← Book details Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 26

Sashe 18

Muhaseen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧15
Amsa sallamar da ta yi Jawahir ta yi tare da miƙewa ta nufi in da ta ke ta taryo ta da maɗaukakin farinciki.
Wani dunƙulallen abu ne ya tokare zuciyar Fateema da ta yi tozali da fuskar Jawahir, amma a zahiri sai ta ƙaƙalo murmushi me kau ta ɗora a fuskarta, akan sofa suka zauna kafin Jawahir ta saka masu aiki ciki gaban Fateema da kayan maƙwalashe, lemo ta tsiyaya a cikin glass cuf sannan ta kalli Jawahir tana faɗin.
"Matsala ta da gidanki rashin abinci, yanzu dan Allah ni da na dawo daga wajen aiki mi kayan marmari da kayan fulawa za su yi min, gaskiya nafi son abinci me ɗan nauyi."
Ta faɗa tare da kai cup ɗin a baki ta shanye lemon tas.
Damuwa ce ta bayyana sosai a fuskar Jawahir sannan ta ce.
"To Fatima ya zanyi, wallahi nima abin na damuna sosai musamman Yayana da sai bayan ya dawo aiki ya ke ɗora girkin bawan Allah ga gajiyar aiki ga kuma ta gida, shiyasa fa nike aje fruit da snacks saboda baƙi, a kwanakin baya Doctor ya ɗora ni akan wani magani ma fara amfani da shi yanzu haka kuma ina fatan samun sauyi.
Ɗan jimmm Fatima ta yi kamar ba zata ce komi ba sai kuma ta ƙaƙalo guntur murmushi me kama da yaƙe ta ɗaura akan fuskarta sannan ta ce.
"Kai ƙawata yaushe kika canza magani ban saniba, to Allah yasa ayi sa'a dan ke cutar ta ki anrasa gane kanta, cuta tun jarintaka har girman ki, Allah dai ya yaye ma ki wannan cuta."
Ta yi maganar tana jin zafi na taso mata a ƙasan zuciyarta.
Kallon ta Jawahir ta yi cikin wani yanayi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa dan sam bata ji daɗin maganar Fatimar ba, ita kanta tana fatan a ce yau ga shi ta samu lafiya ta warke daga cuta, amma ba zata ja da ikon Allah ba dole ta amshi ƙaddarar da ya ƙaddara mata tun gabanin ta shaƙi iskar duniya.
Suna a wannan yanayin suka ji ne ƙarar shigowar motar Laminu da sauri Jawahir ta tashi farinciki na bayyana akan fuskarta, sai da ta kalli jikin wawakeken madubin da ke manne a bangon falon ta tabbatar da babu wani abu na kwalliyar ta da ya ɓaci sannan ta soma takawa cikin taku me burgewa har ta fice daga falon.
Saura kaɗan Fatima ya ƙware ganin abin da Jawahir ɗin ta yi, da sauri itama ta tashi ta shiga duduba kanta tare da goge baki har da turare ya sake fusawa sannan ta gyara kayan gabanta ta sauya salon zaman ta.
Hannun shi rike da nata suka shigo yana yi mata magana, da alamar magana me daɗi yake faɗa mata domin kuwa sai faman zabga murmushi take yi jerarun haƙoranta a waje.
Sam bai ankare da Fatima ba suka nufi hanyar shiga bedroom ɗin su sai jin sautin muryarta cike da kwarkwasa suka yi tana faɗin.
"Yayanmu barka da dawowa."
Kallo Jawahir ya yi yanayin fuskar shi na sauya da, sai ta ware ma shi kyawawan idanuwanta sannan ta ce.
"Oh sorry please Yayanah ni kaɗai Fatima ce ta kawo mana ziyara yanzu ba jimawa ɗokin dawowarka ne ya hana ni sanar da kai koda a waya ne."
Wani murmushin ya kuma yi sannan ya saka hannu ya ja kumatunta tare da janta suka shige ciki bai ko bi takan gaisuwar da Fatimar ke yi ma shi ba.
Iya shaƙa Fatima ta shaƙa da abin da Laminu ya yi mata, da farko ta ƙuduri niyyar ba zata tafi ba har sai sun gama sun fito, amma da ta ga sun kwashi awanni har biyu babu su babu alamar su har kiran wayar Jawahir ta yi dan ta tunasar da ita tana nan tana jiran ta amma sai ta ji ƙarar wayar a kusa da ita, sai ranta ya ƙara ɓaci ta suri jakarta ta fice a fusace.
Jawahir ba su suka fito ba sai bayan sallar Magrib lokacin ana daf da yin isha'i masallaci Laminu ya wuce ita kuma ta soma tattare kayan da Fatima ta bar mata a wajen tana jin babu daɗi da basu yi sallama ba ta tafi, bayan ta kwashe komi ta sake kiran me yi mata aiki ta sake share falon tare da bata umarnin ta kunna mata turaren wuta, sai ta shige ciki tare da kulle du wata kafa da hayaƙin turaren zai iya kai mata, a kan bed ta zauna tare da ɗaukar wayarta zata kira mamanta Aisha sai ta taras da tarin kira rututu ga saƙwanin nan daga Fatima, a fili ta furta.
"Allah sarki Fatima ban kyauta maki ba kin zo min ziyara kin tafi ba mu yi bankwana ba."
Sai ta dannawa lambar kira ba'a ɗaga ba sai da ta kusa katsewa, da sallama ta fara sannan ta ɗora da faɗin.
"Allah sarki Fatima ki yi haƙuri ban san tafiyarki ba, fatan kin sauka gida lafiya."
Ɗirkekiyar harara Fatima ta dallarawa wayar sannan ta ce.
"Uhumm Jawahir kenan wai ace har ni zan zo gidanki dan mijin ki ya dawo ki nemi wulaƙanta ni, ba komi ni na janyowa kaina gobe ma rana ce sai idan kin ƙara gani na."
Nan Jawahir ta zage tana ta bata haƙuri har ta samu ta ɗan sauko sannan suka yi sallama ta kashe wayar, tana ajewa Laminu na shiga ɗaki, sai da ya isa wajenta ya saka hannayensa ya rungume ta a jikinsa sannan ya ce.

"Kamar wani abu ya taɓa min ke bayan na fita."
Sassanyan kallo ta watsa ma shi tana jin yanda zazzafar soyayyar shi ke ratsa zuciyarta, kwantawa ta yi akan ƙirjinsa cikin sauyin sauti ta ce.
"Wallahi Fateema ce na ɓatawa rai, kana gab da dawowa da zo muna tsaka da fira ka dawo to shi ne ban koma munyi sallama da ita ba na manta, shi ne fa ta ɗauki fushi me tsanani da ni yanzu na kira ta a waya na bata haƙuri."
Ɗaure fuska ya yi sannan ya ce.
"Wallahi sam bana son wannan ƙawar taki sam bata yi min ba zubin munafukai ne da ita."
A lokacin murmushi kawai Jawahir ta yi bata ce komi ba.

Bayan kwana biyu.
Haka Fateema ta maida gidan Jawahir wajen zuwanta, a madadin su dinga yin fira irin ta ƙawate sai dai ta dinga kawo maganganu marasa tushe, har sai da takai ga Jawahir sam bata son firar Fatima, gashi yanzu ciwonta na yawan tashi a kai a kai, sam ba daɗin jikinta take ji ba wani bi sai de ta ce Laminu ya sauke ta gida idan zai tafi aiki idan ya dawo ya biya ya ɗauke ta.

Bayan watanni biyar da aurensu Allah ya azurta su da samun ƙaruwa, bayan Jawahir ta yi doguwar jinya a asibiti a binciken da likitoci suka yi suka gano tana ɗauke da ƙaramin ciki, sosai ƴan uwa da abokan arziƙi suka yi farinciki da hakan, a ɓangaren Laminu kuma sai sambarka abu biyu ya haɗe ma shi ga farincikin samun ƙaruwa ga kuma damuwar ciwonta da yanzu ya tsananta sosai, ko magana ta yi me ɗan tsawo sai ta yi shesheƙa ko kuma numfashinta ya ɗauke.
Da wannan damar Fatima ta yi amfani wajen shiga jikin Jawahir ɗin sosai, har sai da ta cimma abin da ta jima tana son cimmawa amma bata samu dama ba tun lokacin da ta fara haɗuwa da Jawahir ɗin, hasalima ta gida dangantaka da ita ne dan ta samu wannan abin, sai de ko sau ɗaya bata taɓa samun damar hakan ba sai a yanzu, a yanzun da ta shiga jikin ta sosai da sunan tana tausayin halin da take ciki.

Gaba ɗaya a rayuwar Laminu waje ɗaya ne Jawahir ta gaza a gare shi, yana matuƙar son macen da ta iya girki, girke me suna girki ba muna girki ba sai kuma ya yi rashin sa'a ita sam bata girki, da yake yana matuƙar son ta sai hakan sam bai dame shi ba ya ke zaunawa ya kashe lokacinsa ya girka musu kafiyayen abinci me rai da mitsi, yanzu da aka dawo da Jawahir gida Fatima ke zuwa dubiya akai-akai dai ya yazama tana zagewa ta girka lafiyayyen abinci, yana ci yana santi daga haka ne ya soma sake mata fuska ganin irin bautar da take yi wa matar shi babu gajiyawa, yayinda ita kuma Jawahir zuwan Fateemar ya soma takura mata dan bata da damar sakewa da mijinta kamar baya, ko magana zasu yu basu da sirri haka zata zaune sai ta ji abin da za su tattauna, bama wannan ba sai suna maganar da ta shafe su sai kawai ta dinga tsoma musu baki, abin na ƙona ran Jawahir sosai yayin da shi kuma Laminu bai ga aibun hakan ba.

Yanda Fateema ke nan-nan da cikin Jawahir ya saka Laminu ya sake mata, har yakan mai da ita gida idan dare yayi mata, shi sam bai ɗauka hakan zai iya janyo wani abu ba.

Da farko Jawahir ta tsaya ne dan ta ga iya gudun ruwan Fateema amma da ta ga abin nata bana ƙare ba ne sai ta tare ta wata rana da safe da ta zo gidan, lokacin Laminu ya shiga wanka.

Bayan sun gaisa Jawahir ta haɗe fuska abin da bata taɓa yi ba sannan ta ce.
"Yauwa Fateema dama ina so ince da ke na gode sosai da ɗawainiya haƙiƙa kin ciki ƙawa ta ƙwarai a wajena, tun da dai na samu sauƙi yanzu daga yau ba sai kin sake zuwa ba kya dinga bari sai bayan kwana biyu sai ki dinga zuwa muna gaisawa."
Wani kallo Fateema ta jefa mata a fakaice irinna baki isa ba, amma a fili sai cewa ta yi.
"A,a ma sha Allah ki ce sauƙi ya samu to shikenan dama wallahi kamar kin san al'amurrana duk sun tsaya cak saboda jinyar ki kwata-kwanta ban da nutsuwa yanzu haka zance da nike yi maki wajen aiki, aiki na can ya tarar min sosai amma dai tun da kin dakatar da ni da kanki ai kinga sai in koma inci gaba da aiyukana yanzu."
Jin haushin mutane sam ba ɗabi'ar Jawahir ba ce hasalima an shaide ta da rashin son hayaniya ko rikici.....✍🏻
Chapter 18 · 0% Book details