← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar yadda suka saba bayan sallar ishah suka hadu suka ci abinci a faranti daya tare da yaran nasu shiyasa wani lokacin idan yaran basa nan shima fahad din baya nan sai takasa cin abincin ita daya saboda sabo da tayi naci tare dasu, adakin yaran suke tana zaune tana kallonsu suda abbansu yana shiryasu domin kwanciya bacci,duk wanda yashirya sai yaje kan karamin gadonsa ya kwanta, saida yagama shiryasu sannan yazo ya zauna yana yimusu tatsoniya dukkansu yaran dariya sukeyi bilkisu na tayasu saboda yadda yadage yana rera wakar da gizo keyi acikin tatsoniyar, daga karshe addu'a suka yiwa yaran suka fito daga dakin kowa yanufi nashi domin shirin bacci, wanka bilkisu tayi ta zauna ta bata lokaci wurin gyara jikinta da turaruka da mayuka masu kamshi sannan tasaka rigar bacci mai daukar hankali wannan itace dabi'arta da daddare bayan yara sunyi bacci takan sa kayan bacci na daukar hankali bayan sallar asubah kuma sai tasauya da wasu kayan masu dan dama dama, tana rikeda mimi akafadarta ta wuce dakin fahad yana kwance yana waya amma jin motsinta sai yakashe wayar ita dai batayi magana ba sannan bata kawo komai aranta ba tashi zaune yayi ya karbi mimi ya kwantarta gefe guda sannan yaja bilkisu jikinshi itama ya kwantar da ita yana fadin,
"Oyoyo baby nah.....bari inbaki wani labari..."
"Am all ears..." Tafada tana gyara kanta akan kirjinsa babu jimawa yajita shiru ashe tayi bacci abinta tabarshi yanata magana Shi kadai.

Cikin yan watannin da bazasu gaza huduba ginin da fahad ke yimusu ya kammala komai sabo yasaka musu acikin gidan ginine na zamani ga bedrooms din yaransu maza nasu daban suma matan hakan gaskiya yakashe kudi ba kadanba wurin gina gidan shiyasa bahaushe yace mahakurci mawadacine wata rana, walima sosai bilkisu ta shirya musu yan uwa da abokan arziki suka zo suka tayasu murna aranar suka tare, sun tare babu jimawa yabiya musu umarah ita dashi suka tafi suka bar yaran awurin ayiyah dama Mimi ce kadai ke shan mama, gaskiya fahad karshe ne domin kamar kada su dawo dan soyayyar da ya shayar da ita sunyi ibada kuma sun sha love dan zata iya cewa aduk tafiye tafiyen da suka taba yi tare dashi babu kamar wannan, wannan shine best moment din da yafi tsaya mata arai, gida suka dawo cikeda kaunar juna da kuma dokin ganin yaransu,dawowarsu babu jimawa ta samu canjin wurin aiki domin yanzu tana aikine tare da gwamnatin jaha duk inda gwamnati take tana nan shiyasa yanzu bata samun zama sai dai sam hakan bai shafi zamantakewarta da iyalanta ba tana basu lokutansu kamar yadda tasaba.

Zaune take kan gadonta tana sanye da kayan baccinta purple colour masu mutukar santsi idonta sanye cikin farin glass din dake kara karfin ido, aiki takeyi acikin system dinta Mimi kuma na kwance gefenta tana bacci dakin duk ya gauraye da daddadan kamshi na night spray dinta, ahankali yabude kofa yashigo jikinsa asanyaye,zama yayi gefenta ya kwantar da kansa kan kafadarta,
"Bae ya akayi?" Tafada tana cigaba da latsa system dinta, dagowa yayi ya kalleta yana jin faduwar gaba,
"Baby magana zamuyi....."
Barin abinda takeyi tayi tarufe system din ta tureta gefe daya sannan ta maida hankalinta gareshi ta rungumeshi ajikinta kamar wani jariri, lukus yayi yana shakar kamshin jikinta,
"Bae meke damunka?

Uhmm?"
"Kaina ke ciwo...."
"Ayya sorry....

Kasha magani?"
Kai yadaga mata sannan ya kalli Mimi wacce ke kwance tana bacci, mayar da kallonshi gareta yayi ya dan saki murmushi,
"Bari naje dakina please kizo yanzu..."
Kai ta daga masa tana cire medical glasses din dake idonta, a wani sukurkuce yafita daga dakin nata har lokacin fa gabanshi bai bar faduwa ba kai anya kuwa zai iya sanar da ita?

Tayaya?

Kasa zaune kasa tsaye yayi adakinshi sai kaiwa da kawowa yake tayi ahaka tashigo ta iskeshi tasake bulbulo wani turaren mai rikita tunani, hannunshi takama har bakin gadonshi suka zauna,
"Kamar da akwai abinda kake son fada min ko bae?"
Lumshe idanuwansa yayi shi dama yasan bilkisu tasan shi ciki da waje takan gane damuwarsa tun kafin ya fada mata.

Girgiza mata kai yayi sannan ahankali ya kwanta ajikinta yadora kanshi akan cinyarta,
"Bana jin dadine...."
"Ayya sorry baby ai kafada min.....

Zo kayi bacci you will feel better insha Allah..."
Kafada yamakale mata nan tayi murmushi ta hade tafin hannunta da nashi tana murmushi,
"To mekake bukata da baza kayi bacci ba?"
Da hannu ya nuna ta idanuwanshi alumshe,
"Ni....?"
Kai ya daga mata, sumarshi ta shafa sannan ahankali tasoma yimasa magana kasa kasa bayan takai bakinta kusa da kunnenshi,
"Karka damu dama ni ai takace akoda yaushe but yanzu ka dan yi bacci zakaji dadin jikinka please.... da asubah sai inbiya bashi"
Kai ya daga mata, gyara musu kwanciyar tayi suka kwanta tare sai shagwaba yake zuba mata ahaka yasamu bacci.

Washe gari da safe ta rigashi fita aiki shikam bayan tafita zama yayi yanata tunanin tahanyar da yadace yabi wurin fada mata abinda ke ranshi daga karshe salim yakira yana dauka yafara fada masa shifa yakasa sanar da bilkisu, dariya salim yayi yace,
"Shiyasa idan ance kai matsoracine ka musa, kai wallahi mijin hajiyane tsoronta kakeji, simple abu ka kasa fada mata....

To me kake nufi?"
"Salim dan Allah kazo ka fada mata, yanzu tafita aiki amma nasan around 1 zata dawo saboda girka lunch..."
"Shikenan may be zan shigo....

Matsoraci kawai"
Murmushi fahad yayi yakatse wayar duk da haka fa gabanshi bai bar faduwaba dan koda yafita yaje wurin aiki ma kasa zama yayi, 2 da yan mintuna yakoma gida, yara duk sun dawo daga makaranta suna babban falo suna kallon cartoon ita kuma bilkisu taci uwar kwalliya cikin coffee din shadda ta kafa dauri sai kamshi takeyi, gaba dayansu daga ita har yaran sukaje suka taroshi suna yimasa oyoyo, hadasu duk yayi ya rungume yana kashewa bilkisu ido daya alamun tayi kyau, tanata jera masa abincin da tayi akan center table din dake tsakiyar falon salim yakirashi yace ya karaso, fita yayi yashigo dashi su hanfa suka yanyameshi suna kiran, "Abba salim oyoyo...."
"Lallai Abba salim yau kaine da rana tsaka haka?

Kodai batan kai kayi" bilkisu tafada tana dariya,
"Hajjaju takanas yau gidan nan nazo..."
"To muna yimaka maraba"
Daga haka tajuya kansu hanfa tana cemusu,
"Maza atashi aje ayi shirin islamiyya abarsu daddy suci abinci...

Oya let's go mana,muje wurinsu anty mariya su shiryaku"
Saida fahad yaga tafiyarsu sannan yamaida kallonsa kan salim,
"Abokina nidai anya kuwa bazan fasaba?

Allah bana son bacin ran hajjaju sam"
"Kai kasani, idan kaga zakayi kai kasani idan kuma kaga fasawar zakayi shima duk kai kasani....

Nidai bani abinci inci"
Daga haka yamike yasoma zuba abinci ahaka bilkisu tafito ta tarar dasu, cikin sauri tace,
"A'a Abba salim dakanka....

Bari azuba muku mana..."
Karba tayi ta zuzzuba musu sannan takoma kusa da fahad ta zauna, sunata yar hira kadan kadan amma mafi yawancin hirar itada salim keyi yana yimata hirar budurwarshi shi fahad yaki sakewa ayi dashi da haka suka gama cin abincin a lokacin ne salim ya fuskanceta,
"Hajiya bilkisu magana nazo muyi ta fahimta saboda abokina yakasa fada miki shiyasa ni ya gayyatoni dan insanar dake...."
Tattara hankalinta tayi zuwa kan salim tana kallon fahad,
"Lafiya?

Ina sauraronka dai...."
"Yawwa....

Dama fahad ne yace insanar dake zai kara aure....

Zai dawo da tsohuwar matarsa husnah....."
Ai bilkisu ji tayi tamkar anbuga mata guduma atsakar kanta wannan dalilinne yasa numfashinta ya dan tsaya cak na wucin gadi babu bata lokaci idanuwanta suka kada daga farare izuwa jajaye jur......
*ANFARA ANFARA....Tagwayen littattafai guda biyu tamkar da dubu sune aka fara sharbar romonsu wato mulki ko sarauta Kashi na biyu na marubuciya phertymah xarah da kuma takwaransa kumallon Mata wanda ke dauke da cigaban labarin kamar da wasa wanda marubuciya ummi Aisha ta rubuta...

Wanda ke bukatar wadannan dadadan littattafan guda biyu zai biya 500 mai son guda daya kuma zai biya 300 ta wadannan lambobi kamar haka.*
2083371244
Aisha M.Salis.

Zenith Bank
Sai atura shaidar biya ta wannan no
+447894142004
Ko kuma recharge card ta wannan no
08169334980
*_Ummi Shatu_*
[1/21, 5:06 AM] Nawarty
*HASKE WRITERS ASSO*.
*KUMALLON MATA.....!*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*D'andano daga labarin kumallon mata*
*3*
***Kanta ta dafe da hannunta guda daya sakamakon sarawar da taji gefen kanta yayi cikin karfin hali da dauriya ta kalli salim tana kokarin daidaita nutsuwarta wacce tayi bulaguro daga gangar jikinta na wucin gadi,
"Masha Allah.....

Kace gidan namu zai samu karuwa nan bada jimawa ba....

To Allah yasanya alkhairi...."
Juyawa tayi ga fahad wanda yayi sakare yana kallonta cikeda mamaki kamar wani soko haka yasaki baki da hanci yana kallonta, cikin murmushin karfin hali tace,
"Yanzu dama akan wannan maganar ne ka gayyato Abba salim kaki fada da kanka?

To me kake son nuna masa?

Kenan kana son nuna masa kai matsoracine ka kasa sanar dani zaka kara aure?

Well....

Congratulations, Allah yasa ayi damu..."
Shiru fahad yayi daga shi har salim bilkisu tabasu mutukar mamaki, "anya kuwa matar nan babu wani abu wanda ta boyewa ranta?

Anya da zuciya daya take yin wannan maganganun?" Wannan itace tambayar da yake tayiwa kansa acikin zuciyarsa, mikewa yaga tayi fuskarta dauke da murmushi,
"Ku dan bani 2 minutes bari nadawo....
Chapter 3 · 0% Book details