← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 26

Sashe 9

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaunefa ko ka mantane....

Tashi pls karka makara"
Janyota taji yayi ya rungume bayan ya matsar da pillow din dake jikinsa ada,
"Dan Allah yau ba ranar fitina bace katashi kayi wanka kashirya 10 fa zaku tafi..."
"Karfe nawa yanzu?" Yatambayeta bayan yadan bude lumsasshun idanunshi yana kallonta,
"Karfe 8 takusa fa...."
"To ai dasauran lokaci baby love...har zaki bani breakfast..."
"Karka damu gashi nan nashirya maka dama...

Tashi kayi wanka dan saurayi..."
Murmushi tasashi yi bai shirya ba,
"Idanma zolayata kikeyi babu wani abu...."
"A'a ni na isa?

Nidai katashi pls"
"Wai dan Allah meyasa kike min rowane kwana biyun nan?"
Murmushi tayi ta shafi kansa,
"Yaufa nafara hutu....

Garama kasani...."
"Karya kikeyi.....ke ai bakya mensuration idan kina shayarwa ko kin zata namanta?"
"Naji dan Allah tashi...

Kaji"
"Wai jiya ni kika yiwa wayo ko?

Akomai dai sai kin nuna min kin rigani zuwa duniya...."
Dariya tayi ta tashi zaune tana fadin,
"Nidai bari naje nayi wanka....

Ina son yin hoto da ango kafin yafita kowa yaganshi"
Sake rungumota yayi,
"Let's do it together....

Please"
Makale kafada tayi tana kokarin zamewa,
"No kaje kayi kai daya..."
"Ni ban yarda ba, tare zamuyi"
Babu yadda ta iya haka dole ta biye masa suka shiga wankan tare wankan da ya daukesu tsawon lokaci dakyar ta samu ta banbarosu suka fito kowannensu daure da towel,
"Ina zuwa...

Please ka shirya kafin nadawo"
Tafada tana saka babban hijab, fita tayi daga dakin ta nufi nata bedroom din,zama tayi ta shirya kanta cikin wani tsadadden leshi dark purple dinkin riga da skirt Wanda yayi mutukar amsarta, kwalliya tayi sosai tasha powder da janbaki harda jagira, kafa dauri tayi tasha turare tafita tana gyara sarkar Indian gold din da tasaka a wuyanta wacce take faffada domin ta cika mata wuya,dakin yara tashiga nan ta iske iyallo nata drama dasu hanfa wai ita sanyi takeji tagaji da wannan sanyin dake cikin dakin kamar ana zuba kankara shiyasa duk tabi ta kudunduna abargo sukuma su maryam suna shirya su Mimi da awwab ita Mariya tana bathroom tana yiwa Muhammad da hanfa wanka, gaida iyallo tayi suka gaisa iyallo nata fadan wannan sanyin da suke sakawa yara,
"Woww Anty wallahi kinyi kyau..." Maryam tafada tana dariya, jin haka yasa Mariya fitowa daga bathroom domin ganewa idonta,
"Woww Anty kamar ma kece amaryar....." Inji Mariya,
"Nagode maza ku gama shiryawa Ku fito Ku karya ga abinci can nashirya..."
Juyawa tayi ta kalli iyallo,
"Hajiya iyallo bari akawo miki naki nan ko?"
"A'a bar abincin nan yanzu sai zuwa anjima zan fito"
"To shikenan bari naje na sallami oga"
Juyawa tayi tafita takoma dakin fahad wanda ke zaune gefen gado yana sanye da blue din shadda sai kyalli takeyi yana ta kokarin balle links din hannun rigarshi, ganinta yasashi barin abinda yakeyi yazuba mata ido yana kallonta gaskiya yau tayi wata ta daban,
"Baby......wow....

Kinyi kyau"
Zama tayi gefenshi tana kallonshi,
"Bae kayi kyau kaima....

Yaushe akayi wannan askin ban ganiba sai yau?"
Wuyanta yakaiwa kiss yana cewa,
"Abinda nayishi tun jiya da yamma shine baki ganiba sai yanzu....

Gaskiya kin tafi dayawa..."
"Exactly....

And you look handsome this morning what's the secret?

Ohhh namanta ashefa ango kake...."
Dariya yayi yana mai mika mata hannunshi dan ta balle masa links din dake jiki,
"Zan ramane bari nadawo baby...

You will cry over and over and over again..."
Dariya tayi itama ta dauki agogonshi mai tsada na azurfa ta daura masa sannan ta dauko turare ta fesheshi dashi har saida ya kwace saboda kar ya hawar masa kai, hula ta saka masa wacce take kalar kayanshi amma akwai ratsin Fari ajiki,
"Wow....

Best ango eva....

Kayi kyau wallahi, duk wanda yaganka yau zaiyi expecting cewa yaune ranar aurenka nafarko, indeed you look very young & adorable...let me snap u...."
Kin yarda yayi ganin ta dauko expensive phone dinta, sai hannu yake sakawa yana karewa har yasamu nasarar janta jikinshi nan ta daddaukesu tare daga nan ta zauna ta hada musu breakfast tare suka karya gwanin ban sha'awa ayau dai babu wanda zai kalli fuskarta yace wai kishiya ake shirin auro mata saboda yadda tasake dashi sosai sunata zuba soyayyarsu, saida suka gama ciyar da juna sannan suka fita tamkar amarya da ango, afalo sukayi arba da su Mariya da yaransu suna karyawa cikin tsadaddiyar shiga ta alfarma matan kayansu iri daya haka suma mazan nasu irin daya su biyu, daukar mimi fahad yayi yajasu Muhammad da hanfa jikinsa yasake jan bilkisu gefen damanshi su maryama sunata haskasu ahaka salim yashigo ya samesu nan yafara tsokanar bilkisu yana cewa,
"Wai hajjaju bilkisu ke ko dan kishin nan ma bakya yi bare ki bata rai?

Gaskiya fa kamata yayi ki tubure kice baki yarda ba...."
Dariya tayi tace,
"A'a Abba salim ko kaima kana cikin yan bakin cikin zamu samu karuwa ne?

Ai duk macen da take ita daya babu kishiya to bata sanin level din son da ake yimata....."
Dariya salim yayi yana gyara zaman hularsa shi dai fahad jinsu yakeyi baice komai ba,bin bayansu tayi domin rakiya tana yiwa fahad addu'ar Allah yatsare ya kiyaye hanya,
"Wai....

Lallai hajjaju harda su rakiya?

Auren kishiyarki fa zamu je mu dauro"
"Ohh Abba salim, adawo dai lafiya"
Daga haka takoma ciki tana dariya shikuma fahad ya daki salim akafada yana cewa,
"Fuck you malam kana neman ka ballo min ruwa...

Kabarni da rigima"
Tunda suka tafi take hidimar gabanta domin ta shirya walima inda zata gayyato malamar addini wacce zata tunatar da yan uwa mata,
Gidan fal yake da mutane musamman ma danginta da na fahad duk matan yayunshi na gidan amma banda Anty juwairiyya matar ya sunusi, duk wannan uban cikowar bata dauke mata hankali ta manta da fahad ba ana gama girki ta dibar masa nasa takai dakinsa sannan ta kirashi domin taga miss calls dinsa har guda uku, tana daf da katsewa taji ya daga,
"Soul mate...

Ina kika shiga ne haka?"
Murmushi tayi ta zauna gefen gadonshi,
"Sorry bae wallahi hayaniyace tayi yawa..."
"Sannu da kokari Allah yayi miki albarka nima yanzu zan taho gareki..."
"Allah yadawo dakai lafiya..."
"Amin I love you..."
"I love u too..." Tafada tana kissing din wayar sannan takatse tafita ta nufi bedroom dinta, wata kwalliyar tasake sha cikin golden colour din material doguwar riga taci dauri mai kamada gwaggwaro sannan tafita nan gida ya gauraye da guda kowa sai tayata murna yakeyi sakamakon ga motar da fahad yasiya mata nan kowa yana gani,anan compound din gidan aka gudanar da walima kamar yadda tashirya inda malama Hajara ta gabatar da lecture mai taken kishiya abokiyar rayuwa, kowacce mace dake wurin taji dadin wannan lecture din saboda malama hajara tabayar da wasu sirrika na mussaman,
saida aka kusa tashi daga walimar sannan anty Juwairiyya tazo tanata tabe taben baki gamida harare harare sai kallon bilkisu take tayi wacce ke cikin kyakkyawar shiga itada yaranta cikeda walwala, itafa saima yau ta taba zuwa gidan ashe haka fahad ya tara kudi?

Ashe haka ya kashewa bilkisu da yaranta kudi?

Hararar bilkisu tayi aranta tana cewa,
"Munafuka jibi yadda taketa fara'a tana walwala kamar ba kishiya ake yimataba...

Ni banma taba ganin matar da tashirya walima dan ana yimata kishiyaba sai ita....

Kai gaskiya ban yarda da itaba duk yadda akayi akwai wani mugun nufi aranta"
Maganar Anty Kubra faccalarta ne yadawo da ita hayyacinta,
"Gaskiya bilkisu ta burgeni...

Kiga yadda tasaki ranta shiyasa shima fahad din yaketa daga darajarta a idon duniya..

Kalli dalleliyar motar da yasiyo mata can fa..."
Ai tunda Anty juwairiyya taga wannan motar hankalinta yasake tashi nan ta sulale takoma gefe tana kiran layin husnah dan yazama dole tashafawa husnah wannan labarin tunda duminsa dan idan tazo itama ta san irin takunta sannan karta yarda da bilkisu dan duk abinda takeyi yanzu makircine da kaidi irin na mata.....
*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
*_Ummi Shatu_*
[1/21, 5:08 AM] Nawarty
: 7***Ahankali take bude idanuwanta wadanda suka yimata nauyi sannan shima kanta yayi mata wani irin dummmm babu dadi, dakin take bi da kallo tana son tunano shin meya kawota nan?

Idonta ne yakai kan zeetah wacce ke kwance da waya a hannunta daga ita sai half vest da gajeren wando iya cinya kanta yasha kitson attachment wanda yake tuli guda, fashewa tayi da kuka sakamakon tuno abunda ke damunta,
Daidai lokacin azima tashigo ita da Lady hannunsu sakale cikin na juna,
"Beauty kin tashi.....

Sannu" lady tafada tana zama gefen ta tare da kamo hannunta,
"Pls kidaina kuka mana bahijja....

Kiyi hakuri, tashi kiyi wanka kici abinci gashi"
Har lokacin bata bar kuka ba sakamakon tuno rayuwarta da ko ita wacece amma yau wai itace cikin wannan halin,
"Kitashi kiyi wanka kici abinci...." Lady tace da ita tana dagota, bata da zabin da yawuce tabi abinda suka fada amma kanta wani irin azababben ciwo yake yimata kamar zai rabe gida biyu,
Da taimakon azima taje tayi wanka tafito domin jikinta babu wani karfin kirki har yanzu sakamakon abinda tasha,
Kayan sawa suka fito mata dashi acikin kayansu sannan suka ajiye mata take away wanda suka shigo mata dashi, muryar lady taji tana cewa,
"Wannan nakine beauty...

Ke na kawowa"
Bata ce uffanba ta dauki kayan tasaka sai lokacin idonta yakai kan agogo karfe 9 da wasu mintuna,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un...."
Tafada tana dafe goshinta sakamakon tunowar da tayi cewa batayi sallar magrib ba jiya haka ta ishah, gashi yau ta makara sallar asubah har karfe 9,
"Ki daure kici abincin nan beauty...

Pls"
Kallon lady tayi sannan ta dauki hijabinta,
"Bari nayi salla tukunna...."
"Is ok"
Tashi tayi tai salla sannan suka bata abincin takarba ta bude, soyayyen dankaline da kwai sai yar sos agefe sannan ga lemo wanda taga lady ta watsa wasu kananan kwayoyi aciki sama da guda biyar sannan ta tsiyaya tasha ta ajiye mata rabi agabanta,
"Beauty kisha saboda kisamu ki manta da damuwarki...
Chapter 9 · 0% Book details