← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta ya ke zuciyar shi na dokawa da wani yanayi daya soma sabawa da shi daga jiya zuwa yau, yanayin da bai taɓa sanin akwai kalarsa ba yanayin da ke yi ma shi daɗi a can ƙasan ranshi, a yanzu da ya kalli doguwar fuskarta me ƴar cika wacce ta haɗa du wasu abubuwa da zasu tabbatar da mace ta cika kyakkyawa, sai ya ji kamar yana tsoron wani abu, wani abu wanda bai tantance ko minene ba.

BAYAN AWANNI BIYAR.

Ba Jauhar kaɗai ba hatta da Suhail ya saki baki ne yana kallon mutanen da suka kewaye unguwar da ƙofar gidansu, riƙo rigar shi da Jauhar ta yi daga gefe tare da shigewa bayansa tana leƙo da kanta, sai hakan ya bashi karsashi da ƙarfin gwuiwa, sake ɗaure fuskarsa da ba ko ke iya tantance yanayin ta ba yayi sannan ya saka hannun shi ya janyo Jauhar ya soma takawa cikin takun shi irinna jaruman maza.
A gaban shi ya tsayar da ita yana nitsa idanuwanshi masu cike da kwarjini a kan fuskar farin mutumin da ke tsaye a jikin ƙerarrariyar tsadaddiyar mota yana kallon su da wani yanayi a kan fuskar sa.
A karo na farko kenan da gaban Alhaji Laminu gabata ya faɗi bayan ya haɗa ido da ɗan uwan jinsinsa namiji, sai de ba iya mazantaka ya ke hangowa tattare da Suhail ba harda gobara me ci wacce ba kowa ke iya gane hakan a tattare da shi ba sai me zurfin tunani, kallon idon shi kawai da yayi daga fitowarsu daga gida, ya tabbatar da yana ɗaya daga cikin mutane na daban.
Sakin hannunsa ya yi tare da takawa tako ɗaya biyu uku sai ya caya tsak a gaban ƴar shi, ƴar shi da jiya ya shiga cikin gagarumin tashin hankali saboda rashin ta, bai yi wata-wata ba ya yanyo hannunta zuwa gare shi, sai ta yi wani abu wanda ya sake karyar da zuciyar shi, wani abu da shi da kan shi ya buɗe mata ƙofar yin shi.
Jauhar na ganin ya soma tunkarota gabanta ya shiga dokawa, lokacin da ya daka gannu ya janyota, bata gaza ba wajen riƙe dantsen Suhail ba, tare da tirjewa ta ƙwace hannunta tana fashewa da kuka me sauti.
Hawaye ne suka gangaro daga fuskar Alhaji Laminu, yayin da zuciyar shi ta karye ganin ƴar shi na gudun shi a gaban wasu mutane, ji yayi tsanar kan shi na sake baibaye shi tare da soma danasani akan abin da ya dinga aikata ma ta cikin rufewar ido, koda dai har da laifinta amma yasan bai kamata ya aikata hakan ba.

BAYAN ƳAN MINTUNA
Kallon yan da motocin suka yi jerin gwano suka shiga ɓacewa daga layin Suhail ya yi, sai ya saki ajiyar zuciya yana jin kamar ya rabu da wani abu, wani abu me muhimmanci a tatare da shi.
Ya zaɓi ya juya ya koma gida, sai de tsayuwar wata motar a gaban shi tare da fitowa da driver ɗin Alhaji Bello ya yi tare da yi ma shi sallama, sai ya zaɓi tsaya dan jin abin da ke tafe da shi.
Kuma bayan da ya yi ma shi bayani akan Alhajinne ke nemanshi yanzu cikin gaugawa sai ya zaɓi tafiya kawai ba sai ya koma cikin gidan ba.
Kuma ko da suka isa bayan sun kwashi mintuna masu tsayi suna tafita, bai ji zai iya bin umarnin da Binta ta bashi ba, koda hakan zai zama karo na farko da zai saɓawa umarninta.

Bayan ya zauna a kan kujera ya hanne hannuwansa yana karanto tazbihi a cikin zuciyar shi bai yadda ya ɗago ba sai da ya Alhaji Bello ya fito shi da wani matashi, bayan sun gaisa a taƙaice ya soma sanar da shi dalilin kiran da yayi ma shi cikin gaugawa.

MUHASEEN
Gyara zaman shi yayi da kyau, sannan cikin izzar da ta gama bin jinin shi ya buɗe bakin shi ya soma faɗin.
"Saleem, sai nike ganin yanzu lokaci yayi da zan tsayu wajen binciko mutanen da suka zama jigon rayuwata, ina jin sauyi me girma a tattare da ni, ina so in yi amfani da wannan damar wajen yin abin da ya dace domin ban san wace kaɗɗara goben zata juyo min da ita ba." Ya yi maganar damuwa na bayyana akan kamulalliyar fuskarsa.

"Idan kuma goben ta juyo da ƙaddarar alkairi fa?."
Saleem ya yi maganar yana so ya nusar da Muhaseen daidai akan abin da yake shirin aikatawa.
"Ina saka ran hakan, sai de bani da tabbacin hakan zata faru."
Ya yi maganar muryarsa na sauyawa da wani yanayi, wani yanayi wanda ya ke riskar kansa a cikin shi a lokuta mabanbanta, nisawa ya yi tare da furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce.
"Ka shirya mana tafiya."
Yana aje maganar ya miƙe tsaye tare da soma tafiya cikin takunsa me nuna mazantaka.
Murmushi Saleem ya yi sannan shima ya tashi ya bi bayan shi.
Cikin awanni ƴan kaɗay ya gama shirya musu komi ya tsaya jiran........✍🏻

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3&amv=2
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 18
Cikar lokacin tafyar su.
Cikin abin da bai rufe awa ɗaya da ƴan kai ba Saleem ya gama sallamar du wani ma'aikaci da ke aiki a cikin gidan MUHASEEN, ba wai an sallame su hakanan kawai ba, an saleme su ne sai kuma idan ya dawo gidan suma su dawo, domin ba za'a yanke albashin su ba duk watan duniya za'a biya su.
Securities kaɗai suka rage suma dan nasu aikin bai ƙare ba har sai ya bar garin cikin aminci sannan.
A shirye tsaf cikin kayan gargajiya Saleem ya fito yana danna tsadaddiyar wayarsa, tsak ya tsaya tare da sakin baki yana kallon Muhaseen wanda ya cake cikin shiga irin ta sarauta, sai ya rikiɗe gaba ɗaya ya saura likin shigar irinta alfarma, ga wani kwarjini da ya kumalulluɓe shi da cikar zati.
Ganin fitowar Saleem ya saka shi tashi tsaye ya soma takawa cike da izza wacce ke nuni da shi ɗin jinin sarauta ne gaba da baya, haɗiyar yawu Saleem ya yi tare da bin bayan shi yana yaba kyawun da ya yi.
Har suka isa cikin mota babu wanda ya ce komi a tsakaninsu, du yanda bakin Saleem ke ƙaiƙayin ɗumi haka ya haƙura ya shanye dan baiga fuska a nan ba.
Lumshe ido Muhaseen ya yi tare da soma jero addu'o'i kariya a zuciyarsa, yayin da wani abu da sam baya son wanzuwar shi a tare da shi ya soma bin jinin jikin shi.
Ko da suka isa airport bai fito ba kamar yanda Saleem ya fita, sai da aka kammala komi har pasinger sun soma shiga sannan Saleem ya so ya sanar da shi.
Tare da Gurds ɗin sa ya jera suna kewaye da shi suna bashi kariya, sai de kuma kewayen da suka yi mashi bai hana a ranar da ƙaddara ta wanzu ta keta ta tsakaninsu ka wanzu akan shi ba, kamar de ranar da ƙaddara da fizgi idanuwansa har ya yi tozali da wacce ta hana ruhin shi nutsuwa, gaba ɗaya zuciyarshi bata tare da shi sam tana can wajen da bai san ko ina ne ba a garin Legos.
Har ya daidaita zaman shi a kan kujerar jirgi amma sam babu nutsuwa a zuciyar shi, gaba ɗaya tunanin ya cika ta taf.

KANO STATE.
Jirgin su bai yi landing ako ina ba sai a cikin airpot da ke a garin Kano ta dabo tumbin giwa, yayinda jami'ai gami da masu kakin fada irinna gidan sarauta suka cike wajen da aka tanada dan taryar fasinja.

Tun da ya diro da ƙafarsa a ƙasa ya taka ƙasar data zama mallaki a gare shi, wani abu ya shiga ratsa jinin jikin shi yana tsuma shi yayin da izza ta sake baibaye ilahirin jinin jikin shi, nan take komi na shi ya soma sauyawa da irin sauyin da yake fuskanta a du lokacin da ya dira ƙafarsa a cikin garin Kano.
Yayinda bushe-bushen algaita ya shiga ratsa ƙofofin kunnuwansa nan take jinin mulki ya soma aiki a jikinsa, har aka buɗe ma shi mota ya shiga bai koda buɗe laɓɓan bakinsa da sunan magana ba, hasalima fadawa da jami'an da aka barbaza a wajen basu bawa ƴan jaridar da suka baibaye wajen datar matsawa kusa da shi ba.
A jere motocin suka shiga tseren gudu suna barin airpot ɗin da haka har suka fice gaba ɗaya.
MASARAUTAR KANO
Lokacin da aka buɗe babbar ƙofar da aka tanada dan wucewar shi har cikin masarautar, gaba ɗaya ya gagara samun nutsuwa yayin da kan shi ya soma sarawa da tsananin ƙarfi kamar zai rabe gida biyu, ga wata kururuwa da ke ratsawa ta cikin dodon kunnen shi tana shiga har can cikin kan shi, dafe saitin zuciyar shi da wani abu me kamar mashi ya daka ya yi tare da furta.
"Hazbunallahu wani'imal wakil."
Tare da dukanin addu'o'in tsari, bai bari kowa ya gane yanayin da yake ciki ba ciki kuwa har da fadawan da suka buɗe ƙofa a gareshi cike da girmama.
Duk taku ɗaya da zai yi daidai yake da ƙaruwar azabar da ya ke ji na baibaye shi, sai de bai karaya ba ya dake gami da shanyewa ya ci gaba da takawa yana tunkarar wanzajiyar ƙaddarar da ke zaman jiran shi.

Zama ya yi akan lallausar ƙasaitaciyar kujerar da aka ƙera da ɗanyan zinare, nan take ya lumshe ido wasu zafafan hawaye na cika idanuwan shi, duk yanda yaso ya shanye amma abin ya gagara, ba komi ne ya saka shi hawaye ba illa hango fuskokin mutane uku masu matuƙar muhimmanci a gareshi da yayi, da kuma tuno lokacin da wani mutum me daraja ke zaune akan kujerar.

MUHASEENNNNNNNNNN🗣️🗣️
Wasu muryoyi suka yi tarayya wajen kiran sunan shi da ƙarfi kuma atare, sai kawai ya ɗaga kan shi sama ya saki kuka me sauti, sake damƙar hannun kujerar ya yi da iya ƴarfinsa ya shiga jijjigawa tururi gami da sautin kuka na fitowa daga bakinsa.
Chapter 21 · 0% Book details