← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cak komi ya tsaya ma wacce aka kira da gabata, ɗif ta ji zafin marin ya ɗauke, yayinda zafin kalaman wanda ya ke amsa sunan Uba a gareta ya shiga ƙone zuciyarta, nan take zafafan hawaye suka shiga silala daga cikin rinannun idanuwanta, sai kawai ta ɗaga kanta ta kalli innuwar mutum da ke tsaye a jikin bene, a saman busasun laɓɓanta da ƙaramun sauti ta furta.
"Jiya da yau kinci nasara a kaina, ki jira zuwan gobe."
Sannan ta fice a guje kuka me ƙarfi na kubce ma ta, kai tsaye wajen ajiyar motocin gidan ta nufa tana gujin kuka, jikin wa ta farar ƙal ɗin MBW ta nufa ta tsaya, ganin hakan ya saka me kula da motoci bata key yana tambayarta a kira driver, amma sam bata amsa shi ba ta wani fizgi key ɗin tare da buɗe motar ta shiga, ta jata da mugun gudu.
Tana tuƙi tana kuka sosai, tana kukan kasancewarta a wannan rayuwar me cike da ƙunci, sai da tai nisa sosai sanna taci burki a wani ƙaton fili ta fito daga motar tare da durƙusawa ta ɗibi ƙasar wajen da hannunta, da mugun ƙarfi ta furta kalmar.
"MUHASEEEEEEEEEEEEEEEEEEN." Sai da wajen ya amsa da ƙarfin amon sautinta, kafin ƙaƙƙarfarn kuka wanda yafi na baya ya sake kubce ma ta, kuka ta ke kashirɓan kamar me son zare zanta, nan take farar motarta tai jazur idanuwanta suka rini, yayinta jikinta ya shiga jijjigawa tsabar yanda ta ke kukan daga ƙasan ranta.

LEGOS NIGERIA
BANANA ISLAND.
Duniyar mafarki.
*Sai yaushe zaka zo gare ni, ka wadatani da abin da Ummana ke buri a rayuwa, ka sauya rayuwata ta koma kamar ta kowa, na gaji sosai da wannan wahalar da nike yi, ina so in huta koda na ƙanƙanin lokacine.*
Hasken da ke zagaye da shi ya ke faɗa ma shi cikin murya me cike da sanyi gami da gajiyawa, kafin ya samu zarafin yin wa ta magana ya jiyo muryarta ta kwalla masa kira da ƙarfi, a hankali hasken ya shiga disashewa, yayinda sautin muryarta da ke ambayar sunanshi cikin neman agaji ya karaɗe wajen.

Wani irin juyi ya yi a ƙoƙarinsa na gano inda sautin ya ke, sai de kuma ba tare da saninshi ba a zahiri yayi juyi, kuma yakai ƙarshen makeken royal bed ɗin da yake kwance akai, bai ankare ba sai jinsa yayi a ƙasa timmmm, ya faɗo, lamarin da ya sakashi wartsakewa daga baccin.
Yamutse kyakkyawar farar fuskarshi da saman hancinsa yai jazur yayi, yana jin raɗaɗi na ratsa ƙeyarshi datasha ƙasa, ga wani nauyi da kanshi yayi, wanda sam bai da alaƙa da faɗuwa, yakai tsayin mintuna biyar yana ƙoƙarin tashi, kafin daga bisani ya dafa gadon ya miƙe tsaye, jiri na kwasarsa, ga bacci sosai da yake ji, sai de kuma yasan barcinshi ya rigada ya ƙare, dama dakyar ya samu barcin ya ɗaukeshi bayan ya lodawa kansa magunguna masu ƙarfi, a gaban ƙofar bathroom ya tsaya dare da danna wasu madannai sannan ƙofar ta buɗe tana faɗin.
"Barka Muhaseen, na'ura ta tantanceka, zaka iya shiga kayi abin da kake so."
Tallabe kanshi ya yi jin sautin na'urar na ƙara saka mashi ciwo da nauyin kai.

HAƘƘIN MALLAKA DA RUBUTU

MARYAM STAR ⭐⭐✍🏻

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3&amv=2
🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 3
A ƙalla ya ɗauki tsayin mintuna arba'in sannan ya fito daga bathroom, jikinshi na ɗigar ruwa da alama wanka ya yi, kyakkyawan fari ƙal ɗin towel ya ɗauka ya shiga goge ruwan jikinshi, sannan ya jona handrayer ya soma tsane gashin kanshi daya jiƙe da ruwa, bayan ya gama ya buɗe clothset inda jerin underwere suke, ya janyo farar best dare da farin boxer, sai kuma inda jallabiyoyi suke nan ma fara ƙar ya ɗauko haskenta har kashe ido ya ke, ya zira a gurguje, turare kuwa ya fesa aƙalla saman da kaloli biyar masu daɗin ƙamshi, sannan ya nufi wajen da aka tanada domin yin sallah, yana kallon agogo da ke nuni da ƙarfen biyu da mintuna ashirin na dare, a nutse ya kabbara sallah shi kanshi bazai iya ƙirga adadin sallolin daya jeranta ba, bai tsagaita ba sai da ya ji ansoma kiraye-kirayen sallar asubahi, sannan ya zauna yayi tazbihi me tsawo bayan ya gama jeranta addu'o'i, sai ya tashi daga wajen still yana tazbihi ya nufi ƙofar fita, agogon da ke dokawa du lokacin sallah ce ta karaɗe ko ina na gidan da tsuwarta, kan kace kobo tuni ma'aikata sun soma ɓulɓulowa wasu sun wartsake wasu na murzar idanu alama bacci, haka suka jera zuwa masallaci, sai da suka cika moyoci kusan goma tab sannan suka tafi, a can masallacin ma haka suka hau jerin yin alwala yayinda shi me gayya me aikin ya shiga ciki abinsa.
Basu suka fito daga massalacin ba sai da rana ta soma fitowa, wani fari dogon matashi ne ya jera kusa da Muhaseen yana gaida shi, sai de be amsa ba yaci gaba da takawa ciƙe da ƙasaitarsa.
"Am sarki nace ba, ko za canza maka wani maganinne tun da na lura waɗannan kamar basu amsheka ba, ga idanuwanka nan sun sauya kala kuma sun ɗan kumbura, sai a haƙura da fitar kawai yau."
Bai amsa shi ba haka yaci gaba da takawa ba kuma dan bai ji abin da ya faɗa ɗin ba, sai dan magana na sahun farko cikin abubuwanda ke mashi wahala.
Ɗaya bayan ɗaya tarin ma'aikatan da ke aiki a gidan suka soma shigowa su na kwasar gaisuwa, sai de ko motsi baya yi bare ya amsasu har su gama su wuce wasu suma su zo suma su kwashi tasu gaisuwar.

Dy abin da ke wakana yana ji, sai de sam baya cikin hayyacinsa a baɗini, a zahirine kawai suke ganin a zaune amma a baɗini ciwo da damuwa da rashin samun barci ga kuma tarin mafarkan da ke addabar rayuwarsa ne suka haɗu suka damalmala rayuwarsa, ya kwashi a ƙalla awa ɗaya a zaune kafin ya miƙe cikin shanye yanayinsa ya nufi dining room inda aka tanadar masa lafiyayyen breack, zama ya yi a kujerar dinning ɗin tare da kafe flask ɗin da aka tanadar masa da hot tea, kallon flask ɗin kawai da ya yi ya sanar da farin matashin da ke biye da shi abin da ya ke buƙata, sai da ya wanke hannunsa a sink sannan ya ɗauki tsaftataccen glass tea cup ya tsiyaya ma shi tea ɗin daketa tashin ƙamshi, cike da izza ya amshi cup ɗin tare da yin basmala ya soma sha da zafin, yana jin yanda zafin ke zarcewa cikin cikinshi kai tsaye yayinda zufa ta soma tsattsafo ma shi, hanjin cikinsa da suka daɗe da ƙullewa suka soma warware kansu su na amsar ruwan zafin da jiƙa su, tas ya shanye tea ɗin sannan ya janyo wani kyakkyawan fari ƙal ɗin bowl wanda ke ɗauke da lafiyayyar fan cake wacce aka yane sammanta da fresh honey, guda ɗaya ya ɗauka tare da kaiwa bakinsa ya soma ci, iya ita kaɗai ya ci ya tasho daga wajen yana ɗan dafe kansa da ke sarawa ga ciwo da ya ke yi masa sosai.
Da kallon tausayi matashin ya bishi har sai da ya ƙulewa ganinsa sannan ya zauna ya shiga karyawa, yana yi yana dudduba aiyukan da zasu yi a yau da kuma time a wa ta loptop da ke hannunsa, sai da yai seteling komi sannan ya tashi a wajen ya nufi wa ya hanyar daban, cikin a bin da bai wuce mintuna goma ba ya fito tsaf dashi cikin suit a gaggauce ya nufi ƙofar da Muhaseen ya shiga, ya sona danna lambobin sirri a gaggauce yana yi yana duba lokaci, ga mamakinsa lokacin da ya shiga bayan ya ambayi izini, sai ya iske Muhaseen a gaban wawakeken miro yana feshe turaru, jikinsa sanye da arnayen suit wanda suka dace da kalar skin ɗinshi yayi kyau sosai du kuwa da babu fara'a bare annuri a fuskarshi, lokacin da ya juyo bayan ya gama abin da yake ya kafe matashin da mayun idanuwansa masu cike da kwarjini, sai natashin ya daburce jin kaifin idanuwan ogannashi na yawo a kanshi, jiki a sanyaye kanshi har lokacin na ƙasa ya soma faɗin.
Chapter 3 · 0% Book details