shige ɗaki, amma a ƙasa ranta murnace fal, sannan tayi ƙudurin dole Sulai yai aiki a wajen Alhaji Bello.
Wajen neman duniya ido rufe tana ƙoƙarin jefa kanta a gagarumar matsala wacce ba zata iya fitar da kanta ba, ba tare da ta saniba tana ƙoƙarin yiwa rayuwarta babbar illa da nan gaba zatai kukan kaico da danasani marar amfani.

A saɓule Suhail ya tashi tare da share hawayen idonshi, bai kula Hamza da ya shigo gidan babu sallama ba ya wuce yabar gida.
Wajen siyar da abinci ya nufa, gadai yunwa yana ji kuma ga abinci ya siya amma ya gagara ci, ƙunci da damuwa sunyi mashi yawa, yanajin yanda zafin zuciyarshi ke fitowa ta bakinsa ta hanyar suraci, ganin abincin ba zai ciwu ba ya sanyashi tashi yabar wajen, ya miƙi hanya ya soma tafiya ba tare da shi kanshi yasan inda yake jefa ƙafarshi ba saboda damuwa data dabaibaye shi.

Jauhar
Sosai tai kuka awajen tana sake danƙar ƙasar wajen a cikin hanayenta, gaba ɗaya farar fuskarta ta yi jazur, idanuwansa sun sake rinewa, jikinta sai kyarma ya ke, cikin muryar kuka ta soma faɗi bayan ta kwanta aƙasa.
"Yah Allah ya ɗauki raina ko zan huta da wannan baƙar rayuwar, yah Allah na roƙeƙa ka kusanto da ajalina anan kurkusa, na gaji da rayuwar na gaji na gaji."
Sosai tasha kuka a wajen har numfashinta na shiɗewa, ta jima sosai a wajen babu koda giccin mutane.

Bai ankara da yayi nisan kiwo ba sai da ya tsinci kanshi a tsakiyar filin Allah ta'ala, babu gida gaba babu a baya ko giccin mutane babu a wajen, sai zuciyarshi ta shiga dokawa da ƙarfi, yayinda wani abu ya soma fizgarshi zuwa wajen motar da ya gani a nesa kaɗan da shi.
Zuciyarshi tayi tsalle ne a yayinda idanuwansa suka sauka akanta, kwance ta ke a wajen idanuwanta a rufe gashin kanta ya barbaje a ƙasan wajen sanadiyar ko ɗan kwali babu akannata, ga ruwan hawaye da ke silalowa daga idanuwanta da ke a kulle, bakinta a bushe ƙayau ammm kunnenshi na iya jiyo ma shi sautin kukanda take can ƙasa cikin dasashiyar murya, tsintar kanshi yayi a durkushe kusa da shi cikin wa ta iriyar murya ya ce da ita.
"Baiwar Allah mi yayi zafi haka da za ki kwanta a ƙasa kina kuka, hakan ba mutunci bane ki daure ki jure koma mi ke addabar rayuwarki wa ta rana sai labari."
Jauhar data jima tana neman wanda zata zazzagewa cikinta amma ta rasa, jin muryar wani a kanta ya saka ta buɗe raunanun idanuwanta da suka yi jazur sukai luhu-luhu, alamar ta yi kuka baɗan ƙarami.
A karo na farko kenan da taji tanaso ta buɗe cikinta ga wani, wani wanda zai fahimceta yai alƙalanci a cikin bauɗaɗɗiyar rayuwarta, ko babu komi tana so ya fahimceta ya fahimci iri ɗaci da baƙin cikin da ke baibaye cikin rayuwarta.
Yunƙurawa ta yi tare da tashi zaune sannan ta ce cikin disasshiyar murya.

"Tun tasowata ta ke bina da shairi iri da kala, bansan so ba bansan gata ba ina rayuwa a gidanmu kamar a kurku, ƴan aiki sunfini matsayi da ƴanci banida ikon yin komi, komi zanyi kuskurene muryoyin na amsawa a cikin kaina da hayaniyar faɗan Daddynah, ya suke so inyi, miye ribarta da take yi min zagon ƙasa, miyasa sai ni minayi ma ta da zafi haka, banida ikon koda haɗiyar yawu a gabanta tana cin galaba a kaina ta rabani da Papah ta mallake komi ya zanyi, nace ya zanyi da raina❓."
Ta yi maganar a tsawace gamida sake ɓarkewa da wani sabon kukan har jikinta na jijjigawa.
Zama ya idasa yi a wajen tare da soma faɗin.
"Haka suke, nasan wacce kike nufi nima abin da nike fuskanta kenan a halin yanzu, zuciyata na suya rayuwata sam batada amfanin, bazata taɓa bari inji daɗin duniya ba komi nawa natane ni kaina banida iko da kaina ita ke da ni, inajin gajiya sosai da hakan sai de banida yanda zanyi dole nike haƙura ina haƙura da komi dan kawai insamu albarkarta."
Yana kaiwa nan a zancensa wasu irin hawaye masu zafin gaske suka silalo ma shi, sai da ya rintse idonshi da ƙarfi sannan ya buɗe su yanajin zuciyarshi na matsewa waje ɗaya.
"Mi yasa hakan❓."
Ta tambayeshi zuciyarta na rugurgujewa a ƙirjinta.
"Ita ce ta raineni, Ummanah ita kaɗaice sanyin idanuwana kuma ita kaɗaice take sakani a ƙunci da damuwa iya wannan kaɗai na sani."
Sharɓar majina ta yi sannan ta sake gyara zamanta tanajin wani na daban na baibayeta.
"Matar Papa ce, itace ke ƙoƙarin ganin bayana, ta tsane ni ta saka kowana ya tsaneni rayuwa tayi min zafi, ina jin kaina daban da sauran mutane, yace min zai zo gareni amma bai zoba, yace min zai tsaya min sai de ban sake ganinshi ba yace komi zai daidaita a gareni sai de babu abin da ya canza illa sake damalmalewar al'amurra, shin a ina zan ganshi?."
Ta faɗa tana kallonshi ciki yanar da idonta ya yi.
"Waye shi ɗin?."
Suhail ya tsinci kanshi da jefa ma ta tambayar, amsar data bashi ce ta tsaida jinin da ke yawo a jikinshi.
"MUHASEEN sunanshi MUHASEEN."
Ta faɗa tana maimaitawa har saida sunan ya zauna akwanyar Suhail.
Lokaci ɗaya jinin jikinshi ya soma tafarfasa da wani abu na daban, abinda ba zai iya cewa komiba a kai dan bai san yanayin ba.
"Ina so insake ganinsa, ina so ya sake bani ƙwarin gwuiwa kamar yanda yayi a baya zuciyata na mararin sake ganinshi, ina da tabbacin rayuwata zata inganta idan yana tare da ni, ya zanyi?."
Ta dire maganar tana tambayarshi, gwauron numfashi ya sauke sannan ya furzar da huci daga bakinsa.
"A halin yanzu ba iya ke kaɗai ba har ni ina son ganinshi, ina zamu gano shi?."
Wannan tambayar da Suhail ya yi itace ta zama sanadiyyar buɗe ƙofofin ƙaddarar da aka jima da kullesu, aka ɓoye mukullan a inda hankali bazai kai ba, da ace yasan abin da zai faru daga lokacin da aka ambaci sunan MUHASEEN a gabanshi, da bai yi kuskuren fitowa daga gida har ya haɗu da Jauhar ba, da ace yasan abin da ke binne a ƙasan sunan Muhaseen da bai yi kwaɗayin son haɗuwa da shi ba, dole cikin biyu ɗaya ya faru, ko rayu ko mutu.

Wani abu ne me kama da tsutsa ya shiga yawata acikin ƙoƙon kan Suhail, nan take wani abu me kama da tafasar jini akan wuta ya soma yawatawa a cikin naman jikinshi.

BAƘIN DAJI.
Wani mummunan baki ƙirin ɗin mutum ne, me suffa irinta aljannu jikinshi saye da jajayen tufafin kanshi da ƙahunna guda biyu hannunshi ɗaya riƙe da sandar tsafi ga wa ta ƙatuwar kwarya da jinin haɗe da tsutsotsi a ciki, cikin mumunar muryarsa me kama da saukar aradu ya dakawa mutanen da ke durƙushe a wajen wa ta razananniyar tsawa data rikita dajin baki ɗaya, hallitun da ke ciki suka shiga neman maɓoya.
Da wani yaren me kama da kukan sauro ya soma magana a tsawace, yanayi bakinshi na feshin wuta, yayinda wasu mutane biyu da kw wajen suka miƙe tsaye hannayensu a kai fuskokinsu bayyane da matsanancin tashin hankali, ɗaya daga cikinsu har hawaye me kama da jini ya soma sauka daga idonshi, gaba ɗayansu sun ɗimauce, mutumin ya ɗauki lokaci me tsayi yana faɗan kafin daga baya ya buga sandarshi da ƙarfi nan take mutanen wajen suka shiga ɓacewa, duhun wajen ya soma washewa haske na baibaye wajen, daga haka wajen ya shiga ɓacewa kafin daga bisani komi ya shafe wawakeken fili me cike da bishiyu ya bayyana.

Alhaji Bello da Manga ne suka bayyana a ƙofar wani ɗaki, nan take suka shiga maida numfarfashi kamar waɗanda suka yi tseren gudu, goshinansu sai ɗigar zuba suke yayinda hawaye da majina ke kwaranya a fuskar Alhaji Manga, a rikice ya kalli Alhaji Bello yana faɗin.
"Na shiga uku Bello, shikenan aikina zai ɓaci ya zanyi, wai miyasa hakan ke faruwa mina gaza wajen yi, miye matsalae.....✍🏻

KUYI HAƘURI BA YAWA KUMA BA EDITING, WALLAHI NAYI BUSY SHIYASA SORRY HABIBTYS🌹

MARYAM STAR...⭐✍🏻🤝
https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀
بسم الله الرحمن الرحيم.
Chapter 6 · 0% Book details