← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 26

Sashe 24

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

WASHE GARI
A hankali ta soma buɗe idanuwanta har ta yi nasarar buɗe su gaba ɗaya ta shiga yawo da su a ɗakin tana kallon wasu baƙin abubuwa da sam bata san da su ba, kuma har mutanen gidan suka shiga tare da jiranta mata sannu da jiki, bata amsa suba sai kallon rashin sani da ta ke bin su da shi, haka suka zagaye ta suna taɓa fira a tsakaninsu ita dai sai aikin bin su da ido da take yi tana hango tarin banbancin da ke tsakanin ta da su duk kuwa data mance wacece ita a lokaci.
Ta share tsayin kwanaki bata magana, kuma rashin maganarta sosai ya damu mutanen gida, sai de kuma suna bata kulawar data dace, idan lokacin sallah yayi suyi mata alwala suna yawan ɗorata a bayi tayi buƙatunta sam basu nuna gajiyawa da ita, su bata abinci Uwale tayi mata wanka, a hankali ta soma sakin jiki da su saboda basu da matsala ko kaɗan, ta soma sakin jiki da su a sanda aka yi wani taron biki duda ba wani taro sosai aka yi ba iyaka makwota na kusa ne suka leƙo musu aka aurar da ɗaya daga cikin ƴan matan gidan me suna Huwaila, kuma har lokacin basu buƙaci sanin ko ita wacece.
Rayuwa ta tafi da nisa inda har ta shekare a gidan a sannan aka aurar da waccan ɗaya itama gida ya rage daga ita sai Uwale da kuma Mamman, suna zamansu lafiya cike da girmama juna, lokaci bayan lokaci Mamman kan kawo baƙi wasu ƴan gudun hijira wasu kuma marayu ana kawo wasu ana kwashe wasu gidan ya zama na jama'a baya ƙyashin taimakawa mutane da gumin shi, sai da suka shafe shekaru goma sha biyu a tare da ita, kuma har lokacin basu san ita ɗin wacece ba, kuma basu nuna gazawa wajen kulawa da ita ba, a kuma lokacinne Mamman ya kawo wata yarinya wcce b zata fi shekara biyu da haihuwa ba, yarinyar tana da kyau me ɗaukar hankali sai de kuma daga ganinta a cikin wahalar rayuwa ta tashi, dan gaba ɗayanta a firgice ta ke, babu wanda ta yarda da shi a gidan sai ita kaɗai kuma da buɗar bakinta sai kiranta ta yi da sunan Umma yayinda wani abu me kama da ƙaunar uwa da ɗa ta ratsa zuciyarta sannan ta gamsu kuma ta amince da suna Umma ɗari bisa ɗari, yayinda itama ta kira yarinyar da suna Najla kuma ba zata iya faɗar dalilinta na saka mata sunan ba, daga ranar Umma ta soma rainon Najla cikin aminci cike da so da shaƙuwa, sosai hankali Kawu Mamman ya sake ƙwanciya ganin ta soma walwala kuma ta saki jikinta da su.
Umma macece me tsananin ibada duk da ta mance abubuwa masu yawa da suka shafi rayuwarta ta baya, sai de bata manta komi daya danganci addini ba, kuma tun zuwan ta gidan sai ta ƙidaya fitar da ta yi daga cikinshi.

CIGABAN LABARI
Wasu zafafan hawaye ne suka silalo a kuncin Umma yayin da ta buɗe bakinta cikin karkarwar harshe ta furta.
"Na tuna ko wacece ni, na tuna asalina na tuna komi daya dangance ni, kuma ban mance zaman da nayi tare da ku ba tsayin shekaru ashirin da tara."

Kallon juna mutanen ɗakin suka yi sannan Mamman ya furta.

"To Alhamdulillahi na yi matuƙar murna da kika dawo hayyacinki kika kuma tuna ko wacece ke, bazan taɓa manta ranar da na tsince ki ba a bakin titi yashe a ƙasa cikin mawuyacin hali na ɗauko ki na kawo ki nan garin Legos sannan na haɗa ki da matata, a tsayin zaman da muka yi da ke cikin ganganci bamu taɓa cutar da ke ba, haka zalika kema baki taɓa koda kwatanta cutar da mu ba, idan babu damuwa zamu so mu ji asalin labarin ki da kuma asalin ko dan mu sada ki da danginki cikin aminci."
Mamman ya faɗa fuskar shi na washewa da annuri, har ƙasan ran shi ya ji daɗin dawowar Umma hayyacinta sosai matar ke burge shi saboda yanda bata ɗauki duniya a bakin komi ba.

Wasu hawayenne suka sake silalowa a fuskar Umma yayinda ta saka idanuwanta a cikinna Mamman tana karanto kyawun zuciyar shi, haƙiƙa ita ɗin shaida ce akan kyawawan ɗabi'un da yake da su, idan da za'a bincika a faɗin duniya ba lallai a samu masu irin zuciyarsa da yawa ba.
Goge hawayenta ta yi sannan ta ce.
"Yanzu kuwa zaka ji ko wacece ni Kawun Najla."
Kusan kowa da ke ɗakin sai da ya ɗan murmusa domin faɗar Kawun Najla da ta yi ya hasko musu irib dambarwar da suke kwasa a tsakaninsu.
Miƙe ƙafafuwanta ta yi tare da soma magana cike da nutsuwa.
Chapter 24 · 0% Book details