← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗaya hawaye sun gama wanke fuskar shi lokacin da ya dawo duniyar zahiri daga tunanin da ya lula, wani ɓangare ne daga zuciyar shi ya soma faɗin.
'Idan ka bari rayuwar Jauhar ta lalace ta da saninka haƙiƙa ka ci amanar marigayiya Jawahir ina zaka kai nauyin alƙawarin da ka ɗaukar mata lokacin da take bankwana da duniya, ina zaka kai nauyin haƙƙin watsi da rayuwar marainiyar Allah Jauhar da ka yi saboda wasu abubuwa na daban?'.

A hargitse ya miƙe tsaye tare da nufar ƙofar fita hankalinsa a tashi, burin shi ɗaya shi ne yasan inda ƴar shi Jauhar ta ke, da kanshi ya ja mota ya fice daga gidan da mugun gudu, gaba ɗaya zuciyarshi a jagule ta ke, hin kan shi yake kamar wani babban wanda ya aikata gagarumin zunubi.

Rintse idanuwan shi ya yi daidai lokacin da ya ci burki a gaban ƙayataccen tsadaden Hotel wanda ya gama haɗuwa cikin tsari me ban sha'awa, ganin zai ɓatawa kan shi lokaci a banza sai kawai ya dannan hancin motar shi ya shiga ciki bayan an buɗe ma shi ƙofar, ƙarewa harabar makeken hotel ɗin kallo ya yi amma a iya ganinsa bai ga motar da aka sanar ma shi da ita Jauhar ta fita ba, hakan bai wadatar da shi ba sai da ya shiga ciki ya nemi Manager tare da nuna ma shi photon Jauhar haɗi da bayanan ta yana tambayar ko ta zo, amma aka sanar ma shi da bata taɓa zuwa ba a binciken da suka yi.
Wani abu ne me nauyi da ya danne ma shi maƙoshi ya faɗa lokaci guda yana jin wani sanyi na taso ma shi, cike da kwarin gwuiwa ya soma bibiyar manya da ƙananun hotels mafi kusa harma da na nesa amma sam bai same ta ba, sai ya sake jerantawa layinta kira amma sam ba'a ɗagawa....

SUHAIL
A gajiye ya soma buɗe idanuwansa da suka yi ma shi nauyi sosai saboda ciwon kan da ya addabe shi a cikin dare, juyawa ya yi da niyyar yin miƙa amma sai ya ji an ruƙunƙume shi, da sauri ya yunƙura tare da tashi zaune yana ƙwace kan shi, cikin ɗan hasken wayar shi daya kunna fitila ya iya ganin abin da ke faruwa da shi, tsit ya yi cikin rasa abin yi gaba ɗaya komi ya tsaya ma shi cak, a fili ya furta.
"Innanillahi ni Suhail na janyowa kaina."
Yayin da ya gaza ɗauke idon shi daga kallon ta, kwance take ta yi ɗaiɗaya a jikinsa yayinda ta ɗaura duka ƙafafuwanta a kan da hannuwanta kuma rungume da shi, ga busassun hawaye nan sun ja layi a kumatukanta, ɗan ƙaramin bakinta a taɓe kamar me shirin yin kuka.
Tinano abin da ya faru kafin su kwanta barci ya soma yi.
Babu irin dagar da ba'ayi da ita wajen ta kwanta ɗakin Binta ba amma fafur ta ƙiya duk inda Suhail ya saka ƙafa tana biye da shi, yayinda Hamza shi ma ya shiga binsu duk inda suka yi yana shishigewa Jauhar wacce ita tsoro ma yake bata.
Da ƙyar ya sama mata wajen kwanciya a waje cikin net bayan ya shimfiɗa mata katifarsa shi kuma ya haƙura ya kwanta a ƙasa akan tabarma, sam bai san sanda ta baro wajen kwanciyarta ta biyo shi nan ba sai yanzu da ya ganta kwance a kusa da shi.

Lallaɓawa ya yi ya zare jikin shi sannan ya fice ya bar mata ɗakin gaba ɗaya kan shi na kullewa tamau, sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura alwala ya tayar da sallah a tsakar gida.

Gaba ɗaya barcin kirki ya gagari Binta du bayan ƴan mintuna sai ta tashi ta leƙa ɗakin Suhail, akan idanuwanta ta ga tashi da shigar Jauhar ɗakin, kuma ta yi ƙoƙarin tsaida ita amma ko kallo bata ishe ta ba ta wuce tana ƙananun kuka kamar ƙaramar yarinya.

Sanyin asubahi daya shiga busowa ne ya ƙarawa barcinta armashi, nan ta baje ta ci gaba da barcinta hankali kwance.

"Assalamu alaiki Umma barka da safiya."
Suhail da ya tsugunna a gaban Binta ya faɗa a ladabce.
Wani irin mugun jin haushin shi ne ya mamaye ta, a maimakon ta amsa gaisuwar shi sai ta balbale shi da masifa.
"Ih dama ai ka ce min barka da safiya tun da a gaban idanuwana ka kwanta da karuwa a cikin gidannan ni kam bansan sanda ka lalace har haka ba Suhail, to Allah dai ya kyauta amma sam ba zan laminci zaman wannan yarinyar a tare da kai ba, muddin za ta zauna tare da mu sai de ta dawo nan ɗakin cikin mu ta zauna."

Kai tsaye ya amsa ta da.
"To Umma shike nan zuwa anjima zan sallame ta ta tafi gaba ɗaya dama zaman iya na yau ne kawai."
Wani haushi ne ya kama Binta dan ita dam ba haka ta so ba, ta so yarinyar ta ɗan zauna koda na kwana biyu ne ta yanda za su shiga jijinta sosai su samu na su rabon, kwana ta yi tana lissafin yanda dalolin da ta gani a cikin jakar Jauhar za su koma maƙuden kuɗaɗe idan aka canza su zuwa naira, amma dai ta ƙudurce a ranta dole ne ko yaya ta kwashi nata rabon dan haka sai ta sake ɗaure fuska sannan ta ce.

"Ni kam Suhail in tambayeka mana."
Ta yi maganar tare da gyara yanayin fuskarta zuwa yanayin da ya ke tsoron gani.
Sake sunkui da kai ya yi ƙasa cike da biyayya ya ce.
"Za ki iya tambayata a duk sanda kike so, ke kaɗai ce wacce ke da wannan matsayin a waje na, ni ɗin kamar bawa ne a gare ki."
Ya yi maganar cike da ladabi kamar yanda ya saba yi a gabanta a ko yaushe.
Sai de da ace ya san abin da zai fito daga bakinta da ya nemi alfarmar ta ɗan jinkirta zuwa wani lokaci, wani lokaci a cikin lokuttan ranar wanda zai fi zama mafi alkairi, sai de kuma wannan damar da ya bata kamar ya dasa alƙami ne akan taƙardar rubutun ƙaddarar da take jiran lokacin wanzuwarta.

Sosai abin da ta faɗa ɗin ya zo da wani sauyi me girma a cikin rayuwar Suhail, ƙawa zuci abu ne da sam babu shi a tattare da Suhail musamman akan abubuwan da suka kasance ƙawa ne na duniya, kamar kayan ƙyale-ƙyale da kuma mata, mata da ko da kuskure Suhail bai cika kallon inda suke ba, hasalima mu'amala ko wace iri ce muddon bata shafi ta kasuwanci ko neman halalinsa ba ba ya yarda ya haɗa innuwa da mata, bai san mi ya sa ba sam mata basa daga cikin tsarinsa baya kallonsu a matsayin ababen sha'awa.
Ganin wani yanki da tun tashin shi bai taɓa gani ba da ya yi a kan Jauhar a daren jiya, sai ya buɗe tunanin shi akan mata fa daban suke da maza, sannan akwai ababen sha'awa a tattare da su, da kuma ya kalli fuskarta ma tsayin mintuna biyu lokacin da Hamza ya haskata, sai ya tuna da maganar da ya sha ji wani abokin aikinsa a reataurance ke yawan faɗi cewa, kallon fuskar mace kawai na dawo da shi cikin nutsuwar shi idan ya shiga damuwa ko ɓacin rai.
Kallon fararen kyawawan idanuwanta da hotonsu ya tsaya a cikin kwanyar shi kawai da yayi a jiyan, ya buɗe tunanin shi da ya jima da kullewa akan abu ɗaya jal, ya kwana yana tunanin yanda launinsu ya koma bayan sun cika da ruwa masu sheƙi.

Maganar da Binta ta yi ma shi ce ta dawo da shi duniyar zahiri, bai samu zarafin yin magana ba ya tashi ya fice a sanyaye yana jin kalamanta na yawo a cikin kunnuwan shi.

A yanzu kuma da ya tsinci kan shi kusa da Jauhar bai san ta yanda aka yi hannun shi ya kai jikinta da sunan tada ita ba, kawai de ya san yana yin duk abin da zai ye daga yanzu har zuwa nan gaba kaɗan, dan ganin ya warware tunanin da ya dabaibaye Binta har ta faɗa ma shi abin da ta faɗa.
Lokacin da Jauhar ta buɗe idanuwanta da suka yi fayau saboda barci bata sauke su ako ina ba sai a saman fuskar Suhail, fuskar da ke sauyawa da yanayi mabanbanta a cikin lokuta ƙalilan, iya ƴan awannin da ta yi a tare da shi jiya, sun wadace ta wajen gane ainahin shi ɗin ko waye.
A yanzun kuma da ya riƙe hannunta ya matse da ƙarfi a cikin nasa, sai ta kalli hannun sannan ta kalle shi da wani yanayi, bata yi jinkiri wajen furta.
"Suhail." ba, sai da ya ɗaga idanuwan shi da suka ɗan kaɗa zuwa launin jah ya zuba a kanta sannan ta ja numfashi me ɗan tsayi taci gaba da motsa bakinta da sunan magana, yayin da idanuwanta suka shiga tsatstsafo da ruwa.
"Banada Lafiya Suhail, ina jin ciwo sosai." Ta faɗa cikin yaren da tafi ƙwarewa a kai, tana sake ɗamƙar hannunshi a cikin nata.
Maida kallonsa akan hannun su da suka cure waje ɗaya ya yi, yana ganin yanda nashi hannun ke da girma sosai a cikin nata wanda ya kasance ɗan ƙarami me kyau da sheƙi, kamar haka ya ke ganin banbanci da rashin dacewar kasantuwarsu a waje ɗaya, dan haka sai ya zaɓi ya taƙaita komi, komi ya zo ƙarshe tsakanin ta da shi, cikin dakakkiyar muryarsa me ɗan zurfi ya ce.
"Ki tashi ki shirya zan taimaka ma ki ki koma gida."

Sosai maganar komawa gida ta daki kanta, komawarta gida ba abu ne data tsara yin shi a cikin satinan ba, ko da ta fito daga gidasu ta fito ne da zummar barin gidan gaba ɗaya ba ta fito da niyyar komawa ba, ko da kuwa zata koma ba zata faru a nan kurkusa ba, amma kallonsa, da yanayin maganarsa da yayi kama da umarni ya ke bata sai ta sami kanta da amincewa bata kuma yi ƙoƙarin yi ma shi musu ba.
Chapter 20 · 0% Book details