← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sunan Gimbiya kuma Saraunita Aishatu, ni ƴa ce ga Sarkin Katsina Kabir Umar, na yi aure a masarautar garin Kano inda na auri aminin mahaifina me martaba Sarkin Kano me suna Muhusin Salis wanda a lokacin shi ke akaragar mulki, ba ni bace babba a cikin matansa ba amma ni ce na zama tauraruwa a cikin matansa duda kasancewata yarinya a cikinsu.
Mai martaba Muhusin Salis adalin Sarki ne wanda al'umarsa ke farinciki da mulkinsa kasancewarsa me adalci ga al'umma, Allah ya jarabce shi da rashin samun haihuwa tun daga kan matansa na aure har ƙwarƙwarorin da aka ba shi babu wacce ta taɓa haihuwa, hakan na matuƙar damun shi, shi yasa lokaci bayan lokaci yake shiryawa ya zo har Katsina wajen mahaifina domin ya raka shi zuwa duba kafiyarsa da suke zuwa a sirrance ba tare da sanin kowa ba, sai de abin da ke ɗaure musu kai bai wuce yanda duk inda suka je ake tabbatar musu da yana da cikakkiyar kafiyar da zai haihu lokacine kawai bai yi ba.
Babban dalilin sarki Muhusin na neman haihuwa ido rufe bai wuce yanda yake gudun subucewar mulki daga gidan su ba, domin dai ta tabbata muddin bai da kwai a duniya to sarauta zata juya gidanau waziri me ci a lokacin, ba dan wata manufa yake gudun juyawar mulkin ba sai dan tsoron irin baƙin mulkin zaluncin da za'a gabatar muddin ahalin Waziri suka amshi sarautar.
Ko ba dan hawa karagar mulki ba ya kasance mutum me tsananin son ƴaƴa, yara ba ɗaya daga cikin abubuwan da ke bala'in burge shi, yana aje sarautar shi a gefe idan yaga yara ya zauna har ya yi wasa da su cike da soyayya.
Matar Sarki Muhsin ta farko ita ce Sarauniya Zainaba itama babbar ƴar sarkin Gwanbe ce ita ce mace ta farko da Sarki Muhusin ya soma aura tun iyayensa na da rayuwa, ita ɗin macece me ji da mulki haɗe da izza, sam bata ɗaukar kuskure ko ya yake tana da zafi sosai sannan bata yafiya, itama ta jima tana yawon neman haihuwa domin ta zama ita ce mace ɗaya da zata rayu a gidan Sarki sannan ta cika shi da tarin zuri'ar ta yanda mulki zai dawwama a tsatsonta, sai de kuma tana tata Allah na tashi, bayan kwashe shekaru biyu ko ɓatan wata bata taɓa yi ba hakan ya saka a lokacin Marigayi tsohon Sarki ya sake nemawa Me martaba auren ɗiyar wani abokin shi, shima Sarki ne a lokacin ya nada ƴaƴa mata su biyar, da Marigayi me martaba ya nemi iri a wajensa sai ya bada ƴar shi me suna Sarauniya Husna.
Sarauniya Husna ita ce ta zama mace ta biyu a wajen Sarki Muhusin, inda tun tana amarya bayan tarewarta suka soma gaba da junansu ita da Gimbiya Zainaba, inda ko waccensu ke ganin tana sama da ƴar uwarta, sam basa ga maciji kullum cikin jifar junansu suke da shairi.
Bayan kwashe shekara biyu da aure Sarauniya Husna itama shiru shine fa aka sake aurawa Me martaba aure da Aishatu.
Duk da kasancewar bana son shi a lokacin umarnin mahaifina na bi amma bai hana na yi ma shi biyaya bakin iyawata ba, a tsarina ni sam bana son sarauta dan na san shairinta ya fi alkairinta yawa hakan ya saka lokacin da ina karatu na haɗu da wani saurayi muka fara soyayya, koda maganar aurena ta taso haƙuri kawai na bashi domin bazan iya tsallake maganar mahaifina ba, dukda na shiga damuwa a farko amma da Fulani mahaifiyata ta ja ni a jiki tare da nasiha me ratsa jiki sai na fawwalawa Allah lamurana na rungumi ƙaddarata.
Ban jima da tarewa a gidan Sarkin Kano Muhusin Salis ba na gama kanainaye zuciyar shi, yayin da na yi baya-baya da matan shi da sauran munafukai irinna gidan sarauta, na maida hankalina wajen kulawa da mijina tare da soma renon soyayyar shi da ta soma ɗarsuwa a cikin zuciyata.
In taice muku labari cikin ƙanƙanin lokaci na zama Giwar Sarki kuma shalelen shi, domin kuwa na amsa sunana Sarauniya kuma ƴar sarki bayan watanni kaɗan da soma zuwa turaka Allah ya azurta ni da samun juna biyu, juna biyun daya zama makulin buɗe ƙofofin ƙaddarar da suka jima a kulle suna jiran ranar buɗewarsu.
Ba sai na ɓata baki wajen sanar da ku irin murna da farincikin da marsarauta ta yi a lokacin ba, yayin da aka shiga yin sadaka gami da manyan kyaututtuka tare da ƴantar da bayi, gaba ɗaya Me martaba da sauran muƙarrabansa masoya na kusa dana nesa duk sai da suka nuna farinciki da jin daɗinsu, yayinda kuma aka haskawa masu mugun nufi da mubafukai fitila suka gane zahirin abin da ke wakana, ba sai na tsaya fayyace muku irin ƙiyayyar da sauran matan sarki suke nuna min a fili ba, ɓullowar wannan cikin kuma ya sake haska musu wata hanya wacce basu hanga ba daga farko, nan suka tattare komi suka aje suka juyo kai na.
Kwatsam a rana tsaka ciwo ya turnuƙe ni bayan cikina ya soma ƙwaru, ciwon da aka gaza gane gaba bare bayan sa, ganin zan rasa rayuwata Me martaba ya bada umarnin a cire cikin tun da shine matsalar, dukda ya shiga matsananciyar damuwa amma kuma yayi farinciki a ƙalla ya ji ance ya matar shi ta taɓa samun ciki amma ya lalace.
Sai da nasha doguwar jinya har sai da aka koma da ni can masarautar gida domin samun lafiya, na ɗauki tsayin lokaci sannan na dawo daidai daga jinya, nan Me martaba sarkin Katsina ya sake bani addu'o'in tsari sannan ya ƙara min hadimai mata masu gaskiya da amana, cikin mutunci aka dawo da ni masarautar Kano inda acanma Me martaba Sarki ya saka aka shirya gagarumar walima domin tarbata, anyi budiri sosai an ci an sha anyi wasanin gargajiya da al'adun hausa abi sai wanda ya gani sosai aka nishaɗantu.
Yayin da hakan ya ƙara ruruta wutar tsana gami da ƙiyayyata me muni a idanuwan sauran matan Me martaba, musamman Gimbiya Zainaba wacce ko haɗuwa na yi da ita a turaka ko fadar cikin gida gabana ke yankewa yana faɗuwa, kallon kykakyawar fuskarta kawai na jefa ni a ɗimuwa bare kuma aje ga batun ta yi min magana cikin kissar da ta saba amfani da ita, nan da nan nike fita a hayyacina tsoro ya cika duniyata.

A ranar da aka raka ni turaka bayan dawowata a ranar na tantance irin girman da soyayya ta tayi a zuciyar Me martaba, domin dai ni kaina sai da na fayyace irin yanda nike matuƙar ƙaunarsa, daga ranar muka sake curewa muka zama abu ɗaya muka shiga farantawa junanmu duk sanda kwanana ya zagayo, har ƴan fada sai da suka tantance sanda nike da Me gida, domin kuwa ya dinga shige da fice kenan ko zaman kirki baya yi a fada, yakan leƙa cikin gida sau babu adadi.
Yayin da a gefe ƴan gulma da munafukai suka shaidawa sauran Matan Sarki abin da ke faruwa, nan take suka sake ɗaura lamara suka yi shirin yaƙin sunƙuru a kaina.
Bayan shekara ɗaya da lalacewar cikina Allah ya sake azurta ni da samun wani cikin, sai de a lokacin ban bar wata alama ko ɗaya da zata iya bayyana cikin jikina ba, hatta da Me martaba sai da na ɓoyewa ina da juna biyu, duk kuwa da yanda yake liƙe da ni, hatta da turaka sai da na nemi alfarma akan yayi min lamani ina fama da lalura, amma ban amice ya sanarda kowa ba dan sirrina ne, da yake yana da fahimta sosai kuma yana bawa komi da ya dangace ni muhimmanci, sai bai sake ɗaga maganar ba, duk kuwa da yana cutuwa da rashina, daga baya har kwarkwarori aka tanada ma shi waɗanda zasu taimakawa sauran matan shi ɗaukar ɗawainiyar shi, yayin da Gimbiya Zainaba da Sarauniya Husna suka shiga yi min dariyar wai amfanina ya ƙare an gama ɗaukina yanzu a turaka gashi nan yanzu har da ƙwarƙwara Me martaba yake da, ko kaɗan ban damu ba dan nasan ina da dalilina na yin hakan.

Kwatsam a waya rana ina kulle a can cikin ƙuryar ɗakina bayan na bada umarnin kar wacce ta koda leƙo ƙofar ɗakin bare kuma ta shiga, ko minene a jira ni ina zuwa, cire alkyabar jikina na yi tare da ɗage ƙatuwar rigata data taimaka sosai wajen ɓoye girman da cikina ya soma yi, ɗaura hannuwa na na yi duka biyu akan cikina tare da lumshe ido ina shafar cikin, farinciki gami da ɗaukin ranar da zan haife shi na baibaye ni domin ina matuƙar son naga na haihu da Me martaba, na shagala sosai da abin da nike yi ban ankare ba kuma bansan sanda wani ya shigo ɗakin ba abin da na sani na riga da na kulle ko ina kuma na rufe tagogi, amma sai na tsinci muryar mutum a kuda da ni, a kiɗeme na juya ina firfito da duka girman idanuwana cike da razani.
Kallon cikin kwayar idon shi da tayi jazur na yi tare da soma ja baya ina girgiza kai kuka na kwace min me.
Bina ya soma yi duk inda na yi da haka har muka dangane da jikin bango sai kawai na rintse idanuwa ina fashewa da kuka, durƙusawa ya yi akan gwuiwoyinsa tare da daka hannayensa ya tallabe cikin, sai kawai shima ya fashe da kukan muka dinga yi a tare babu me rarrashin ɗan uwansa, ni ina kuka akan hukunci da zai yi min na ɓoye ma shi wannan al'amari me girma yayin da shi kuma ya ke kukan farinciki ganin wani cikin a jikina.
Bayan mun tsagaita da kukanne ya tallabe ni a hankali ya zaunar abakin gado sannan cikin laushin murya ya ce da ni.
"Tauraruwata tun yaushe kike ɓoye min wannan lamarin, watansa nawa yanzu.?
Ya faɗa idon shi a kaina yana jiran ya ji abin da za faɗa.
Chapter 25 · 0% Book details