Sashe 14
Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Abu nagaba shine kai sagir zan tafi da bahijja zamuje taci gaba da zama awurina har lokacin da Allah zai kawo mata miji in aurar da ita...."
Gyaran murya hajiyan tarauni tayi tagoge kwallar idonta sannan tace,
"Alhaji da nice nayi niyyar tafiya da ita wurina inci gaba da riketa har in aurar da ita tunda bani da ya mace..."
Dagowa yaya sagir yayi ya kallesu fuskarsa araunane,
"Abba....
Hajiya dan Allah kuyi hakuri bawai naki baku bahijja bane da wata manufa a'a kawai bana sone tayi nisa dani ayanzu..
Kuyi hakuri kubar min ita ta zauna tare dani saboda zanfi jin dadin hakan...
Dan Allah kubar min ita, ita kadai gareni amatsayin yar uwa..."
Daga hajiya har abban bebeji jijjiga kai sukayi amatsayin nuna gamsuwarsu nan Abba yayi musu sallama yatafi bayan ya ajiye rafar yan dubu dubu su kuwa su umma tareda su aka hada kayan gidan tsaf aka kai wanda za akai gidan yaya sagir wani kuma aka barshi anan sannan aka rufe gidan suka rankaya gidan yaya sagir.
Aranar da yamma su hajiyan tarauni suma suka tafi basu sake kwana ba amma sunbar baba fatsima domin tarinka dan debe musu kewa, hakan kuwa akayi domin baba fatsima macece mai barkwanci da raha shiyasa duk inda taje za aji dadin zama da ita su dinma ta debe musu kewa sosai har na tsawon sati daya lokacin kwanan umma 14 da komawa ga mahaliccinta ranar itama baba fatsima takoma gidanta domin mijinta yayi musu kara sosai da yabarta tazo har tsawon wannan kwanaki, bayan tafiyar baba fatsima itama anty marakisiyya na kokarin tayi iya bakin kokarinta wurin kwantar musu da hankali gaba dayansu, sai bayan tafiyar baba fatsima bahijja tafara samun fuska wurin yaya sagir dan yanzu ya fara amsa gaisuwarta kuma yana dan yin hira da ita, idan yajita shiru adaki yakan kirata suyi hira domin baya son tashiga damuwa har tasamu wani ciwon asanadin radadin rasa mahaifiyarsu.
Yanzu abinda yafi damunta shine ta yadda zata samu daya daga cikin abubuwan da ta saba sha tasha musamman irin syrups din da Faruk ke kawo mata gashi bata da waya dan tun kafin rasuwar umma yaya sagir ya karbe wayar yarabata da ita, so take ta rinka dan shan wani abu saboda ta rage yawan damuwar dake damunta ahalin yanzu,
Tunda tatashi yau bata fitoba tana daki tukunkune kan gado tana tunanin hanyar da zata bi wurin kiran Faruk tunda ta haddace number dinshi akanta ita dama ba kasafai take saving numbers ba wannan dabi'arta ce dan sunsha fada da tsohon saurayinta akan batayi saven number dinshiba, ita so take takoma school dan tuni wasu ma har sun fara exams amma ita gata agida,
Dabara ce tafado mata nan tatashi tafita taga marakisiyya bata falo tana kitchen tana yan aikace aikacenta amma ga wayarta nan akan kujera afalo, wayar ta dauka tanufi bedroom din da yake matsayin nata ahalin yanzu bata tsaya ananba tawuce cikin toilet tasaka number din faruk tayita kira amma bai daga ba daga karshe sai text massage ta tura masa cewar itace sai gashi kuwa yakira,
"Hello guy...
Nicefa yanzu banida wayane fa wannan ma ta sister inlaw dinace na dauka bata saniba..."
"Ayya baby ai inata nemanki but ban sameki ba what's happening?
Meya faru da wayarki?
Kina ina yanzu?
Zan siyo miki waya sai inkawo miki ki fada min irin wacce kikeso?"
"Faruk kabari kawai sai nadawo school yanzu nafa
da maka ina gida kuma mamana ce mafa ta rasu...."
"Ohh my God....
What a great lost....
Allah yajikanta...
Babu damuwa idan kin shigo zamu jone"
Sallama tayi masa ta kashe wayar sannan tagoge number dinsa tafita falo tayi sa'a kuwa dan har lokacin marakisiyya na kitchen tana aikinta.
Daren ranar tayi niyyar yiwa yaya sagir maganar komawarta school amma atsorace take dashi dan gabanta inbanda faduwa babu abinda yakeyi, koda tayi masa maganar bayan yadawo da daddare shiru yayi yana nazari kawai wasiyyar umma yake tunawa nabar mishi amanar bahijja da tayi sannan tace yayi mata duk abinda takeso domin shine gatanta bayan babu ranta dan Allah kar yabarta tayi maraicin rashinsu,
"Shikenan naji kije zanyi shawara...."
Tunda taji yafadi haka tagane akwai alamun nasara washe gari da yafita ya iyo mata siyayya kaca kaca harda sabuwar waya amma yakarya sim dinta na da yace taje ta siyi wani Nasiha yayi mata sosai akan shaye shaye da lesbian din da take kokarin cusa kanta, washe gari da kanshi ya dauketa yakaita bauchi yamayar da ita makaranta,bayan sunje yakira azima amma tace itama tatafi gida kaninta ne yarasu, saida yasake ja mata kunne sannan yatafi yabarta, yana tafiya bayan takai kayanta hostel takira Faruk tace masa tadawo mintuna kadan sai gashi yashigo da sabuwar mota dal dan ko lamba ma babu ba adaurawa motar ba da sabuwar waya babba kirar kamfanin HTC daukarta yayi suka fita daga makarantar.
Abangaren abdurrahman da shamsiyya kuwa sai sam barka zamansu domin tun lokacin da yace mata yafasa aure zamansu yake dadi kullum cikin lallabata yakeyi saboda gudun kar yabata mata rai ciwonta ya tsananta kamar yadda dr bala yafada masa,
Tana zaune cikin kwanciyar hankali da yaranta guda biyar Musaddiq da muhibba sai shuraim da yusra da amra yar auta, su Kansu yaran yanzu sun san ana zaman lafiya agidansu dan shamsiyya rayuwarta takeyi gaba gadi sai abinda takeso take yi,
Yau da wuri ta tashi tayiwa abbansu muhibba karin kumallo domin tafiya zaiyi zaije garin abuja, kafin tagama hadawa har yayi wanka ya shirya yafito cikin suit bakake wadanda suka amsheshi sosai, sai kamshin turaren chronic men yakeyi, a dining yasameta tana karasa shirya kayan karyawar kiss yayi mata a kumatu kafin yaja kujera ya zauna yana murmushi jin dadi,
"Kin san fa 7 jirginmu zai tashi shiyasa naketa wannan gaggawar..."
"Ai baka makara ba..." Tafada tana murmushi,
Agurguje shikam yakarya yaje yaga yaranshi wadanda ke daki sunata bacci ya shafa kansu yafita tarakashi daga nan tadawo gida taci gaba da al'amuranta, aranar kanwarta badiyya tazo domin tayata zama itace kanwarta ta biyu kuma ahalin yanzu tana shekarar karshe a jami'ar sa'adatu rimi inda take yin NCE dinta a bangaren Islamic,
Suna zaune suna hira shamsiyya ta kalleta tana jan tsaki,
"Wallahi wasu matan ma shashashu ne inbanda shashanci tayaya mace dan mijinki zai kara aure ki wani saki jiki kina farin ciki harda tayashi murna a status?
Kalli fa abinda sokuwar labour dinnan tarubuta...."
Ta karasa maganar tana mikawa badiyya wayar tata, nan takarba tana dubawa kyakkyawar mata tagani da wani handsome din mijinta harda yaransu tare dasu sunyi masifar kyau akasan hoton ta rubuta _I congratulate you on your wedding and wish you half of the most beautiful things in the world.
The other half I
ll leave for me._
Murmushi badiyya tayi aranta tana fadin woww, afili kuwa tace,
"Anty shamsiyya wannan din kawarki ce?
Gaskiya sun burgeni"
"Class mate dinace...
Tare mukayi secondary da ita, wai dan tsabar dorawa kai wahala shine harda wani hada walima....
Mtswww nonsense...."
Dariya badiyya tayi bata kai ga yin wata maganar ba su muhibba suka shigo aguje daga makota ganin badiyya duk suka rufu akanta suka rungumeta suna murnar ganinta,
Daki guda shamsiyya ta ware ma badiyya kamar yadda tasaba duk lokacin da daya daga cikin kannenta sukazo bata hadasu da yara dakinsu daban take basu,
Duk aikace aikacen gidan badiyyan ce keyi tayiwa yara wanka da sauran hidindimu, kwananta biyar agidan abdurrahman yadawo daga abuja,
Kullum ita dai badiyya tana daki idan tafito to aiki zatayi kasancewar acikin dakin da takema akwai kayan kallo, kwananta goma sha biyu agidan da wata safiyar
alhamis shamsiyya na bedroom dinta tana sakawa amrah pampers bayan ta yimata wanka, ganin badiyya tayi tashigo idanuwanta jajur kuma shabe shabe da hawaye tana rikeda jakar kayanta,
"Anty natafi gida...." Shine abinda badiyya tafada kuma bata ko jira amsar shamsiyya ba tayi waje abinta da sauri duk da cewa shamsiyya nata kwalla mata kira amma bata tsaya ba,hankalinta ne taji yatashi saboda atunaninta agidane wani abu yafaru shiyasa tayi azamar bin bayanta amma kafin ta karasa tuni badiyya har tafice daga gidan duk da tanata faman kwala mata kira bata saurareta ba tayi tafiyarta akan idonta ta tare napep tashiga har lokacin tanata faman share kwallar dake zuba a idanuwanta, cikin sauri takoma cikin gida taje ta dauki wayarta takira Abasiyya wato kanwarta dake bi mata,
"Hello anty..."
Cikin tashin hankali tace,
"Abasiyya meke faruwa ne agidan?
Waye ya mutu?"
"Wai wanne gidan?
Mutuwa kuma?"
"Dan Allah ki sanar dani gaskiya, gidanmu mana"
"Mu nan lafiya lau muke wallahi, mafarki kikayine?"
"A'a badiyya ce naga tafita tana kuka inata kiranta amma taki saurarata"
"Rabu da ita da shirmenta kila haukan natane ya motsa...
Ni wallahi kinma katse min baccina da nakeyi haka kawai"
"Shikenan sai kije kiyi tayi nidai tunda lafiya kalau shikenan"
Daga haka ta katse wayar ta ajiye taci gaba da abinda takeyi wato shirya amrah tana ta taba baki aranta tana tunanin to me tayiwa badiyya da ta tafi da duku dukun nan kuma tana kuka?