Sashe 17
Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A hankali ya soma buɗe idanuwan shi da suka yi ma shi nauyi sosai, yunƙurawa ya yi tare da tashi zaune yana dafe kanshi da ya yi ma shi nauyi sosai, kallon ɗakin ya soma yi yana tariyo abin da ya faru daren jiya kafin barci ya ɗaukeshi, yasan dai ya sha tea da Hajiya Fatima ta kawo ma shi ya kuma zauna yana jiran dawowarta amma bai san yanda aka yi barci ya ɗauke shi ba, ture runanin komi ya yi tare da tashi ya shiga toilet ya ɗauro alwala, Sallah y gabatar bayan ya gama ne ya tsinci kan shi da addu'ar Allah ya kare Jauhar aduk inda ta ke, shi kan shi bai san dalilin da ya saka ya ke ƙyararta ba amma ya sani kaf cikin ƴaƴan shi Jauhar ta dabance ya fi son ta fiye da kowa, yana jin takaici akan yanda ta sauya daga hallayenta na baya ta ɗauko wasu ta yaɓawa kanta, tunaninta kaɗai ke addabar rayuwar shi sam baya da wata matsala da ta wuce ita ɗin, juya kan shi ya yi zuwa baya ya kafe wani fram da aka sauke daga sama da kallo.
Kyakkyawar mata ce mara tas fuskarta na bayyanar da murmushi ne annuri, yayin da ta juyar da idanuwanta zuwa ga wajen wata ƴar yarinya me kyau da ke zaune akan cinyar wani magidanci wanda a cikin hoton hankalin shi ya karkata wajen matar da ta shagala wajen kallon Babyn.
A hankali hawaye suka silalo daga kuncinsa kewar matar na sake bijiro ma shi, a fili ya furta.
"Allah ya isar da rahamarsa a gare ki Nafeesa, haƙiƙa kin tafi kin bar ni cikin kewa da tunaninki na san hae abada bazan taɓa samun wacce za ta maye min gurbin ki b....."
Bai ƙarasa faɗi ba ya tsinkayi muryar Hajiya Fateema asaman kansa ta na faɗin.
"Yanzu Honey du zaman da muke yi dama kana kallona a matsayin kasashiya, mi na rageka da shi ni dai nasan ina yin bakin ƙoƙarina wajen kulawa da kai da waccan gagararriyar ƴar taka."
Da sauri ya miƙe tsaye fuskarshi da alamar fushi ya ce.
"Haba Fateema taya za ki dinga danganta min ƴa da gagararriya ce miki na yi ta gagare ni?."
Hajiya Fatima da ta ware idanuwanta a kan shi tana kallon shi da tsananin mamaki jin ya kira sunanta gatsalar sai ta buɗi baki ta ce.
"Ta gagareka mana idan har bata gagare ka ba tayaya zata dinga bijirewa maganarka tana yin du yanda ta so, saboda bata ɗauke ka uba ba sam bata damu da kwana a cikin gida ba tafi son zaman hotels wanda Allah kaɗai yasan abin da ta ke aikatawa a can."
"Tasssss" Alhaji Laminu ya wanke fuskarta da taci uban ado da mari, hannunsa na karkarwa ya shiga nuna ta da yatsa yana faɗin.
"Ya isa hakanan ya isa, na gaji da sauraren maganganu marasa daɗi daga bakin ki akan ƴata Juhar ƴata ce kuma ina tsananin son ta ko an gaya ma ki ina jin daɗin halin da take ciki a yanzu, to ya kamata ki sani abin yana matuƙar ƙona zuciyata abin na damuna matuƙa."
Ya aje maganar yana haki kamar wanda ya yi tseren gudu, hawaye Hajiya Fateema ta soma saki sam marin da ya yi mata bai yi mata ciwo ba kamar yanda ya furta yana son Jauhar a gaban idonta, juyawa ta yi ta fice daga ɗakin tana fashewa da kukan kissa, komawa ya yi ya zauna tare da dafe kan shi da ke sara ma shi, gaba ɗaya komi ya hargitse ma shi, kwanciya ya yi a rigingine tare da soma tariyo rayuwar shi tun daga tushe, yana lalibo inda ya gaza ko ya yi kuskure da komi ke zuwa ma shi a juye.
FLASH BACK
RAYUWAR ALHAJI LAMINU GABATA
GABATA Family ne me dogon tarihi tun daga iyaye da kakanni, ahaline da ya gaji dukiya tun daga tushe, a kwai manyan jagorori da ke riƙe da ragamar ahalin daga ciki a kwai, Alhaji Mu'azu da kuma Alhaji Ahmad sannan me bi musu Alhaji Sa'idu, a wannan zamanin su ke riƙe da ahalin kuma sune masu tsawatarwa idan aka yi abin da ba daidai bane.
Akwai ƙaƙƙarfan zuminci tsakanin Alhaji Mu'azu da Alhaji Sa'id, zuminci da ya zamana ba zaka iya tantance abin ɗaya daga cikin su ba komi nasu a haɗe ya ke babu me jin kansu, hatta ta fanin iyalima sun haɗe iyalansu waje ɗaya bayan da suka gina sabon gida a cikin estate ɗin su me suna GABATA ESTATE da ke cikin garin Katsina, yanda mazajen suka haɗa kai haka mataye da ƴaƴayensu suka haɗe kawunansu.
Babban ɗa a wajen Alhaji Mu'azu shi ne Laminu, yaron da yafi soyuwa a wajen Alhaji Mu'azu Gabata kasancewar shi ne ya biyo rabi da kwata na halayyar mahaifinsa, yayin da kuma ya kasance ɗa na farko a cikin ƴaƴan Alhaji Mu'azu hakan ya saka sosai Alhaji Sa'idu ya ke ƙaunar Laminu kasancewar bai samu haihuwa da wuri ba, kuma matarshi ɗaya me suna Aishatu, gaba ɗaya komi na rayuwar Laminu yana a tsakanin iyayensa guda biyu, yakan yi du abin da ya san zai saka su farin ciki sannan yana barin abin da ya san basu so koda kuwa yana matuƙar son abin.
Allah ya bawa Alhaji Sa'idu ƙaruwa matar shi Aisha ta samu ciki cikin ikon Allah, bayan watanni tara ta sintilo ƴarta mace kyakkyawa ma sha Allah, sai de yarinyar ta zo da lalurar rashin lafiya tana fama da lalurar lumfashi, an kaita asibitoci da dama amma ba'a wani samu ci gaba ba hakanan iyayenta suka dinga tattalinta gami da taka tsantsan, yayinda Laminu ya yi uwa yai makarɓiya akan yarinyar da aka sakawa suna Jawahir, koda yaushe yana tare da ita yana bata kulawa, har lokuta na musamman ya ke warewa dan ita kawai musamman da marice idan ya dawo daga makaranta yana ɗaukarta ya dinga yi mata wasanni, du wasu dokoki na likitan da ke duba ta yana da su a cikin kan shi, haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa har Allah ya kawo lokacin da Jawahir ta girma ta zama budurwa.
Tun tashinta ta na ƙarama tasan da zazzafar kulawa me cike da soyayya da yayan ta Laminu ya ke bata, hakan ya saka itama bata aje ƙofa ko da yar kaɗan a zuciyarta da wani ɗa namiji zai iya shiga ba da sunan soyayya, yayanta Laminu shi ne farincikin ta.
Bayan ta kammala karatunta bata nemi aiki ba saboda lalurar da ta ke fama da ita, sai aka tsaida lokacin auren ta ita da yayanta Laminu, yayin da a lokacin aka haɗa aurarraki na jikokin da ke cikin ahalin GABATA, sosai aka sha hidima abin sai sam barka, bayan auren Jawahir da Laminu ana ta sake tabbatar da lallai babu namijin da zai iya son ta fiye da yayan ta Laminu, domin kuwa taf ya cike duniyarta da zallar farin ciki yana bata wadatacen lokacinsa, hakan ya saka itama ta zage wajen kulawa da shi sosai da sosai du abin da ta san zai saka shi farinciki shi ta ke yi, a fagen kulawa da miji tana sahun gaba dama can ita mace ce me sanyin hali gami da nutsuwa, ko a family bata hayaniya da kowa ita kowa nata ne ga kyauta da take da ita, kamar yanda Alhaji Sa'id ya sakar mata bakin aljihun shi ta ke yanda ta so haka Laminu ke cika ta da kyaututtuka iri da iri musamman kyautar kuɗaɗe da ta ke rasa abin da zata yi da su, hakan ya saka hannunta buɗewa da kyauta.
BAYAN WATANNI
Bayan watanni da yin auren su, zaune ta ke akan sofa ha haɗe cikin tsadaden leshi ɗan yayi, fuskarta ɗauke da kwalliya me sauƙi wacce ta sake fito da zahirin kyawunta, remote ne a hannunta tana sauya channel har lokacin akwai kwantacen murmushi da ke bayyane akan fuskarta, turo ƙofa aka yi tare da shigowa da murrmushi ta kalli saitin ƙofar sai cin karo da ƙawarta ƙwalli ɗaya ta yi me suna Fatima, Fatima ita kaɗai ce ƙawa ga Jawahir .....✍🏻
MARYAM STAR⭐⭐
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3&amv=2
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)
𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪
✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2
𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀