← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can cikin barcin na shi, ya soma jin kamar ana kiran sunansa da ƙarfi, bayan kiran sunansa kuma wani abu me kama da ganga ya shiga karaɗe kunnuwansa, kamar wanda aka zaburar haka ya miƙe dangargar asaman gadon, yayinda jikinshi ya soma tsima kamar ana jona ma shi shocking, numfashi na sama-samar kamar zai bar jikinshi.
"MUHASEENNNNNN." Sautin kiran sunanshi ya ƙara karaɗe duniyarsa, nan take ya kwalla gigitacciyar tsawa ya faɗi a wajen yana gurnani kamar zaki, yawu haɗi da wani jan abu me kama da jini ya shiga dalala daga bakinsa, yayin da ya soma murje-murje yana doke-doke a ƙasan wajen, hannayensa duka biyun ya saka a wuyanshi da yaji kamar an shaƙe shi, jijiyoyin kanshi suka fito raɗo-raɗo, daga saman P.O.P ɗin ɗa ki yaji sautin wa ta mummunar murya na faɗin.
"Kayi mana taurin kai, ka ƙi shiga cikinmu, ka ƙi sadaukar mana da abin da muke so a gareka, to lokaci yayi da zamu samu abin da muke so kota ƙarfin tsiya, muna maka albishin cewa jininka ya shigo cikin mu, zai ƙarasa mana abin da muka fara, daga yanzu ka soma ƙidayen ranakun mutuwarka, dolene ka mutu MUHASEE."

Lokaci ɗaya numfashin ya ɗauke, hakan gayi daidai da ambatar, "La'ilaha illa'anta subahanaka innikuntu minazzalumin." da yayi, daga nan ruhinsa ya rabu da gangar jikinsa.

KUBWA
Tun da Suhail ya tashi a barci Binta ta haushi da masifar faɗa akan ya kwashe ruwa yayi wanki, dole ya fita ya ɗebo musu wani, jikinshi na kwankwatsa a dole ya tashi ya harhaɗa kayan ruwan ya fice, sai da ya tsaya masallaci yayi sallah, sannan ya nufi wajen da ake ɗibar ruwan, sai da yai sahu biyar sannan ya cika komi, a gaggauce ya shiga wanka bayan ya fito ya wanke baki tare da kwashe kayanshi daya wanke, ledar namanshi da bai ci ba da lemo ya ɗauka dasu ya karya, wajen ƙarfe bakwai na safiya ya fito tsaf da shi, bayan ya gaisar da Binta da Abba wanda sam baya mashi magana, idan ya kaga Abba ya tanka akan lamarin Suhail to tabbas wani abu yake da buƙata, kamar kullum maganar Binta sai da ta nauyaya zuciyar Suhail, har ya fita yana jin nauyin maganganun na ta.
"Ka fita nema Suhail, kayi aiki tuƙuru amma badomin kanka ba, dan ka ingantamin rayuwa ka wadata ni da arziƙi me tarin yawa, idan kaga wani me kuɗi ko me arziƙi ka zabura kanka kaji kana so ka kamoshi arziƙi idan da hali ka zarce shi, idan kaga mota ta wuce ka kalleta da burin siyamin irinta, domin ba kai keda kanka ba ni ke da kai, dole yanda na dama haka zaka sha, dolene ka biyani ɗawainiyar rainonka da nayi na tsayin shekaru, dole ka wadatani da sukanin abin da zan buƙata saboda bakada kowa sai ni, nice kowa naka."
Yauma a ƙasa ya taka har sai da yayi nisa sosai da gidan, sannan ya hau abin hawa aka saukeshi a kasuwa, haka ya zage yayi aikin gyaran kayan miya, sannan ya zauna ya ci gaba da siyarwa, yauma bai jima ba komi ya ƙare, dan haka ya tattare inashi-inashi ya ƙara gaba, yau da tunanin samun canji aiyuka ya tashi, shiyasa da yaje restaurant bai yi wani aiki ba, ya sanar da bazai sake zuwa aiki ba su nemi wani, babu yanda Manager dake jin daɗin aiki da shi baiyi ba akan ya daure yaci gaba zasu ƙara mashi kuɗi amaa ya ƙiya, dan tunaninshi ya fara canzawa, ga wahala da tayi ma shi yawa haka ya yi musu bankwana ya tafi.
Haka ya ƙarar da wunin ranar yana gararambar neman aiki, bai dakata ba sai da ya samu ta hanyar wani alhaji da yaje wani ƙaton kanti yin siyayya, a kallon farko da Alhaji ya yi mashi yaji wani abu ya ɗarsu a kanshi sai cewa ya yi.
"Ɗan samari idan aiki kake so to kazo ni zan baka aiki a gidana"., buɗar bakin Suhail sai cewa ya yi.
"Kwarai kuwa aiki nike nema amma aikinda zai kawo min kuɗaɗe masu yawa, kominene aikin dumin wahalarsa zanyi."
Ba tare da sanin Suhail ba ya jefa rayuwarsa a halaka, da ace yasan baƙar ƙaddarar da ke baibaye da shi silar wannan neman aikin da ya haƙura ya ci gaba da yin buge-bugensa har Allah ya kawo mashi warwar, amma ƙaddara ta rigayi fata, kalaman Binta sunyi nasarar ingiza zuciyarshi har ya yanke hukuncida daga baya shi da ita zasuyi kuka tare da danasani...

Ɗaga kanshi ya yi yana ƙarewa tangamemen falon kalo, yana jin cewar lokacin farantawa Binta rai yayi, domin tuni zuciyarshi ta ɗaukeshi zuwaga tunani gashi can yayi kuɗi ya mallaki tangamemen gida ya saka Binta a ciki, ya wadatata da kayan more rayuwa kamar yanda kullum ta ke sanar da shi ya nemi kuɗin dan ya wadatata, yanaji a ranshi lokaci yayi da ruwan albarkoki zasu jiƙe shi, murmushin da yakan jima bai yi ba ya saki kafin yakai zaune a saman sopa yanajin wani abu daban a ɗayan sashen zuciyarshi, sashen da ke yawan ankarar da shi akan daidai, a jikinshi ya ke jin kamar zai aikata kuskure, saide idonshi ya gam rufewa akan cikar burunshi, hakan ya saka ya danne komi da yake ji.
"Hello Manga, ina sanar ma ka wallahi na yi mana babban kamu, muna cikin alheri wallahi yanzunan na samoshi a hanya kayi ƙoƙari ka dawo yau idan son samu ne zuwa anjima kaɗan sai mu tattauna yanda zamu ɓullo ma shi."
Daga can cikin wayar wa ta murya ta amsa da faɗin.
"Kai mutumina kaja kaya wallahi, to shikenan kar ka damu zan yi ƙoƙarin dawowa idan na samy fly, nima akwai magana a bakina wallahi."
Da haka suka yi sallama suka kashe wayar.
Alhaji Bello kennan shahararen ɗan kasuwa wanda ake damawa da shi a harkar kasuwanci a ciki da wajen Nigeria, yana da shares sosai a manyan kamfanoni, a zahirin gaskiya mutumin kirki ne amma a baɗini tantarin kanshi ne, domin kuwa kura ne lulluɓe da fatar Akuya, yana daga cikin manyan ƙungiyoyin asiri shi da sauran abokanansa, daga cikin manyan aminansa akwai Alhaji Abdu Manga, shima babban mutum ne da ake alfahari da shi kuma a tare suke ƙulle-ƙullensu.

Gaba ɗaya man kan Suhail ya gama tsiyaye wajen ganin zallar dukiyar da aka narka, lafiyayyen abinci aka gabatar ma shi, amma ko ruwa sai ya kasa ɗauka ya sha, hakanan ya tasa abincin a gaba yana kallo, bai ankare ba sai jin sautin Alhaji Bello wanda bai san lokacin da ya dawo falon ba yana faɗin.

"A,a ɗan samari ga abinci an aje maka amma baka ci komi ba, to ko ruwan ka ɗauka ka sha."
Ƙur Suhail ya ƙure ruwan da kallo, sai yake ganin kamar abu ne ke motsi a cikin ruwan, amma sai ya basar da yanayinsa na miskilanci ya ce.

"A'a Alhaji banajin yunwa, idan babu damuwa ina so a faɗamin aikina dan ina so zan je wani wajene yanzu ba jimawa."
Murmushi me cike da ma'anoni Alhaji Bello ya yi, sannan ya ce.
"Aikin naka me sauƙi ne sosai, amma ba yau zaka gara ba, sai zuwa gobe idan Allah yayiwa babban abokina dawowa, karka damu zamu ɗauke aiki domin ka cancanta yanzu dai ga wannan."
Ya faɗi yana zaro ɗaurin sababbin ƴan dubu-dubu guda biyu ya miƙawa Suhail.

Wani abu me kama da ƙyanƙyami ne ya kama Suhail, gashidai a zahiri kuɗi ya ke gani, amma kuma yana jin su na saka ma shi tashin zuciya, ƙyamarsu ya ke, da sauri ya girgizawa Alhaji Bello kai alamar a'a.
Ba tare da komi ba Alhaji Bello ya saka ma shi kuɗin a aljihun gaban rigarshi tare da dafa kagaɗunsa yana faɗin.

"Karka damu cancantarka ce ta haɗamu da kai, zaka ji daɗin yin aiki da mu sosai domin ina me tabbatar ma ka zaka samu alheri, yanzu ka tashi muje zan baka driver da zai kaika har gida, gobe zai zo ya taho da kai, wannan kyauta ce nayi maka."
Yana gama faɗin hakan ya janyo hannun Suhail tare da tadashi tsaye suka fice zuwa compound inda ɗirka-ɗirkan motoci ke jere.

Kallon yanda fuskar Binta ta washe da maɗaukakin farin ciki Suhail ke yi, yayinda zuciyarshi ke dokawa da sauri cike da tsoro, gadai farin ciki ya gani a fuskar Binta, kuna yasan shine silar farin cikin amma kuma ya gagara samun nutsuwa a zuciyarsa haka kawai yaji mutumin bai kwanta masa a rai ba har ya soma tuhumar kanshi akan bin bayan mutumin har ya je gidanshi.

"Oh ni Bintar Malam, yanzu dan Allah Suhail wannan kuɗaɗen du nawa ne ni kaɗai, ma sha Allahu gaskiya niɗin me sa'ace sai yanzu na tabbatar da kai ɗin me rainona ne da kyau gwarzon sadauki, albarkar Allah ta tabbata a gareka ka faranta raina."
Su ne maganganun da Binta keta faman maimaitawa hannayenta riƙe da ƙuɗin da Suhail ya bata.
Runtse ido Suhail ya yi, yanajin farin ciki na baibayeshi da ya samu jin kalma me tsadar gaske daga bakin Binta, yau dai ta saka ma shi albarka ga farin ciki kwance akan fuskaskarta, tabbas yaji daɗin hakan kuma yayi alfahari da ranar yaso kuma ya mance da zullumin da zuciyarshi ke yi akan Alhaji Bello amma ɗayan sashen shi ya gagara bashi haɗin kai, sai ya nisa a nutse ya soma magana.
"Na haɗu da wani Alhaji ne, shine ya baki kuɗin sannan ya ce zai bani aiki aikin nawa zai fara daga gobe, sai de kuma ni mutumin bai kwanta min a rai ba, hasalima ban so karɓar waɗannan kuɗaɗen ba shine ya tilasta ni, amma da na yanke hukunci akan ba zanyi aikin ba dan gaski....."
"Kai dallah sauraramin, bangane mi kake nufi, tashin farko mutum ya fara da baka maƙuden kuɗaɗe irin haka sannan kace ba zaka yi aiki da shi ba, wannan ƙarya kenan ba za'ayi hakan da ni ba wallahi aiki kamar ka yi shi babu fashi, ka ɗauka zaka yi aikinne danni zaka yi aikin dan ka biyani wahalar da nayi da kai, zaka yi aiki dan ka wadata ni, bakada buƙatar komi Suhail kai ɗin baka kai matsayin da zaka yankewa kanka hukunci ba har yanzu kana a ƙarƙashin kulawata."
Chapter 5 · 0% Book details