← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 26

Sashe 4

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Am, dama nayi zaton zamu je ni da Fawas mu gabatar da meeting ɗin duba da nayi kamar baka jin daɗi, daga can zanje na sako ma ka wasu magungunan tun da na lura waɗannan sam basa ai....."
Bai idasa ba ya ji ƙamshinsa na shiga hancinsa da alamar ya ƙaraso gabanshi kenan, a karona farko daya buɗi baki ya ce.
"Babu buƙata Saleem."
Daga hakan kuma ya fice yabar wanda ya kira da Saleem ɗin tsaye a wajen yana sauke numfarfashi, sai kuma ya yi hanzarin biyo bayan Muhaseen ɗin wanda ke taku cike da izza da nuna mazantaka, idan kaga yanda ya ke tafiya sam bazaka ɗauka a kwai wani rauni dake baibaye da shi ba, saboda baya nuna gazawarshi a fili yana yin komi a yanda ya dace duda tarin abubuwam da ke baibaye da rayuwarsa.
Bai tsaya ba sai a gaban jibgegiyar mota fara sol sabuwar ƙira wacce iya hasashen mutum bazai iya ƙiyarta kuɗinta ba, kasancewar itace ta farko da aka fara ƙerawa a shekarar.
Buɗe ma shi motar aka yi ya shiga ya kame a baya, yayinda aka buɗewa Saleem gaba kusa da driver ya zauna shima, sai sauran securitys ɗinsu suma suka shirga sauran motocin, cikin tari suka fice daga danƙareren gidan sannan suka soma kwasar gudu a hanya kamar dan su kaɗai aka yi hanyar.
Basu wani jimaba suka sauka a wawakeken company nan ma babu wani jinkiri suka kutsa kai can ciki har baki ƙofar shiga cikin compony wajen elevator, du wanda ya hango shigowarsa zai aje abin da yake yi ne ya nufo wajen ya kwashi gaisuwa a wajen Sarki Muhaseen, duda ko sau ɗaya bai taɓa amsawa ba hasalima ko kallon masu gaisheshin baya yi.
A saman ƙofar shiga elevator aka rubuta da manyan baƙi.
WELLCOME TO STAR GOLD AND JEWELRY INTARNATIONAL LIMITED, cikin salo me burgewa, STAR GOLD & JEWELRY INTERNATIONAL LTD na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sayar da gwal da kayan ado a ƙasar. Kamfanin yana da hedikwata mai hawa goma sha biyar, tare da rassan shaguna a manyan birane.
A kowace safiya, ma'aikata kan hallara kafin buɗe aiki. Jami'an tsaro sukan fara duba harabar kamfanin da na'urorin tsaro. Bayan haka, Manajan Kamfani ya kan gudanar da taƙaitaccen taro domin jin rahoton sassa daban-daban.
Sashen kimanta gwal shi ne ke karɓar sabbin kayayyaki domin tabbatar da ingancinsu. Bayan an tantance su, sai a mika su ga ma'ajin kaya wanda zai rubuta su a kundin kamfani kafin a kai su babban shago.
A cikin shago kuwa, ma'aikatan tallace-tallace suna karɓar kwastomomi cikin girmamawa, suna nuna musu nau'ikan gwal, zobba, sarƙoƙi, 'yan kunne da sauran kayan ado. Idan an kammala ciniki, mai karɓar kuɗi zai tabbatar da biyan kuɗi sannan ya bayar da rasit.
A ƙarshen rana, kowane sashe yana gabatar da rahotonsa ga Babban Manaja. Daga nan sai a tattara bayanan tallace-tallace, kuɗaɗen shiga, da kayan da suka rage domin a miƙa rahoto ga Shugaban Kamfani.
Shugaban Kamfani kuwa yana zama a babban ofishinsa da ke saman bene, inda yake karɓar rahotanni, tattaunawa da manyan abokan hulɗa, da kuma yanke hukuncin da ya shafi ci gaban kamfanin.
MUHASEEN, shine C.E.O a company yayinda Saleem shike riƙe da miƙaminVice president, yana kula da ayyukan company idan C.E.O bayanan ko wani uzurin gaugawa ya taso.
Fawas shine GENERAL MANAGER, shima yana bada himma sosai a kan aikinsa sai de baikai Saleem ƙwazo ba, domin kuwa Saleem ya sadaukar da duka lokacinsa ne wa oga kuma amininshi ɗaya tilo a duniya, wanda ya zame masa uwa kuma uba wato MUHASEEN, yana jajircewa su gabatar da aiki a tare komi wuyarsa ko, kuma shine mutu guda ɗaya tilo daya taɓa sanin matsalar Muhaseen, saboda yarda da amincin da ke a tsakaninsu.

Bayan angama gabatarwa Muhaseen du wani tsari da kuma abubuwan da ke wakana a kamfani nan suka ɗunguma aka shiga meeting, meeting ɗin da ya ɗaukesu tsayin lokaci ba'a gama ba, koda suka fito lokaci yaja sosai har ƙarfe ɗaya ta yi, kai tsaye Masallaci suka wuce ɗomin yin sallah, Saleem yaso su tsaya wajen cin abinci amma Muhaseen bai bada fuskaba hakanan ya haƙura suka wuce ɗayan kamfanin da aketa jiransu, kamfanin sarrafa ƙarafene inda suka yi baƙin turawa da ke son sarin kaya a wajensu, kuma a matse suke da kayan hakan ya saka tun safe suke zaman jira, a canma sun sha wahala sosai, basu bar wajen ba sai da suka tabbatar da komi ya tafi daidai sannan, haka suka dinga ziyarta shaguna da kamfanoni sam basu samu hutu ba, gabaki ɗayansu sun jigata ga yunwa dake saƙalar hanjin Saleem dole Muhaseen ya tsayarda su a wajen cin abinci gudun karya shiga haƙƙinsu ya saka akayi oder me yawa aka yiwa sauran drivers da securitys takeaway sannan suka ƙarasa gida, ko bayan da suka isa gidan wanka kawai ya tsaya yi yaci gaba da aikin cike-ciken takardu da sanya hannu, bayan ya gama dana gabansa ya bawa Saleem yayi arangen shi kuka yaci gaba da aiki a loptop, yayinda shima Saleem ya soma nashi aikin na lissafi da tantance kuɗaɗen da suka fita a yau, yasan ba lallai yagama aikin a yauba amma sanin cewa idan bai yi ba Muhaseen ɗin zai yi ƙoƙarin yi da kanshi ya saka ya bada himma, yana yi yana yage baki yana hamma, amma ahaka ya dage yacigaba da yin aiki.

Gaba ɗaya kanshi ya cunkushe, ga nauyi gami da sarawar da yake ma shi, ga rashin barci da bayayi a kwanakin, sannan ga tunanin mafarkan da a kullum ya kada kafaɗarsa a ƙasa ya ke yinsu, ga kuma ayyuka da suka sha kanshi, yana so ya rage wasu abubuwan amma babu hali, dole komi sai shi zai yi, wasu abubuwan basa buƙatar wakilci.
Ɗaga kaifafan idanuwansa yayi tare da miƙa kallonsa wajen Saleem da barci ya kwashe shi yana ai, wani ɗan guntun abu me kama da murmushi ne ya so ya bayyana a kan fuskarshi, sai kuma ya shanye abinsa, murya acan ƙasa ya ce.
"Guy."
Can cikin barci Saleem ya ji muryar Muhaseen a sukwane ya wartsake yana hamma, sannan ya ce.
"Wai nikam ba zamuci komi ba yau, har yanzu da saura space a cikina wallahi."
Ya yi maganar yana marairaice fuska dan Muhaseen ɗin ya taisaya ma shi.
Lumshe ido yayi sou biyu yana buɗewa, hakan ya ankarar da Saleem abin da oga kuma abokinsa ke nufi sai ya tashi da sauri yana miƙa yabi hanyar dinning room.
Sai da ya gama harhaɗa du abin da zasu buƙata sannan ya saka ƴan aiki suka ɗauko zuwa cikin shahararen falon, a gaban Muhaseen ya yi umarnin su aje, da kanshi ya soma haɗa ma shi sababben wato Hot tea, tare da abinci ɗan kaɗan yana fatan Muhaseen ɗin ya ci koda ƙanƙani ne.
A yangance Muhaseen ɗin ke kurɓar tea ɗin, yanajin yanda gaɓɓan jikinsa ke amsawa da matsananciyar gajiya, ga kwanyarsa da abubuwa sukai ma ta yawa tana buƙatar hutu, sai de kuma yasan ba lallaine yauma ya samu barci ba, da ace ana sabo da rashin barci da tuni ya saba, dan kuwa kullum abin nashi ƙara gaba ya ke.
"Guy, ina so ka bincika min wani maganin, ina son hutu sosai."
Iya maganar da yayiwa Saleem kenan yana miƙewa a dake ya shige ciki, murmushin cinnasara Saleem ɗin ya yi dama ya daɗe yana jiran wannan damar, da hanzari ya gama loda abincin sannan ya miƙe tare da kiran Doctor ya sanar ma shi a kawo sababbin magungunan da suka yi magana akai.
Sanin da yayi sam baya iya shan magani hakanan kai tsaye ya saka ya samu fresh milk ya jiƙa maganin a ciki, a maimakon yabi umarnin Doctor sai yao san ranshi ya jiƙa kusan guda biyar alhalin biyu aka ce yasha,
Sanda ya kai ma shi maganin ya taras har yayo wanka, ya tsaya a gaban miro sanye da ƙaramin towel da bai wuce cinyoyinsa ba, yayinda baiwar ƙwanji da cikakkiyar ƙirarshi ta sadaukan jaruman maza ta bayyana a fili, saurin kawar da kai Saleem ya yi yana jin kwarjinin MUhaseen na baibayeshi a sanda suka haɗa ido ta jikin miro.......✍🏻
KU BIYO NI SAU DA ƘAFA DAN JIN YANDA ZATA KAYA.

MARYAM STAR⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS💪🤝✊.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DczAiFp992p78VNoV6tcMo?s=sw&p=a&mlu=3&amv=2

🌹𝙈𝙐𝙃𝘼𝙎𝙀𝙀𝙉🌹
(𝐿𝑎𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑧𝑢𝑐𝑖𝑦𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖, 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑚𝑒 𝑐𝑖𝑘𝑒 𝑑𝑎 𝑡𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑘𝑎𝑙𝑢𝑏𝑎𝑙𝑒😔.)

𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀 𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐.

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍,𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪

🤝𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙃𝙄𝘿𝙊𝙍𝙄𝘼 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝙏𝙀𝘼𝙈✊

𝙋𝘼𝙄𝘿 𝘽𝙊𝙆
𝙎𝙀𝘼𝙎𝙊𝙉 𝙊𝙉𝙀
بسم الله الرحمن الرحيم.

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 4.
Juyowa ya yi gaba ɗaya tare da fuskantar Saleem, taku uku ya yi ya isa gabanshi, amsar cup ɗin yayi bayan yayi Basmala ya ɗaga ya zuba rabi a bakinsa, sai ya hama haɓar Saleem ya matse bakinshi bayan ya ɗage kanshi sama ya zuje ma shi sauran a cikin baki.
Azabar riƙo ta saka Saleem haɗewa da ƙarfi, sai da Muhaseen ya tabbatar da maganin ya wuce sannan ya dake shi, fuskarshi na washewa kamar zai yi murmushi, nan take jikin Saleem ya soma saki, tsayuwa ta gagareshi da kyar ya isa gaban gado kawai dai ya gaɗi ragwajam a ƙasa barci me nauyi yayi gaba da shi.
A nitse Muhaseen ya gama shirinsa, ya sake yo brush sannan ya dawo ya gyarawa Saleem da ke barci haiƙan kwanciya shima ya kwanta bayan ya yi addu'a, tare da fatan ya samu barci domin kuwa gaba ɗaya jikinsa amsawa ya ke da tsananin gajiya da buƙatar hutu, cikin ikon Allah bai wani jimaba sosai barcin ya ɗaukeshi, sai de bame nauyi ba kamar Saleem daya mance duniyar da yake.
Chapter 4 · 0% Book details