Sashe 13
Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
MAITAMA
Zaune ya ke ya rafka uban tagumi, yayinda ya da tsunduma a kogin tunani ya yi nitso a can ƙasan kogin.
Cikin kissa ta ke kallonsa tana murmushin a zahiri yayinda a baɗininta ta ke ƙudurta mugun nufi, aje flask ɗin hannunta ta yi a gabansa sannan ta matsa kusa da shi sosai ta dafa kafaɗarsa sannan ta ce.
"Haba Honey mi zai sa ka dinga damun kanka da tunani irin haka, kana so ka sawa kanka ciwo ne, yarinyar nan Jauhar ka san halinta sarai bai kamata ace kana sawa kanka damuwa saboda ita ba, ka share da lamarinta ka fuskanci rayuwarka data iyalinka kabarta da halinta mu muna buƙatar farin cikinka."......✍🏻
NASAN ZAKU JI YANAYIN LABARIN NA SAUYA SALO, KUYI HAƘURI KU BIYO NO SANNU A HANKALI KOMI ZAI WARWARE ZAKU FAHIMCI INDA LABARIN YA DOSA NAN GABA KAƊAN.
MUN GAMA DA SHIMFIƊAR LABARI YANZU ZAMU KUTSA CAN CIKIN LABARIN ƊUNGURUN GUM
ALHAMDULILLAH MUNA GAB DA DAMA FREE PAGE NAN KUDA, KU DAGE DA TAYA NI SHARE A GROUPS ƊINKU NA WHATSAPP DA FACEBOOK NAGODE SOSAI.
MARYAM STAR⭐⭐⭐......✍🏻 ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)
𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪
✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2
𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀
𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 11
Gwauron numfashi Papa ya sauke sannan ya kalli matarshi da ta ci ado cikin jan leshi wanda ke nuna kuɗinshi a fili, ta yi kyau sosai a idonshi, sai de a zuciyar shi ba hakan ba ne wata fuskar daban ya ke hangowa kwance akan tata fuskar, fuskar da ta zama wani yanki na rayuwarshi, yanzu da babu ita sai ya ke jinsa kamar ba cikakken mutum ba, ko farinciki ya ke yi yana ji a jikinsa bai cika ba kamar can baya.
Tafin da ta yi a saitin fuskarshi ne ya dawo da shi hayyacinsa daga duniyar tunanin daya afka, far ta yi da ido cikin murya me jan hankali ta ce.
"Honey ya dai ko na yi maka kyau ne da yawa?."
Sai kawai ya janyota zuwa jikinshi sosai yana murmushi ya ce.
"A koda yaushe ke me kyau ce musamman idan kika yi kwalliya irin hakan."
Sosai farinciki ya bayyana akan fuskarta na jin daɗin yabon da ya yi mata.
"Ga tea ɗinka nan karya huce."
Ita ta bashi tea ɗin a baki tana yi tana masa iyayi, shi kuma yana biye mata duda zuciyarsa a ƙuntace ta ke, sai bayan da suka gama ne sannan ya sake kallonta tare da faɗin.
"Ko dai zan je da kaina Hotels mafi kusa in duba ko Jauhar tana can, kar wani abu marar kyau ya faru da ita kinga na kira wayarta sau da yawa amma ba'a ɗaga ba hankalina ya gaza kwanciya."
Ya yi maganar yana kallon yanda fuskarta ta soma sauyawa da wani abu me kama da ɓacin rai, da ƙyar ta janye yanayin ta wanu marairaice cije da kissa ta ce.
"Na ɗauka mun gama wannan zance ai Honey, sanin kanka ne ko sau dubu zaka kira ta ba za ta taɓa ɗagawa ba, so ka daina damuwa kawai koma ina zata je ni nasan dole za ta dawo nan tun da bata da wanda suka fi mu, amma tun da ka matsa bara in saka security su bibiyi motarta."
Bata barshi ba sai da ta tabbatar ta goge ma shi tunanin Jauhar a cikin kanshi, ko da ta fice sai ta kama sabgogin gabanta ta share shi.
Yanayin da ya saba shiga ne yanzunma ya riskeshi, a du sanda Jauhar zata bar gida abin na damunshi sosai sannan kuma yana so ya yi maganar amma sam matarsa Hajiya Fatima bata tari, daga ƙarshe idan ta bashi tea ya sha sai ta zauna ta yi mashi fira, daga nan kuma sai barci me nauyi ya ɗauke shi ba tare da ya shirya ba.
Wawan Tsaki Hajiya Fatima ta doka tare da ɗaukar danƙareriyar wayarta ta soma kiran wani layi da aka yi save da My Sister.
"Hello Matar Alhaji ya ake ciki ne, inace komi ya daidaita."
"Mtswwwwww wani daidaito fa yana can yanzu haka yana zancen mayyar yarinyar can, tun safe na kaɗa ƙeyarta ta fice daga gidan amma har yanzu bai daina damuwa ba, yana can na saka shi barcin dole ai."
Dariya aka sheƙe da ita daga can cikin wayar sannan sautin murya ya sake fitowa.
"Kai wallahi Fatima wannan mijin na ki anyi uban ƴan taurin kai, wai kina nufin har yanzu bai haƙura da waccan Mayyar ba, gaskiya sai kin zage dantse idan ba haka ba ba zamu samu abin da muke so ta sauƙi ba."
"Hummm ke dai ki bari kawai gabaɗaya kaina ya kulle wallahi na rasa abin yi yanzu haka ga damammaki sai wuce ni suke yi, gaba ɗaya kaina ya kulle a kan mutuminnan, ni tsoro nike kar zaman jiran shekarun da na yi ya tashi a banza wallahi."
Haka suka ci gaba da tattauna ko waccensu na faɗin albarkacin bakinta.
KUBWA
Kwance Suhail ya ke a ɗakinsa saman katifarsa da ya gama kakkaɓewa ya shimfiɗa bargo, gaba ɗaya kanshi ya kulle tunanin yanayin da ya shiga a lokacin da ya furta sunan MUHASEEN kawai ya ke, ko yanzu da ya ke a kwance tunowa da sunan kawai da ya yi sai da ya ji kanshi ya doka da ƙarfin gaske, nan take ciwon kai ya safko ma shi, yunƙurawa ya yi tare da tashi zaune ya dafe kanshi yana aranto addu'o'i, ji ya yi kamar tsayuwar mutum a kusa da shi da sauri ya ɗaga kanshi da ke niyyar tarwatsewa abin da ya gani ne ya saka shi miƙewa ba shiri har jiri na kwasarshi.
Jauhar ce tsaye a gabanshi daga ita sai pant da bra ga kayan da ta cire a hannunta tana kallonshu cikin ɗan hasken da ke a kwai a ɗaki.
Da wani irin zafin nama ya tura ta baya ta faɗi ƙasa sannan ya juya baya a rikice gaba ɗaya ya rasa abin yi in banda rawa da sarawa babu abin da kan shi da jikin shi ke yi, sai faman zare idanu ya ke.
"Suhail."
Ta kira sunanshi a raunane tana jin azaba a hannunta data faɗa a kanshi.
Bai juyo ba kuma bai fita ba kawai de yana jinta ne.
"Wash hannuna, na yi wanka ba'a bani man da zan shafa ba ina jin sanyi sosai."
Yan da ya ji ta furta Wash hannunta ya tunasar da shi ya tura ta da ƙarfi kuma yasan zata iya faɗuwa harma ta ji ciwo.
Kamar ba zai juyo ba sai kuma ya juyo amma bai yadda ya kalli sashen da ta ke ba, sai kawai ya janyo abin da ya ke lulluɓi ya soma takawa da baya-baya zuwa inda ta ke, sunkuyawa ya yi tare da aje mayafin sannan ya ce a taƙaice yana tashi.
"Ki suturta jikinki."
A cikin ɗan hasken ta ke kallonshi tana kuma kallon abin da ya aje ma ta har ya fice daga ɗakin, sai kuma ta kalli jikinta tana son fahimtar mi ya ke nufi, dan ita bata gane komi ba ga hannunta da ke zugin azaba kamar zai ɓalle.
A ƙofar daƙin Binta ya zauna, sai de zamanshi ba jimawa ya tsinkayo muryar ta tana raɗa.
"Ka yi du yanda zaka yi ka samu kudanci da ita, yarinyar me arziƙi ce wataƙila ɗiyar shi Alhajin wanda zai ɗauke shi aiki ce ɓoye min ya yi bai faɗa min gaskiya ba, kai idan ma da hali kawai ku tafi wajen aikin a tare zan gobe idan zai ta fi kaima Alhajin ya baka aiki a wajensa ko mun huta da wannan baƙin talaucin."
Bai idasa jin abin za suke tattaunawa ba ya miƙe yabar wajen dafe da kanshi da ke masa ciwo bana wasa ba.