← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 26

Sashe 12

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Umma kamar ba ki ga irin hantarar da shi Mamman ɗin yake yi min ba, kina ganin yanda aka tashe ni da ruwa kuma me sanyi, hakan ai bai dace ba."
Nisawa Umma ta yi sanna ta ce.
"Duda haka Gimbiya bai dace kina musu haka ba ko ba komi su ɗin iyayene a gare ki, tun da basu rage ki da komi ba sun ɗauke ki tamkar ƴarsu ta cikinasu basu nuna maki banbanci abin da suke yi miki ma bai kamata ki riƙe shi a zuciyarki ba, idan kika yi duba da yanda kullum rana ta Allah suke taruwa wajen tashinki barci, nasan haka Allah ya yi ki da gigin barci amma wallahi haɓar Kawunki a kumbure take sakamakon harbi da kika yi mashi da ya je tashin ki a barci, ki yi haƙuri kin ji ƴata ta kaina kuma Sarauniya a fadar Sarki da yardar Allah."
Umma ta faɗa tana shafa kumatun Najla wacce jikinta yai sanyi.
"Umma bara inje in duba Kawun."
Tana faɗin hakan ta miƙe cikin takunta me jan hankali ta wuce can ƙarshen gida inda ɗakin Mamman ya ke, da siririyar sallama ta shiga sai ta hangeshi kwance yana shafa man zafi a haɓarshi har wajen ya kumbura, da hanzari ta idasa ida wajenshi tana faɗin.
"Ayya Kawunah ka yi haƙuri dan Allah kawo in shafa maka."
Ta faɗa da fuskar tausayi tare da ƙoƙarin amsar kwalbar man zafin,doke hannunta ya yi tare da juyawa ya bata baya.
Dariya ce ta kamata ganin zungureriyar ƙeyarsa da ya juya mata, cike da shaƙiyanci ta ce.
"Wai Allah Kawu kodai harda ƙeya na harbar maka, wai kaga yanda tai tsini kuwa, maba in mulmula maka."
Ta yi maganar tana fashewa da dariyar shaƙiyanci.
A mugun fusace Mamman ya juyo tare da faɗin.
"Dan Ubanki fice ki bani waje yau ga ƴar banzar yarinya, wuce ki bani waje na ce tun kafin inyi ƙasa-ƙasa da kw marar mutunci kawai."
Ya yi maganar yana zare mata ƴan ƙananun idanuwansa.
Bata fita ba sai zama da ta yi a ƙasa tana kallonshi cike da tausayi, kuma bata fasa faɗar du maganar data zo bakinta ba, dama haka take bata iya shiru idan taga abu dole sai ta tanka ba kamar shi da ta mayar kamar kakanta.

"Wai ni Uwale naga jaraba, biyo shi kika yi har nan ki idasa min shi ko.?"
Uwale ta faɗi tana dire robar ruwan zafin data ɗaura ta aje tsumman gannunta tare da dafe ƙugu sannan ta soma faɗin.
"Wallahi Najla ki fita idona in rufe, ki wani zo kin tsare min Miji da idanuwanki uwa na mage, sai faman kallonshi kike uwa ta Allah, to taso ki fita."
Ta yi maganar tana yi mata nuni da ƙofar fita.
"Haba Auntie Uwale ikon Allah, nifa sannu na zo inyi ma shi, wallahi tausayi yake bani, kalli ƙeyarshi kamar harda nan ya ji ciwon ji yanda ta zinguro kamar an leƙo da bakin kare ta taaga."
Ta yi maganar tana ƙunshe dariya dan tasan ta taɓo jarabar Uwale tun da ta taɓa mata miji.

BANANA ISLAND
A hankali ruhinsa ya soma fita daga duniyar da yake, ya kaishi duniyar da ke jiranshi ya kwanta da sunan yin barci, zaune ta ke a sanan dutse sanye da fararen tufafi masu haske da walƙiya, irin hasken da idan idanuwa suka kalla zasu jima suna kallon komi da hakan kafin su washe su koma daidai, kamar dai kullum yau ma jifarshi ta dinga yi da sassanyan murmushi me kashe gaɓɓan jiki, sai kuma ta tashi tsaye tare da saukowa daga kan dutsen ta soma tunkararshi shi ma bai dakata ba ya ci gaba da nufota da hanzari yana son cimmata, zuwansu daf da juna sai kowanen su ya tsata suka shiga kallon juna, a hankali ta ɗaga hannunta fuskarta ɗauke da murmushi me fita da haske ta nuna ma shi wani waje, wani waje wanda abu me muhimmanci ya ke ya ga abin tabbas sai ya tunkari abin da hanzari yana so ya isa waje sa, yayinda ita kuma ta ke biye da shi tana kautar da abubuwan da ke a hanyar, bai kai ga isa wajen ba wani abu ya faru, wani abu da ya zama shamaki a tsakaninsu, nan take ta ɓace daga wajen aka barshi shi kaɗai a tsugunne yana ta son tashi amma ya kasa, ga duhu ya gama baibaye wajen ta yanda baya iya ganin komi.

A zahiri
Dunƙule hannayensa ya yi da ƙarfin gaske, nan take jijiyoyin da ke aiki a cikinashi suka soma harba ciki da sauri nan take naman jikinshi ya shiga mummurɗewa ƙwanji ya bayyana a damatsansa, gadon ya soma jijjigawa da ƙarfin gaske.
Bayyanar wasu halittu marasa kyawun gani a gare shi ya saka shi saurin tashi daga durƙushen da ya ke, a hankali suka shiga kusanto shi su na watsa ma shi wani abu wanda ke ƙone jininshi nan take, sannu a hankula jikinshi ya soma saki ya durƙusa akan gwuiwoyinsa yana kakari, nan aman jini ya shiga fitowa daga bakinsa me yawan gaske, su kuma halitttun sai suka baibaye aman suna lashewa, da zarar sun lasa sai su ƙara girma nan take, gaba ɗaya ya gama galabaita har kuma lokacin ya ƙi daina aman, ga shi gaba ɗaya halittun sun girma sosai, sai ya soma ja da baya dan tsere musu, yayinda su kuma suka shiga biyo shi harsunansu a warwaje, ji ya yi ya yi karo da abu yana ɗaga kai sai ya ga wannan dutsin me fitar da haske, shi ya dafa tare da miƙewa tsaye akan diga-digansa sai faman haki ya ke, daga can sama ya tsinkayi muryarta na faɗin.
"Kai ɗin jarumin Sadauki ne, bai kamata ace rayuwarka ta ƙare a yanzu ba, hasalima ba'a fara komi ba akwai manyan abubuwanda ke jiranka, tashi ka yi faɗa da ƙarfinka ka doke kowa ka hauda kanka matakin nasara."
Daga haka sai ta sake yin sama sosai tana jefo ma shi haske me walƙiya nan take ƙarfinsa ya dawo, ya miƙe tsaye da kyau ya shiga kokowar yaƙi da mutuwar da ke tunkararshi.

A firgice ya farka daga barcin kansa na mugun sarawa, yayinda zuciyarshi ta shiga dokawa fiye da kima, jinin jikinshi ya soma tafarfasa cike da azaba me raɗaɗi, da kyar ya iya buɗe jajayen idanuwansa ya kalli inda ya ke a kwance, da sauri ya runtse su gabanshi na faɗuwa ganin jini da ya yi face-face kamar an yanka dabba, da ƙyar ya isa sauka daga kan bed ɗin yana jin yanda jiri ke kwasar shi hanyar toilet ya nufa a galabaice ya buɗe ƙofar ya shiga, ruwa ya tara ya yi soma wanke jikinshi cike da ƙarfin hali da jarumta, bayan ya gama ya ɗauro alwala ya samu ya fito da bin bango, yana gab da zuwa wajen da aka ware dan yin sallah ƙarfin shi ya ƙare nan take ya faɗi a wajen a sume kamar gawa, duniyar shiru ta kusance shi, a ƴar ƙofar da ta rage bata ƙarasa rufewa ba a idonshi ya ke hange wasu mutane na zagaye a kanshi su na wasu maganganu ba sam baya iya fahimtar yare.

BAƘIN DAJI.
Alhaji Bello da Alhaji Manga ne durƙushe a gaban wani mutum me mummunar halitta, a gabanshi wani farin abu ne ke yawo cikin hayaƙi, hannunshi marar kyawun gani ya saita a daidai wannan abin me haske, nan take sautin nishi me kama da shesheƙa ya fito, janye hannun ya yi tare da kallon su da ƙwala-ƙwalan jajayen idanuwansa masu ban tsoro.
"Kun zaɓi rayuwa tsakanin mutuwa, dole ɗaya zai riske ku ko dai ku rayu ko kuma ku mutu, a cikin rayuwar akwai tarin ƙalubale me rikitarwa ita wannan ƙungiyar da kuke a cikinta dole zasu buƙaci rayuwarku anan gaba, kuna da zaɓi guda ɗaya tak do kai ku ƙyale farin ruhi ku haƙura da komi, idan na ce komi ina nufin komi, ko kuma ku kawo ƙarshen rayuwarku da kanku, tabbas na hango mummunar mutuwa tafe a kanku, baƙin tsafi gaskiya ne shan jini ma gaskiya ne amma Me girma Dodo baya yafiya, dole ku zaɓa rayuwa ko mutuwa?."

Gaba ɗaya hantocin cikunansu suka kaɗa lokaci ɗaya, yayin da zufa ta shiga keto musu kallon juna suka yi da maɗaukakin tsoro a fuskokinsu, sannan Alhaji Manga ya ce.

"Mun zaɓi rayuwa me girma Boka."
Dariya me ban tsoro bokan ya kwashe da ita, sai da ya tsagaita sannan ya ɗaga hannunshi sama nan take hayaƙi ya bayyana ya jefa hayaƙin a jikin bango ya zama baƙin madubi sannan ya ce da su.
"Za ku rayu a ƙarƙashin ikon me girma Dodo, za ku rayu cikin daula da arziƙi, zaku ɗauka a duniya amma a bisa sharaɗi ƙwaya ɗaya, sharaɗin shi ne zasu bar farin ruhi bari na har abada, zasu sadaukar da jininku ga Dodo, zai yi yafiya ne idan kuka sadaukar da jininku Ƴaƴanku ko ƴan uwanku, ku kauda kai daga farar dukiya ku nemi baƙa ƙirin marar haske, babu ku babu addininku babu ku babu kusantar haske, rayuwarku zata daidaita ne idan kuka kasance a cikin ɗuhu."

ABUJA
Ta jikin bango Alhaji Manga da Alhaji Bello suka ɓulli gaba ɗayansu a hargitse suke sai faman haki suke, kulle kawunansu suka yi a ɗaki sannan Alhaji Manga ya fara da faɗin.

"Dodo ya ci amanar mu, anlinke mu ta baibai su na neman kawo ƙarshen rayuwarmu ba tare da mun cimma nasara ba, wai mi yasa babu nasa sai faɗuwa a kullum?."
Ya yi tambayar yana kallon Alhaji Bello.
"Tabbas Boka ya yi gaskiya, idan muna so muga daidai dole ne kyale farin haske, wannan farin hasken ba komi bane face burinmu tun na ƙuruci akan dukiyar MUBASHAR, mu gwada ɗaga ƙafa mu gani idan komi zai tafi daidai, mu fara ceto rayukanmu da ake farauta sannan mu sake shiri, daga yau a yanzu kuma anan zamu bar komi ba zamu sake waiwaya ba har sai mun gano abin da ke ɓoye, mu fara aiki da maganar boka daga yau sai mu san abin yi daga baya."
Chapter 12 · 0% Book details