← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MARYAM STAR⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3&amv=2
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 16
Amma a yanzu sai ta tsinci kanta cike da jin haushin Fatima, kuma sam bata ji babu daɗi ba data sallame ta a yau.
Bayan Fatima ta tafi babu jimawa Laminu ya shigo falon yana saka hula, kallon Jawahir ya yi sannan ya ce.

"Na ji kamar muryar Fatima ko, dan Allah ki ce da ita ta haɗa min breck ina sauri ne bana so in yi latti."
Ruwa ne ya soma taruwa a cikin fararen idanuwanta lokacin da ta ji maganar da yayi, sai ta kafe shi da idanuwanta tana kallon shi bata ce komi ba, amma tabbas ta soma danasani akan barwa Fatima ragamar gidanta na ƙanƙanin lokaci da ta yi, ga shi yanzu komi yana son ya zada daga ainahin yanda ya ke, a da kulawa sosai ta ke samu daga wajen Laminu amma a yanzu bai ko damu da kallonta ba idan yana magana gaba ɗaya ya soma canzawa daga yanda ta san shi a baya, nan take ta ƙudiri niyyar kawo sauyi a gidanta.

"Yayanah."
Ta kira shi da murya me rauni ruwan hawaye na silala daga idonta, ɗago da kan shi ya yi sai kawai idon shi ya sauka a cikin nata da suka jiƙe jagab da hawaye, da sauri ya matsa kusa da ita tare da riƙe ta ya soma magana.
"Ƙanwar Yayanya ita kaɗai, mi yake damun ki, kojikinne mu tafi a sibiti yanzu, bara in ɗauko key mu tafi."
Riƙe shi ta yi da hannu ɗaya sannan ta dunƙule ɗauyan ta naushi ƙirjinshi daidai saitin da zuciyarshi ya ce da iya ƙarfinta, ya ɗan ji zafi kasancewar da ƙarfi ta naushe shi amma sai ya maze bai nuna komi ba sai ƙara riƙe ta da ya yi yana kallon ruwa hawayen da ke gudu daga fuskarta, sai jikinsa ya yi sanyi tausayin ta ya mamaye shi.

"Ƙanwar Yayanta mi ke faruwa?."

"Ban saniba ba ko ka soma gajiyawa da ni amma dai ka sani abun na ɓata raina yana min ciwo a zuciya sannan ba zan iya yi maka uzuri ba."
A rikice ya soma tambayar minene.

"Sam bana so alaƙar da kake ƙoƙarin ginawa tsakanin ka da Fatima, a kwai halayenta ba sam basu kwanta min a rai ba ni na zauna da ita na fi kowa sanin wacece ita, daga yau bana son sake ka ambaci koda harafin farko daga sunanta bana so, sannan aiyukan da take fakewa da su tana ruɗarka daga yau zan ƙoƙarta in dinga yi da kaina, idan ta kama zan nemi taimakon ƴan aiki, amma na Fatima bana so."

Wani abu me kama da ɓacin rai ne ya soma taso ma shi, dan sam bai ga dalilin ta na faɗin haka ba hasalima kamata ya yi ta yabawa Fatimar akan ɗawainiyar da ta yi da ita, ko rarrashinta bai tsaya yi ba ya shiga ciki ya ɗauki key ɗin motar shi ya fice daga gidan rai a ɓace.
Sosai Jawahir ta shiga tashin hankali domin irin hakan bai taɓa faruwa tsakanin ta da shi ba sai yanzu da Fatima ta samu damar shiga jikinta, wuni ta yi tana kukan baƙin ciki yayin da daga ƙarshe sai da ta kwanta a sibiti jinya dan ciwon ta ne ya sake tashi, kuma ko bayan da ta ji sauƙi sam bata yarda ta koma gidanta ba ta ce da Mommy Aisha gida zata koma, basu kawo komi a ransu ba aka kwashe ta aka wuce da ita can Family house, bata yi sanya ba wajen sanar da iyayen ta abin da ya faru, inda duk suka goyi bayanta kuma ransu ya sosu da abin da Laminun ya yi, amma saboda dattako irin na su sai basu faɗawa iyayensa ba suka bar maganar a tsakaninsu, sai da ta kwashe sati ɗaya cur tana hutawa a gida, yayin da ta zage wajen koyan yan da za ta sarrafa girki cikin sauƙi ba tare da ciwon ta ya tashi ba.
A cikin satin sosai Laminu ya yi kewarta gaba ɗaya ya fita a hayyacin sa kuma ya gane kuskuren da ya so tabkawa na bawa Fatima dama ta shiga rayuwar auren su.
A ranar da Jawahir ta dawo gidan ta sosai ya yi farin ciki, inda ya shiga ɗawainiya da ita, ina yaka sa ina yakan aje, farinciki ya baibaye duniyarsa tare da bata haƙiri, itama haƙurin ta bashi daga nan suka sake buɗe ƙofar dawwamamen farinciki a rayuwar auren su, basu sake bawa matsala damar da zata kusance su ba, suka ci gaba da rainon cikin su cike da ƙauna.
Sai de abin da Jawahir bata saniba shi ne, wannan aikace-aikacan da ta ke yi cike da dauriya ya soma gaigayar lafiyarta, basu ta shi gane ciwon ta ya kai matakin ƙarshe ba sai da cikin jikinta ya shiga watan haihuwa, a rana sau lumfashinta ya ɗauke fiye da goma kusan ko yaushe su na hanyar zuwa asibiti.
Allah ya ƙadarto Jawahir ba zata yi rayuwa me tsayi ba, gaba ɗaya Laminu ya rasa walwalarsa duk ya fige saboda tashin hankalin yanayin da ta ke ciki, a ranar wata juma'a ranar da EDD ɗin ta ya cika, kwance ta ke a kan gadon asibiyi yayin da hancinta ke toshe da abin shaƙar numfashi, laminu na gefe riƙe da hannayenta yana matsawa, gaba ɗaya ranar hankalin shi a tashe ya ke, zame hannun ta ta yi tare da cire abin shaƙar, sannan ta ce ya tada ita zaune, taimaka mata ya yi ta zauna tana cije bakinta da ya bushe.
Busashen murmushi ta sakar ma shi, sannan cikin sanyin murya ta ce.

"Ƴaƴana."
Sai ya miƙe daga tsayen da ya ke ya koma kusa da ita saman gadon, ya ɗaura kanta bisa kafaɗar shi yana shafa gashin kanta da ya barbaje a cukwuikwuye sannan ya ce.
"Na'am shalele Yayanta mi ke yi maki ciwo yanzu, kar ki damu Babynmu ya kusa zuwa duniya, idan namiji ne sunan Abba za mu saka ma shi, idan kuma mace ce sunan ki zan saka mata, ke ko ƴaƴa nawa za ki haifa indai mata ne to sunan ki zan tai maimaita musu."

Ɗaga kanta ta yi kaɗan ta kalle shi sannan ta koma ta sake kwanciya a kafaɗarsa tana faɗin.

"Kasan wani abu Yayana, ina ji a ajikina wannan cikin nawa ba yaro ɗaya ba ne, ƴaƴa biyu kwance a ciki, sai de ban san mi yasa idan aka yi scarning ake gani ɗaya ba na bar shi a ikon Allah kawai amma jikina ya bani cewar yara biyu zai haifa."
Sai ta kai hannu ta shafa cikin nata sannan ta ci gaba da faɗin.
"Idan biyu na haifa ka banbanta musu sunaye ɗaya ka saka mata Jauhar ɗaya kuma Jawahir, ni Jauhar shi ne zaɓina kai kuma Jawahir shi ne zaɓin ka, kaga mun raba kenan."

Dariya ya yi me ɗan sauti sannan ya ce.
"To shikenan Ƙanwar Yayanta Allah yasa ki haifa min yara biyun zan fi farin ciki da hakan.
Tari ta soma yi sai da ya ɗan tsagaita sannan ta ce.

'Dan Allah idan na yi maka wani abu wanda ya ɓata ranka ka yafe ni."
Shafa bayanta ya soma yi sannu a hankali sannan ya ce.
"Ba ki yi min kaifin komi ba Jawahir ke ɗin mace ta gari ce Allah ya albarkace ki."
Sai ta cire jikinta daga na shi tana kallon shi da idanuwanta da suka ƙara haske sosai sanan ta ce.

"Ni na san na yi maka Laifi Yayana, na yi maka laifi dana rabaka da Fatima dan na fahimci kamar ka soma son ta, ina so ko bayan bana raye ka aureta ku zauna a tare domin ina son duk abin da kake so, sannan ka roƙa min yafiyarta ita ma kace ta yafe min akan abin da na yi mata."

Bai ce komi ba illa janyo ta daya sake yi hakanan ya ji bakin shi ya yi nauyi ya kasa magana, da ace ya san abin da zai faru a ƴan mintunan da ke kusanto su da ya buɗe bakin sa ya yi mata magana koda kuwa bakin na shi da dutse aka danne shi.
"Yayanah."
Ta sake kiran shi cikin shesheƙa
Bai samu zarafin amsawa ba a wannan karon illa sake riƙe ta da ya yi, bata damu da rashin magar shi ba ta ce.

"Idan na haihu ban samu damar gani Babynah ba, ka ɗauko albon na hotunan mu ka zaɓo hoton da muka yi da Khadija ɗiyar Anty Sadiya ka bayar a haɗa shi da na abin da zan haifa, zan so idanuwana ko bayan bana nan su kalli abin da na haifa."

Ɗaukewar fahimta ce ta samu Laminu a wannan yanayin, gaba ɗaya maganganun da ta ke faɗa yana jin ta kuma ya kwashe su tsaf a cikin kan shi ya adana su, amma bazai tantance ma'anarsu a lokacin ba, haka ya kasa kunne yana sauraren duk abubuwan da take faɗa ma shi kafin daga bisani ciwonta ya tashi gadan-gadan, nan ya tashi a rikice ya kira....✍🏻

MARYAM STAR⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3&amv=2
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

✊ 𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈🤝
https://chat.whatsapp.com/Ek6DPlIu4ad0QgTfrn3rab?s=cl&p=a&ilr=4&amv=2

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 17
Doctors babu ɓata lokaci suka taru a kanta suka shiga ƙoƙarin ceto rayuwarta, ga kuma naƙuda data taso mata gadan-gadan kuma ba zata iya haihuwa da kanta ba dan tana cikin wani hali, nemo Laminu aka yi tare da yi ma shi bayanin suna so za su yi mata aiki cikin gaugawa, jiki na rawa ya saka hannu tare da biyan kuɗin komi, shi dai fatan shi ɗaya ta samu lafita.

CIGABAN LABARI
Chapter 19 · 0% Book details