Sashe 16
Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Sarki,,,, Sarki Umma Sarki na gani a yau kuma a yanzu."
Ta yi maganar tana damƙar hannun Ummar da iya ƙarfinta gaba ɗaya ta ruɗe ta fita a hayyacinta.
Wani abu me ƙama da mashi ne ya caki zuciyar Umma, yayinda itama jikinta ya hau rawa ba gaira ba dalili, wani abu data daɗe da yiwa zuzzurfan rami ta bizne a can ƙasar zuciyarta ya shiga buɗewa da tsananin ƙarfi, sake damƙe Najla ta yi suka soma jijjiga atare.
"Ikon Me sama sai kallo, ke dai Najla baki gakiya da shirme da shashanci, yo shashanci mana idan ba shashanci ba minene hakan kike yi, kin zo kin ruɗa mata tana zamanta lafiya, Allah ya yaye ma ki wannan cutar, wataƙila Sarkin Aljannu ne ya ke wasa da hankalinki."
Ta faɗa ta na yin gaba ta barsu a nan, tallafar fuskar Najla Umma ta yi a cikin tafukan hannayenta, wasu hawaye na kwanciya a cikin idanuwanta cikin sarƙewar murya ta ce.
"Ma sha Allah, ina taya ki murna ƴata na cikar burinki da kikaga muradinki a yau, ina me adduar Allah ya amsa ya zama mijinki, Allah ya tabbatar da alkairinsa a tsakaninku."
Da ace Umma tasan cewar addu'ar da ta yi kamar tayiwa kanta ne, da bata yarda ta tsaya iya nan ba, da ta haɗa da kanta a ciki wataƙila hakan ya zama mukulin buɗe ƙofofin da suka jima a datse.
Kwanciya Najla ta yi a jikin Umma tare da ƙanƙameta tana jin yanda jikinta ke rawa har lokacin, tana jin kanta daban ga wani dunƙulallen farinciki daya dunƙule mata waje ɗaya a ƙasan zuciyarta.
A ranar zance da ta wuni bayar da labarinsa kenan, ko kulawa da ciwonta da ke mata zafi bata yi ba, illa sake maimaita labarin da ta ke yi ga du wanda ya shigo gidan, bakinta ko gajiya baya yi wajen bayar da labarin hasalima ko kalma ɗaya bata tsallakewa, sannan lokaci bayan lokaci tana kai hannunta a saitin hancinta ta shinshina ko zata ji mayen ƙarshin ya ragu, sai de yana nan daram ya kame a jikinta.
Tun tasowarta bata taɓa riskar rana me ɗumbin farinciki a gareta irin wannan ranar ba, saboda muhimmancin da ta bawa ranar ya saka ta nufi madafa ta samu tsinke ta saka a cikin wuta sai da ya yi zafi sosai sannan ta buɗe farar cinyarta ta rubuta date ɗin, sam bata ji zafin wutar ba sai ma buɗe wajen da ta ke yi ta kalla du bayan lokaci fuskarta ɗauke da murmushi me zurfi.
MUHASEEN
Tun zamanshi a kujerar da aka tanada don yin meeting ya kasa taɓuka komi, sai faman shan ruwan da aka aje a gabansa da ya ke lokaci zuwa lokaci, gaba ɗaya hankalinsa baya wajen yana can wani waje, wani waje wanda shi kanshi bai san ko ina ne ba, yayinda idonshi ke kallon lallausan hannunsa da ya nannaɗe hannun rigar izuwa sama, har lokacin yana jin ɗumin tafin hannunta me laushi na ratsa wajen yana bi ta jijiyon jikinsa yana isa har zuwa can cikin zuciyarsa.
Har aka gama dogon meeting ɗin bai ce komi ba daga ƙarshe sai Saleem ne ya tashi ya yi jawabi a madadinsa, daga nan kuma basu wuce ko ina ba sai wajen da aka gama loda kaya ana ƙirga kwantenonin da za'a dita da su daga company, nan ma bin mutanen wajen ya dinga yi da ido ba kuma dan hankalinsa na kansu ba, sai dan fuskar da ya ke gani kwance akan fuskokin mutanen wajen.....✍🏻
MARYAM STAR⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪.
Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb8OWPtBKfi1C9DGBa13
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)
𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪
✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2
𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀
𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 14
Iska ya shaƙa da ƙarfi ya cika bakinsa sannan ya furzar tare da saka hannu ta yamutsa sumar kan shi kamar me jin ƙaiƙayi.
"Alhamdulillah komi ya daidaita zamu iya tafiya yanzu."
Saleem ya yi maganar alamomin gajiya na bayyana akan fuskar shi da muryar shi.
A saman laɓɓa Muhaseen ya amsa shi da.
"Okay."
Yana yin gaba sauran gurds ɗin sa na take ma shi baya.
Kai tsaye gida suka yiwa tsinke, bayan isarsu Saleem ya sallami Gurds ɗin tare da tabbatar musu aikinsu na ranar ya ƙare, da murna wasusunsu suka tafi dan sun jima rabon da su samu lokaci irin na yau.
Gyare tsaf suka tarar da makeken falon, komi a tsabtace cikin tsari, babu abin da ke tashi illa sanyi AC da ke busawa tako ina, kai tsaye Muhaseen ya wuce sashen shi tun a hanya ya soma rage kayan jikinsa, yana isa ya jefar da su a ƙasa ya haye kan bed ya kwanta rigingine tare da zira ƙafafuwansa da ko takalma bai cire ba a ƙasa, a zahiri P.O.P ya ƙurawa ido amma a baɗini tunanuka ne hargitse a cikin kwanyarshi, lumshe ido ya yi tare da soma ƙidayar bugun zuciyar shi daya sauya ya koma very slowly, kuma duk dokawar da zuciyar shi zata yi sai ta doka da wani yanayi, kafin ya ankare wani barci me nauyi ya ɗauke shi, a cikin barcin ne kuma ya yi mafarki kamar yanda ya saba.
ABUJA
"Alhaji Bello mi ka ke faɗa min haka, tayaya za ku ɗauko abu tun daga tushe yanzu kuma da kuke gab da cimma nasara ka ce kun aje, miye ribar ɓata lokacinku da kuka jima kuna yi a banza, gaskiya dai ka sake tunani wannan sam ba mafita ba ce."
Wani babban mutum da zai yi sa'a da Alhaji Bello ya faɗa ran shi a ɗan ɓace.
"Ni ma dai abin ya so ya ɓata min rai, amma sai na share kawai, idan baka manta ba yau shekara ashirin da biyu kenan muna yaƙi akan wannan dukiyar, tayaya da rana tsaka za'a zo mana da wani zance marar tushe, indai yaƙi akan dukiyar MUBASHAR ne yanzu na soma, shima bokan sam ban yarda da shi ba, babu gaskiya a zancensa bazan bijirewa Me girma Dodo ba, zan kasance a ƙarƙashin shi har zuwa lokacin da burukana za su cika, batu kuma akan sadaukarwa ba zan yi ba dan ni sam ban yarda da wannan Bokan ba macuci ne."
Alhaji Bello ya faɗa yana ɗaukar goran ruwan da aka aje a gaban shi ya kai baki yana sha.
"To yanzu ta ina za mu fara, dan gaskiya ko ni na kwaɗaitu dana ji yawan dukiyar sannan ina tunani akan ba zamu sha wahala wajen samun ta ba, domin kuwa wannan yaron na shi da lallaine ya iya bi da ita ta hanyar data dace ba, yanzu minene abin yi."
Sai da Alhaji Bello ya shanye ruwan tas sannan ya aje goran tare da sake amatsar da fuskar sa wajen mutum cikin ƙasa-ƙasa da sauti ya ce.
"Mafita ɗaya ce Alhaji Ahmad, mafitar kuwa ita ce na samo wani yaro daga gani zai yi ƙwazo da farko naso in haɗa shi da Alhaji Manga, amma tun da ya bijiro da wannan lamarin sai na canza shawara, yanzu zamu ɓullo ma shi ta bayan gida ne a zahiri zan goyi bayan shi ya yinda a baɗini za mu gina kanmu domin kuwa farautar dukiyar Mubashar yanzu muka fara."
Miƙa ma shi hannu Alhaji Ahamadu ya yi suka cafke suna fariya irin ta su ta manya.