← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun bayan shigarsa ɗakin fadawan da ke tsaron lafiyarsa suka shiga kewaye wajen bayan sun rufe ƙofar, dan umarnine daga sama akan bawa wajen tsaro da kariya na musamman, babu mahaluƙin da ya isa ya gifta ta wajen ba tare da an gan shi ba.

ƊAKIN DUHU.
Zare idanuwanta da suka ture zuwa jajaye ta yi tana sake saita ƙwari da bakar da ke zane jikin ɓaƙar takarda, fari sol ɗin hakkin wanda ya zama shi ne kibiyar ta saita a daidai saitin alon ƙirjin mutumin da aka zama da zan fenti, sannan ta saka yatsanta ta harba da iya ƙarfinta, a wannan karon baya ta yi da sauri jikinta na rawar mazari, duk da ta kauce zuwa ƙasa sai da zafin dafin kibiyar tsafin ya huro mata a gefen idonta har cikin kai, inda nan take gashin wajen ya ƙone saboda azabar ƙarfin tsafi.
Zare jajayen udanuwanta ta ci gaba da yi bakinta a buɗe sanda ta ɗago takai dubanta akan zanen takardar, gumin tashin hankali ta sharce tare da kallo shatin harbin kibiyoyin da tayi amma im banda ɗaya jal babu wacce ta harba daidai, damƙar baƙar takardar ta yi da iya ƙarfinta zuciyarta na tafarfasa tana ci da wuta, bata jira komi ba ta saka hannu ya yage takardar biyu hakan bai ishe ta ba sai da ta ketata gutsi-gutsi sannan ta ɗauki wata ƙwaryar da aka saka alƙalami a kai da jini a cikinta ta yi wurgi da ita nan take ta faɗi ƙasa a haukace ta shiga ihu gami da kururuwa tana gwara kanta da bango.

SASHEN GIMBIYA.
Da tsananin gudu hadimai biyu mata suka shiga sashen Gimbiya Husna bayan sun nemi izini a gaggauce, a gabanta suka zube suna haki kafin ɗaya daga cikin su ta soma kora jawabi cikin ɗimauta.
"Allah ya taimaki gimbiyar Sarki muna masu baƙin cikin sanar da ke cewar ciwon Sarauniya Zainaba ya tashi yanzu-yanzunan tana a cikin mawuyacin yanayi tana da buƙatar agajin gaugawa."

Farinciki ne ya baibaye zuciyar Gimbiya Husna, yayinda a fili ta tashi daga kishingiɗen da take a kiɗime tana jeranto salati sannan ta ce.
"Na yi umarni a sanar da Sarki faruwar wannan lamari, sannan ina me jajantawa Allah ya bata lafiya, zan shiga yanzu-yanzunan in duba jikin nata."
Tana gama faɗin hakan ta miƙe tsaye, yayin da Kuyanginta suka shiga take mata baya cike da ladabi.

Da hanzari bayin suka tashi dan isar da saƙon Gimbiya Husna zuwa ga Me martaba Sarki.

Zagaye matar da ke kwance a ƙasa kamar gawa Gimbiya Husna ta soma yi, wanu irin sanyi na baibaye zuciyarta yayin da a ƙasaice ta tsuguna ƙada nesa kaɗan da matar sannan ta sona faɗin.
"Sarauniya Zainaba tabbas za ki dawwama a wannan yanayin ba za ki sake jin daɗin rayuwarki ba, taki ta riga da ta ƙare ki jira zuwan lokacin da zan tsinke sauran igiyoyin da ke riƙe da numfashin ki "
Ta yi maganar tana yin alamar yankewa da yatsun hannayenta biyu cike da mugunta.

Wani mummunan murmushi Sarauniya Zainaba ta yi a ƙasan ranta sanda kalaman Gimbiya Zainaba suka sauka a cikin kunnuwanta, tsaf ta gama naɗe dukanin maganganun data faɗa mata a kwanyarta tana jiran cikar lokacin data ɗiba dan aiwatar da ƙudurinta.
Fit Gimbiya Husna ta fice daga ɗakin tana sharar hawaye kamar da gaske, yayinda gabanta yai mummunar dokawa jiyo amon sautin muryar Sarauniya Zainaba na tashi cikin mummunar dariya, bata ƙara mintuna biyar a wajen ba ta fice kuyangin ta na take mata baya.

Sannu a hankali ya soma jin yana dawowa daidai yayin da wannan abin da ke sukar ƙahon zuciyar shi ya tsaya lokaci ɗaya, muryoyin da ke yi ma shi amsa kuwa suma suka ɗauke kamar laukewar ruwan sama a lokacin damuna, a hankali ya ɗaga idanuwan shi da suka jiƙe jagab da ruwan hawaye yana kallon saitin wani waje a cikin ɗakin na alfarma a fili ya furta.

"Idan ke ce zaki zamo silar warwarewar tsakuɗaɗen zaren daya baibaye rayuwata, na roƙe ƙi da ki sake bayyana a gare ni a karo na biyu, ina da buƙatar kwarin guiwa dan aiwatar da tarin aiyukan da ke gabana, ki zo ki zama hasken da zai haska min hanyar duhun da zan tunkara."
Ya yi maganar yana damƙar iska a cikin hannuwan shi sannan ya langaɓe kan shi gefe ɗaya yana fizgar numfashin sa.....

LEGOS NIGERIA
AGEGE.
Yunƙurawa Najla ta yi tare da tashi da ƙarfi har taba bige hannunta da jikin ginin da ke kusa da gadon da ta ke a kai, da sauri ta dafe saitin zuciyarta da ta sauya yanayin bugu lokaci ɗaya, gaba ɗayanta a ruɗe ta ke har bata iya tantance inda ta ke jiyo sautin muryar Umma da take jin maganarta can sama.
"Innalillahi Najla lafiyar ki ƙalau kuwa, ki yi addu'a ki maimata abin da zan faɗa, Hasbunallahu wani'imal wakil."
Caraf Najla ta amshe tare da soma maimaitawa da ɗan ɗaga sauti yayinda gaba ɗaya jikinta ke rawar mazari kamar wacce aka jonawa shock.......✍🏻

LABARI DAI NATA SAUYA SALO, GA SHI MUN ZO MASARAUTA, TO DAI KU BIYO NI DAN WARWARE ZARE DA ABAWA KARKU MANTA DA DANNA MIN LIKE SANNAN KU TAYA NI SHARE A GROUPS ƊIN KU NA WATSAPP.

NI CE TAKU

MARYAM STAR ⭐⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3&amv=2
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 19
Hawaye ne suka sulalo daga idanuwanta, sai ta damƙi hannun Umma da ɗan ƙarfi cikin muryar kuka ta ce.
"Umma,,,,,,,,Ummana."
Cike da tausaya mata Umma ta share mata hawayen da suka cika idanuwanta sannan ta ce.
"Na'am ƴata mi ya faru."
"Ummana dama kin ce in dinga neman zaɓin Allah ko?."
Ta yi maganar tana kallon fuskar Ummar ta cikin dishi-dishin hawayen da suka cika idanuwanta.
"Ƙwarai kuwa ana so a komi bawa zai yi ya nemi zaɓin Allah, domin kuwa shi ne kaɗai zai iya zaɓa ma shi abin da zai fi zama alkairi gare shi."
Kwantawa Najla ta yi akan kafaɗar Ummar sannan ta ce.

"To Umma dan Allah ki taya ni da addu'a Allah ya tabbatar da alkairi a rayuwata."
Sosai ta bawa Ummar tausayi sai ta shafi kanta da babu ɗan kwali sannan ta ce.
"In sha Allahu ƴata zan ƙara akan wacce nike yi miki akullum, amma faɗa min mike firgita ki a farci cikin ƴan kwanakinan?."
Ta yi tambayar amma a ƙasan ranta tana tsoro da fargabar tabbatar wani abu, wani abu wanda bata isa ta hana faruwar shi ba idon lokaci ya yi.

Sai da Najla ta ja hanci sannan ta ce.
"Daga shekaran jiya du sanda zan kwanta barci sai na yi mafarki da wasu mutane, suna tsorota ni sosai idan na farka sai inga kamar da gaske ina ganinsu, kuma ba ni kaɗai bace harda wannan Sar....."
Ko mi ta tuna sai kuma ta yi shiru bata ƙarasa ba.
Mummunar dokawa gaban Umma ya yi, yayin da tunaninta ya shallake komi ya isa a mafarkin da ta yi a dare shekaran jiya.
'Gudu ya ke iya ƙarfin sa ga jini tako ina yana zuba a jikin shi daga cikin manyan raunikan da aka ji ma shi, amma sai bai tsaya ba ya dage haiƙan yana gudun ba don ceton ran shi ba sai dan isa ga wani waje inda wata mata me kama da iya ke zaune a saman farin dutsi, yayin da wani yaro ke zaune yana kuka a nesa da ita, hankalin matar ne ya rabu gida biyu a tsakanin wannan me gudun yana son tunkaro ta da kuma wannan yaron da ke kuka har yana ƙoƙarin shiɗewa, da taga ba zata iya ceton su ita kaɗai ba sai kawai ta fashe da kuka me sauti, nan hankali wanda ke kukan ya dawo gareta da saurin shi ya taso tare da isa inda ta ke ya dafata, hakan ya yi daidai da isowar wancan wanda ke gudun wajenta, bai yi wata-wata ba ya faɗa jikinta ya ƙanƙame nan take numfashin shi ya ɗauke gaba ɗaya.'
Da sauri ta rintse idonta lokaci ɗaya jikinta na ɗaukar rawa, nan take ta soma jijjiga da ƙarfi idanuwanta na sauyawa daga haske zuwa launin ja, yayin da baƙar ƙwayar ciki ta soma ɓacewa, cikin ƙanƙanin lokaci ta fita daga kamaninta zuwa wata kamar, jikinta ya yi haske fayau kamar babu jini yayin da gashin kanta ya soma warwarewa daga kitson da aka yi mata, sai da ya warware tas sannan ya kwanta lub a gadon bayanta kafin ta ɓingire ta faɗi a wajen kamar matacciya.
Ba iya Najla da ke kusa da ita ba hatta da Uwale da su Jimmai sai da suka kiɗeme ganin abin da ke faruwa.
"Mun shiga uku mun lalace, shikenan matar mutane da mutu a gidan mu wayyo Allah."
Cewar Jummai data ɗora hannu aka ta shiga kurma ihu tana salati hankali a tashe.
Da sauri Najla ta yunƙura da niyyar ta taɓa jikin Ummar wacce ta faɗi a ƙasa, amma sai wani abu me kama da shokin ya kamata, da sauri ta janye hannunta tana zare ido sai kuma ta sake komawa da niyyar taɓa ta ɗin, wani ja da shokin ya yi mata bata san sanda ta faɗo daga kan gadon tana riƙe hanunta ba, nan take ta fashe da kuka tana kallo sai tin ummar da ke kwance a ƙasa.

"Innalillahi yau mu munga bala'i, ke Salamatu je ki kirawo Mamman ya zo ya ga abin da ke faruwa."
Babu ko kallabi Salamatu ta fice a guje dan zuwa kirawo Mamman.
Chapter 22 · 0% Book details