← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 26

Sashe 24

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko zaku ci tuwo?"
Murmushi husnah tayi ta daga ido ta kalleta,
"Anty ai duk abinda kika dafa zamu ci....."
"Ai to ban saniba ko kuna da zabi...."
"Bamu da wani zabi duk abinda kikeso wallahi muma zai yimana..."
"To shikenan Allah yakaimu daren...."
Shi dai yana jinsu baice komai ba har suka gama sai su biyu ke dan taba hirarsu ahaka har bilkisu tagama tatashi tace bari tashiga ta duba mimi wacce ke cikin bedroom tana bacci.

Da kallo yabita har saida ta kule masa yadaina hangota,sai a lokacin yasake da husnah,bayan sun gama cin abincin husnah tafita zuwa part dinta shi kuma yabi bayan Bilkisu zuwa cikin bedroom dinta,
Kwance ya isketa kusa da mimi da waya a hannunta,
"Ni zan fita....."
Kallonshi tayi fuskarta dauke da murmushi,
"Adawo lafiya ranka yadade...."
"Wannan bata tashi daga baccin ba?"
"Bata tashi ba ai gara tayi nima na huta"
"Zakiyi bayani idan taki yi da daddare...."
Daga haka yajuya yafita tabi bayansa da kallo, kwanciyarta taci gaba da yi acikin daki tana hutawa har saida su maama suka zo lokacin ne tafita dan rakasu part din husnah,ai kuwa cikin girmamawa da mutuntawa ta karbesu suka gaisa tareda yimata Allah yasanya alkhairi suka tafi.

Part dinta takoma taci gaba da abinda yake gabanta lokacin dora girkin dare nayi tashiga kitchen bayan ta goya Mimi,sanye take da doguwar riga mai karamin hannu marar nauyi,tana tsaka da aikin tuwon da takeyi husnah tashigo cikin fara'a tace,
"Anty....ashe kina nan kinata aiki,kawo in tayaki"
"Ahhh haba amarya ai baza ayi hakaba daga zuwa sai kifara aiki?

Dan Allah kibarshi karki damu wallahi..."
"A'a anty wallahi saina tayaki ai nima zama da kwanciyar wuri daya sun isheni....."
Dukda Bilkisu tana hanata amma bata yarda ba har saida ta karbi jajjagen kayan miya da yankan alayyahu ta tayata shiyasa tare suka yi girkin duk da bawata hira sukeyi sosai ba amma dai sunyi sun gama cikin armashi kuma anan itama husnah tasake ganin wasu abubuwan wadanda suka shafi girki duk da babu laifi itama tanada sani akai,tare suka kwashe tuwon shinkafar da suka girka miyar alayyahu wanda yaji isasshen nama sai kamshi ke tashi wanda idan ka shaka dolenka kaji yunwa na ratsaka koda kuwa akoshe kake,
Kasancewar lokacin anata kiraye kirayen sallar magrib yasa kowaccensu wucewa dakinta bayan sun gama shirya table, basu sake fitowa ba sai bayan da aka yi sallar ishah lokacin fahad yashigo shida su hanfa part din husnah yafara kai yaran yace suje su gaida anty sai yanzu ta tsaya tayiwa yaran kallon tsaf gaskiya tubarkalla kyawawa ne masu kama dashi sak dukkansu kamarshi sukayi,tare da ita suka shigo part din bilkisu itama fitowarta kenan daga dakin fahad tanufo falo tana rikeda mimi wacce ke tata rigimar amma ganin yan uwanta yasata fara karar murna tana bangala dariya,
Sosai husnah take kallon bilkisu afakaice wato idan Allah yabaka kishiya wayayyiya hawan jini tsaf zai iya kasheka mutukar baka kai zuciyarka nesa ba,yanzu ma wata arniyar shadda dark brown colour bilkisu tasaka sai maiko shaddar keyi dinkin ya kama jikinta kasancewar riga da skirt ne gashi taci dauri duk da bawani kalmashe kalmashe tayi masa ba simple style kawai tayi taci make up kamar mai shirin zuwa dinner Allah yasota itama tayi wanka ta sauya kayan jikinta daga na dazu zuwa doguwar riga yar kanti,kai ai dolema mutum ya koyi gayu ko dan bilkisu domin sam ita bata tsufa kullum cikin kuruciya zaka ganta,
Table dukkaninsu suka hau fahad sai satar kallon mutuniyar tasa yakeyi wacce tafito kamar amarya kai wanda bai saniba bazai iya banbance tsakaninsu wacece amaryar ba cikin nishadi suka gama cin abincin domin su Muhammad nata basu labarin gidan ayiyah, husnah zama tayi tana kallonsu saboda yanda suka sake suna hira da yaransu da alama sun gina kyakkyawar rayuwa da mu'amalarsu da yaransu tun daga tushe kawai sai taji itama tana burin ta haihu ko dan irin haka,har wurin karfe 9 suna part din bilkisu fahad baida niyyar tafiya sai bilkisu ce ma tace,
"Baby to kuje mana amarya ta kwanta tahuta ko bacci take bukata...."
Dan harararta yayi kafin yamike,
"Tashi mutafi husnah tunda anfara korarmu...."
Dariya husnah tayi ta mike tayiwa bilkisu saida safe suka fita,tana ganin fitarsu tatashi tarufe ko ina ta tattara
kan yaranta suka wuce ciki saboda tasan fahad na iya dawowa,ai kuwa sai gashi yadawo din ita lokacin ma ta kwanta,cizon yatsa yasoma yi saboda jin kofar falon nata arufe........
*_Ummi Shatu_*
[2/1, 2:48 PM] Nawarty
: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
21***Kishingide yake bisa lallausar kujera wacce take sheki kamar gold kirar royal kan cinyarsa yar karamar laptop ce yana dan lallatsawa cikin kwarewa da kwanciyar hankali,sanye yake da kayan shan iska saboda yanayin zafi da garin na yola ke fama dashi,yar karamar rigace marar nauyi light blue sai wando iya gwiwarshi dukkaninsu shara shara ne marassa nauyi,
Wani matashin saurayine yafito daga cikin wani kayataccen daki yanufoshi fuskarsa dauke da murmushi,dukawa yayi ya durkusa sannan cikin sanyin murya yace,
"Nagama kammala komai ya shugaba na...zaka iya shiga ka watsa ruwa...na gyara maka dakin sannan kuma na wanke toilet din haka kuma na wanke maka dukkanin kananan kayan naka...yanzu abinda yarage shine kayi wanka sai ka karya domin tuni anjima da hada karin kumallon da yadace dakai wanda ko tantama banayi zakaji dadin sanyawa cikinsa shi....."
Shiru yayi kamar bai jishiba, kasancewar yasaba da halinsa idan har da sabo yasashi sake gyara zamansa sannan cikin sanyin muryar da tafi ta dazu yace,
"Ya shugaba na maina da alama yau kamanta ko wacce ranace yau agareka.....yaufa itace rana mafi muhimmanci da farin ciki atare dakai....Allah ya albarkaceka ya shugaba na, Allah yaci gaba da tsareka fari mai farar aniya...hadari sa gabanka inda kakeso...sukari bakai farin banza ba....."
Idanuwanshi na kan laptop din dake bisa cinyarsa ya dan buda baki kadan yace,
"Zaidu me kace anshirya min amatsayin abin karyawa?"
"Allah ya taimaki maina dan sarki jikan sarki....akwai gurasa da miya akwai da sugar sannan akwai da zuma,sai dankalin turawa da miyar kwai sannan anyi farfesun kayan cikin saniya sai soyayyen naman kaji masu romo romo da wainar shinkafa sannan anhada maka koren shayi kamar yadda aka Saba...."
Jijjiga kai yayi yaci gaba da abinda yakeyi zuwa wasu yan sakwanni yakalli wanda yakira da suna zaidu,
"Zaidu duk afitar dasu abar min iya kazar kadai da shayin...."
"Amma ranka yadade baka dan hadawa koda gurasar ne?

Ka gafarceni ya shugaba na amma gaskiya wannan rashin cin abincin naka yafara yawa....

Kuma gwaggo kilishi har tafara korafi akai"
Dan murmushi yayi bayan yarufe laptop din dake kan cinyarshi sannan ya kalli zaidu dakyau,
"Zaidu halittar tawace ai haka ni bana son inta durawa cikina tarkace....ka kyale gwaggo kilishi gigin tsufa ke damunta...."
"Allah yaja zamaninka....." Zaidu yafada yana fadada murmushinsa,
"Kawo min abincin...."
Daga haka ya maida hankali kan wayarshi wacce ke ajiye kusa dashi bai kara bi takan zaidu ba wanda yadage yanata zuba masa kirari kamar babu gobe,
Tea din ya karba bayan zaidu ya tsiyaya masa cikin cup nan yafara kurbarshi sannu sannu yana yi yana duba jaridar daily trust da ya dauka bayan ya ajiye wayarshi,
Suna nan zaune zaman kurame yana cigaba da karatun jaridar da yakeyi aka kwankwasa kofa da sauri zaidu yatashi yafita mintuna biyu yasake dawowa cikin girmamawa ya tsugunna gabanshi yana yimasa alamar girmamawa da hannunshi,
"Maina mai wanke maka kafane yazo....ashigo dashi yanzu ko sai ka kammala karyawa?"
Agogo ya dan kalla 12 daidai na rana dan rausayar da kanshi yayi,
"Ai kawai kashigo dashi zaidu kaga yau juma'a banida isasshen lokaci sosai"
"Angama ranka yadade...." Zaidu yafada yana barin wurin cikin hanzari,
Sake kishingida yayi yana cigaba da karyawa har su zaidu suka karaso cikin girmamawa mai wankin kafa yafara aikinsa yayinda shi kuma zaidu ya zauna yana dan bawa maina labari lokaci zuwa lokaci ahaka har aka kammala wanke masa kafafun nasa,
Ciki yatashi yashiga batare da yadauki komai wanda yake wurin ba duk sai zaidu ne ya tattare su yamayar ciki bayan ya sallami mai wanke kafar,
Wankan juma'a yayi sannan yayi shirin masallaci cikin manyan kaya brown din shadda yar gaske da hula yar bama mai mutukar tsada kalar kayanshi sai agogon Rolex na azurfa turaren oud khasusi yafesa sannan yafito kafarshi sanye da takalmi silifas,zama yayi a falonshi ya dora kafa daya akan daya kamar yadda yasaba wannan shine zaman da ya iya, baiyi ko minti biyu da zamaba zaidu ya bude kofa yashigo shima cikin tashi shigar ta zuwa masallaci,
Bakaken takalma half cover irin na sarauta yaje ya dauko masa yakawo gabansa ya ajiye nan yasaka baice komai ba yatashi yayi gaba zaidu yatake masa baya har zuwa gaban motarshi wacce ke ajiye agaban sashen,bude masa gefen mai zaman banza yayi yashiga ya zauna sannan shima yashiga mazaunin driver yaja suka tafi.

Misalin karfe 2:30 zaidu yayi parking aharabar gaban sashen umma jidda nan yafita cikin sauri ya budewa maina kofa yafito yana yiwa iska wata irin shaka wacce bazaka taba gane abinda yake nufiba shin isace ko kuma sarauta?
Chapter 24 · 0% Book details