← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 26

Sashe 16

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka taci gaba da zama agida har tsawon sati uku babu yan kwanaki cikin wannan hali badiyya tafara wani matsanancin zazzabi da amai mai ban tsoro duk ta dashe tayi wani fari fauuu wanda hakan yatashi hankulan jama'ar gidan nan gwaggo amarya ta tisata agaba takaita asibiti kasancewar akwai layi tunda asibitin gwamnatine yasa suka wuni curr acan basu dawoba sai la'asar liss,
Lokacin da suka dawo duk su shamsiyya na tsakar gida banda zuhuriyya wacce ke can dakinsu tana karanta littafin Hausa,
Zama gwaggo amarya tayi jikinta duk asanyaye kuma babu kuzarin kirki,
"Lafiya dai ko?

Allah yasa dai ba malaria dinnan bace ko typhoid dan yanzu su sukafi addabar al'ummarmu zazzabi kadan sai ace malaria ko typhoid" inji inna sabuwa, ita kuwa baba dake gefe cewa tayi,
"Nikuma ulcer nafi kawo mata tunda tace kirjinta har rikewa yakeyi"
Ajiyar zuciya gwaggo amarya tasauke sannan cikin sanyin murya tace,
"Kaddara ce dai Allah yarigada ya aiko mana, badiyya tajawo mana magana ta iyo cikin shege....."
"Innalillahi wa innah ilaihir raji'un" shine abinda kowannensu ke furtawa, abasiyya kuwa tsaye ta mike tana rikeda amrah amma bata san tamike dinba saboda tsananin rudewar da tayi, kowa arazane yake mutuka ita kuwa mahaifiyarsu tamkar wacce aka kafa takasa koda motsi, wani irin kuka mai ban tausayi badiyya tafashe dashi jin irin cagwadar da ake ta yimata kowa na tofa albarkacin bakinsa ana cewa tayi asara ta daukowa gidansu abun kunya, har baba yadawo tana kuka kuma taki tayi magana tambayar duniya su innah sabuwa sunyi akan tafadi wanda yayi mata cikin amma taki tace komai daga karshe saida baba yadawo shima ya iske wannan bakin labarin karshen tashin hankali shima yashiga dan da ace yanada cutar hawan jini to da tabbas babu abinda zai hanashi tashi, shima dai maganar guda dayace akan waye yayi mata ciki amma shi dinma bata fada masa ba, ai tun a wannan rana tafara ganin tsangwama da kyara da tsana domin babu ruwan kowa da sabgarta iya gwaggo amarya ce kadai ke dan sakar mata fuska tana lallabata tana yimata nasiha cewar tabata wayonta tunda ta iyo cikin shege amma ta daure tafada musu wanda yayi mata.

Da wayo da dabara gwaggo amarya tasamo kanta tace zata fada aranar da daddare bayan baba yadawo daga wurin sana'arsa dauke da tsarabar su yalo, goba, rake da sauransu gwaggo amarya ke sanar dashi tashawo kan badiyya zata fadi ko waye yayi mata wannan cikin, gaba dayansu duk sun taru atsakar gidan suna son jin abinda zatace amma sai faman shasshekar kuka takeyi taki magana wanda har hakan yasoma fusata wasu daga cikinsu musamman ma mahaifiyarsu,
"Wallahi badiyya idan nataso sai jikinki yagaya miki, wannan ai zancen banzane.....

Zakiyi magana ko kuwa?" Baba mahaifiyarsu tafada tana huci dan bakin ciki,
"A'a yimata ahankali mana, badiyya ke muke sauraro ki fada mana waye wanda yayi miki wannan cikin?" Baba yafada yana tattara hankalinsa gaba daya ga badiyya,
Cikin kuka ta daga kai takalli baba,
"Yaya abdurrahman ne mijin anty shamsiyya....."
Kowa dake zaune awurin saida maganar ta girgiza shi mutuka ita kuwa shamsiyya mikewa tsaye tayi zumbur kamar wadda aka tsikara tana kallon badiyya wacce tahade kai da gwiwa tana wani sabon kukan mai ban tausayi........
*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
*_Ummi Shatu_*
[1/23, 2:05 PM] Nawarty
: 13***Cikin rawar jiki shamsiyya ke nunata da yatsa jikinta sai karkarwa yake tamkar mazari,
"K'arya kikeyi algunguma munafuka wallahi badai mijina ba.....

Kije can kinemi Wanda ya kunsa miki wannan abun kunyar amma badai uban 'yaya na ba......"
Kuka badiyya keyi sosai tana shassheka, cikin rashin kwarin jiki gwaggo amarya takamo shamsiyya ta zaunar da ita tana fadin,
"Ya isa shamsiyya zauna ayi maganar a tsunake mana......"
"Badiyya kikace abdurrahman ne mijin yar uwarki yayi miki wannan cikin?"
"Wallahi baba shine.....

Last zuwan da nayi gidanta cikin dare yashigo dakin da nake....."
"Zan fasa miki baki idan baki daina shiryo karyarki ba akan mijina.....

Wallahi baba karya takeyi abdurrahman bazai taba aikata wannan mummunan aikin ba....

Tadaije tanemi wanda yayi mata awani wurin amma ba mujina ba...."
"Shamsiyya kiyi mana shiru kibari mugama da ita mana...." Baba yafada cikin fada yana kallonta babu shiri ta nutsu ta shiga taitayinta,maida kallonsa yayi ga badiyya wacce tahade kai da gwiwa tana faman gursheken kuka wanda sautinsa yacika gidan,
"Badiyya....." Baba yakira sunanta babu alamun wasa,
"Ki fada mana gaskiya karki yarda kiyi min karya dan idan kika yi kuskuren fada min karya to wallahi sai ranki yayi mutukar baci.....

Kifada min waye yayi miki cikin nan?"
"Wallahi baba shine, abdurrahman ne mijin anty shamsiyya"
"To dama can akwai wani abu atsakaninku ne?"
Girgiza kai tayi har lokacin idanuwanta basu bar zubar da hawayeba,
"To yaushe kuka fara wannan mugunyar rayuwar tare dashi har hakan takasance?"
"Wallahi baba babu ruwana ba laifina bane....

Wannan zuwan da nayine na karshe hakan tafaru shiyasa ma nadawo gida..."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un....." Baba yafada yana dafe kansa bayan yajingina ajikin bango,kowa nagidan jikinsa yayi sanyi kalau da jin wannan mummunan labari wai abdurrahman ne ya aikata haka amma dayawa basu yarda ba musamman ma shamshiyya dan ita anata ganin ma kawai kazafi badiyya tayiwa mijin nata kuma uban yayanta shiyasa takasa yarda azuciyarta cewa dagaske abdurrahman din ne yayiwa badiyya ciki ai kuwa yazama dole ta nemoshi awaya acikin daren nan dan taji gaskiyar lamari duk da tasanma karya ake yimasa,
"Yazama dole gobe naje gidan waliyyin abdurrahman akirashi nasakoshi agaba muzo tare domin kawo karshen wannan maganar....

Ke badiyya idanma karya kike yimasa tun wuri kifada dan gobe zai zo kuma sai kin maimaita abinda kika fada yanzu"
Daga kai tayi alamun tayarda tana faman fitar da hawaye shamsiyya kuwa saboda tsabar tafarfasar da zuciyarta keyi kasa zama tayi nan tamike tawuce daki da sauri tadauki wayarta tafara neman abdurrahman saboda tasan ai yanzu yadawo daga saudiyya tun shekaran jiya ko jiya,
Abin haushi wayar bata shigaba haka tayita gwadawa amma bata shiga ba haushi kamar ya kasheta ga wani irin zafi da ciwo da zuciyarta keyi mata tana jin haushi da tsanar badiyya na ratsa kowacce kafa dake zuciyarta akanme tazabi tayiwa mijinta sharri?

Akan me zata dangantashi da wannan mafi munin laifin?

Ko kaffara bazata yiba abdurrahman ba mazinaci bane sannan baya harkar mata,
Acan waje kuwa dakyar baba ya iya yunkurawa yatashi yashiga cikin dakinsa sakamakon nauyin da kafafuwansa suka yimasa tun bayan da badiyya tasanar dashi wanda yayi mata wannan aika aikar, nan yabarsu a inda suke babu wanda yasake iya motsawa acikinsu har tsawon wani lokaci kowa akwai abinda yake sakawa acikin ransa bama yakamar mahaifiyarsu wacce bacin ranta yafi na kowa, ita kuwa badiyya har lokacin bata bar kuka ba daga karshe gwaggo amarya ce tazo ta kama hannunta suka tafi dakinta nan taci gaba da kukanta tana mai danasanin rayuwarta, ita meye amfanin rayuwarta ayanzu?

Tazama mujiya acikin tsintsaye kowa ya juya mata baya babu wanda ya yarda da ita kowa haushinta yakeji yana ganin laifinta, kwana tayi tana kuka gaba daya muryarta ta disashe kuma idanuwanta ma sun kumbura suntun sunyi jajur saboda tashin hankali ga rashin bacci ga kuka,
Duk gidan su harisu ne kadai suka samu bacci amma kowa haka yakwana idonshi tangararau dan tashin hankali shamsiyya kuwa kwana tayi tana gwada kiran wayar abdurrahman amma bata sameshi ba sai wurin karfe 3 nadare nan wayar tayi tagama har ta tsinke bai daukaba, haka taci gaba da kiransa amma baya dauka daga karshema sai taji yakashe wayar nan damuwarta da tashin hankalinta suka kara nunkuwa.

Wayewar garin tunda sassafe baba batare da yayi ko karin kumallo ba yafita acewarsa zai koma gidan alhaji mai kwano domin yazama dole yakira masa abdurrahman yazo yawarware wannan kullin sannan yafitar dasu daga duhun da suke ciki,
Kamar jiya yauma haka tabi dakin iyayen nasu mata ta gaishesu daya bayan daya, tababa tana zaune kan abin salla cikeda matsananciyar damuwa koda yake ai yazama dole tashiga halin damuwa duba da irin yanayin da take ciki abu goma da ishirin ne yahadu yatarar mata aka, lokacin da tashiga dakin gwaggo amarya suna tare da badiyya gwaggo amarya sai Nasiha take yimata cikin harara shamsiyya ta kalli badiyyan wacce ke durkushe tana hawaye,
"Ai dama kin daina wannan kukan munafurcin kin fadi gaskiyar Wanda yayi miki ciki, sannan wallahi idan kika kuskura kika kara ambaton sunan mijina mai rabani dake sai Allah....

Banza munafukar Allah ta'ala" daga haka tasaka kai tafice hakan yasa badiyya sake fashewa da kuka musamman ma da zuciyarta tayi mata wani bahagon tunani,yanzu idan abdurrahman yazo ya musanta maganarta ya karyatata mecece madogararta?

Kuka taci gaba da yi gwaggo amarya na bata hakuri amma ina bata sanma tanayi ba har saida tagaji dan kanta sannan tayi shiru,kowa dake gidan yana daki akunshe wanda sai ka rantse da Allah mutuwace akayi musu, inna sabuwa ce kadai tasamu kuzarin fitowa tazo ta dora karin kumallo tayi duk yan aikace aikacen tsakar gida har zuhuriyya tasamu itama tafito ta tayata sukayi tare.

Shiru gidan ya wuni babu wani motsi har yamma lokacin da baba yadawo nan aka shimfida masa tabarma yazauna yana sanar dasu inna sabuwa cewa yanzun nan waliyyin abdurrahman yakirashi wato alhaji mai kwano yasanar dashi cewa gasu nan tafe shida mijin shamsiyya shiyasa yayi azamar baro wurin sana'arsa yataho gida.
Chapter 16 · 0% Book details