Sashe 15
Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata da amsar wannan tambayar shiyasa ta watsar taci gaba da abinda takeyi.....
*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
*_Ummi Shatu_*
[1/21, 2:04 PM] Nawarty
: 12***Yana nan tsaye inda tatafi tabarshi yajingina da jikin bango rungume da hannayensa sai turo baki yake kamar tana wurin, yasan bilkisu kawai jarumta da dauriya take nunawa amma tana da mutukar kishi akansa ko ada da bata sonsa bare yanzu da yazame mata wani sashe na rayuwarta,
Hannunshi ya cusa cikin sumar kanshi yana shafawa ahankali Allah sarki yasan yanzu watakila tana can tana kuka ko kuma tana tunane tunane dakyar ma daren yau idan zata iya bacci,
Fasa zuwa part din amarya husnah yayi yanufi wurin bilkisu domin yanada bukatar ganin halin da take ciki sam baya son damuwarta baya kaunar yaga tana cikin damuwa wannan ajininsa ne,
Bilkisu kuwa lokacin da tabar dakin fahad dakinta taje takai kayanta da ta debo kamar su inner wears, turare, hijabai da zannuwa sai kayan bacci dama su tafi ajiyewa adakin nashi, tana son ta kwanta amma kuma tana jin kamar bazata iya wannan baccinba sakamakon abinda ke sokar zuciyarta, bata kwana da yaranta amma yau yazama dole ta kwanta tare dasu ko hakan zai debe mata kewar mijinta,
Dakinsu hanfa taje ta rinka daukosu daya bayan daya tana dawo dasu dakinta tana kwantarwa kan gadonta bayan tagama tashiga bathroom ta dauro alwala kamar yadda tasaba domin hakan yana da mutukar muhimmanci kuma kariyace tsakiyar yaran tashiga ta kwanta tana kokarin yimusu addu'a taji yabude kofa yashigo, wuta ya kunna ganin kan gadon acike dasu hanfa yasashi waro manyan idanuwansa yana gimtse fuska,
"Baby daga tafiyata yau shine har an kawo masu maye gurbina...?"
Murmushi tayi tamike zaune sannan itama tayi kasa da murya gudun kada su tayar da yaran,
"Dan Allah ango kaje katafi kabarmu muyi bacci muma...
Ni wallahi bacci nake son inyi"
"Au korata ma kikeyi?" Yafada yana sake bata rai, sauka tayi daga kan gadon ta nufeshi tana zuwa takama hannunshi tajashi waje,.
"Dan Allah karka tada min da yara suna bacci...
Jeka tafi wurin amaryarka saida safe"
Hannun nata yaja yahadata da jikinsa yana laluben bakinta har yayi nasara, tureshi tayi bayan yan mintuna tana harararshi,
"Haka kawai ka bata min alwala ta..."
"Alwalar kwanciya bacci ai bata karyewa koda kuwa mutum yasake kama ruwane so karki damu da wannan....
Muje ki rakani"
"Anki din..." Daga haka tashige cikin daki tana jinshi yana cewa,
"To kin manta hular baccinki..."
Dakin yasake binta yakai mata hular ya isketa tana cikin toilet ajiye mata yayi yafita zuwa part din husnah wanda shima yahadu ajin karshe komai nata coffee and milki inbanda kamshi babu abinda yake tashi, komai dake cikin part din iri dayane dana Bilkisu har da dakin yara itama gashi nan gefe daya.
Da murmushi dauke akan fuskarsa yabude dakin nata yashiga tana kwance saman gado ta lulluba da mayafinta dan harma tafara dan bacci zama yayi daf da ita yana kallonta tasha gyaran jiki itama tayi wani kal da ita ga yiri yirin kitson dake kanta wadanda akayi mata kitson gaba kai gaskiya husnah fa ta canja sosai,
Hannunta yakamo wanda ke cikin mayafi atukunkune babu shiri tabude idanuwanta ta kalleshi,
"Ashe kana tafe sai yanzu tabarka kataho?" Tafada tana dan bata rai kadan,
Hannun nata yasake makalewa cikin nashi yana murmushi,
"Ita wa?"
"Uwar gida mana sarautar mata"
Kawar da zancen yayi tahanyar cewa,
"Nidai fatana wannan karon ba irin zuwan baya kika yimun ba...., kar naji kince kina wannan abun naki mai yawan kwanaki"
Dariya tayi masa ta lumshe idanuwanta,
"Duk matsuwarka dai kabari yatafi"
Ido yazuba Mata wanda har saida taji dan kunya wai meyasa fahad baida kunyane ita lokacin suna saurayi da budurwa wallahi kallon salihi take yimasa ashe silent killer ne duk yabi yagama batata da maganar rashin kunya,
"Bafa bacci zakiyi ba Asma'u....
Tashi dan Allah....
Kema ai amatsen kike.....
Tashi muje falo kici wani abu sai muzo muyi bacci, tashi tayi tabi bayanshi yana rikeda hannunta suka fita.
Da kuka shamsiyya takarasa gidansu dake tudun mun tsira anan cikin kwaryar kano, tana shiga ta iske duk yan gidan na tsakar gida kamar yadda suka saba zama Gwaggo amarya tana gaban murhu sai fama da hayaki take tana ta hura wutar amma taki kamawa da alama itacen danye ne kokuma wani abu mai kama da haka, kasancewar tsakar gidan irin dan kut dinnanne baida girma yasa duk tsakar gidan turnikewa da hayaki sai inna sabuwa da babarsu wacce suke kira da baba suna zaune suna tankade da dakan garin kuka wanda za akada miya dashi ganinta tashigo tana kuka yasa duk hankulan mutanen gidan yakoma kanta, wuri tasamu ta zauna bayan ta dangwarar da akwatin da tazo dashi, daidai lokacin Gwaggo amarya tazo inda take domin tayi sa'a wutar takama,
"Ke shamsiyya menene haka?
Ya zaki shigo gida da kuka?
Lafiya?"
Kafin tayi magana abasiyya,zuhuriyya da mardiyya sun fito daga cikin dakinsu sunzo wurin amma banda badiyya duk yadda akayi ita bata nan watakila,
"Wai badake nakeba shamsiyya ki fada mana abinda yake faruwa" Gwaggo amarya tasake fada cikin daga murya,
"Gwaggo abdurrahman yasakeni....
Haka kawai banyi masa komai ba"
Salati suka fara yi da sallallami jin abinda tace,
"Kuma kikace bakiyi masa komai ba?
Anya kuwa shamsiyya ayi saki batare da laifin komai ba?" Inna sabuwa tafada tana jimamim abun ita dai baba wato mahaifiyarsu batace komai ba saima tankaden kukarta da take tayi kamar bata wurin,
"Wallahi babu abinda nayi masa innah.....girki ma nakeyi yace inbari intaho gida yasakeni"
"To wannan abu dai akwai alamar tambaya domin yazo da salo na daure kai...
Allah yasawwake"
Gwaggo amarya ce tafadi hakan tana komawa gaban murhu domin har wutar tasake mutuwa, Jakarta ta bude ta kalli khamisu kaninta Wanda shigowarshi kenan da allo ahannunsa da alama daga makarantar yamma yake tace yaje yasiyo kalanzir yakawo azuba awutar ko za asamu takama.
Sai lokacin ta mayar da kallonta gasu abasiyya wadanda ke tsaye kikam fuskokinsu dauke da damuwar jin bakin labarin da tazo dashi,
"Abasiyya kuna ciki kenan...."
"Ehh wallahi anty, miko amrah din ingoya ta..."
Abasiyya tafada tana mika hannu domin karbar amrah yayinda sukuma su zuhuriyya ke tsaye basu ce komai ba saboda sosai abinda shamsiyya tazo dashi ya gigita tunaninsu,
Suna nan zaune atsakar gidan har badiyya tashigo lokacin an kusa sallar magrib, ganin shamsiyya harda akwatin kaya itama yasata yin turus tana jimami nan ta zauna suka gaisa shamsiyya nakara basu labarin irin sakin wulakancin da abdurrahman yayi mata tunda ita dai tasan bata yimasa laifin komai ba, ahaka har lokacin dawowar mahaifinsu yayi wanda suke kira da baba yana rikeda bakar leda wacce yasiyo yan kayayyakin kusa da baki kamar yadda yasaba duk lokacin da zai dawo daga wurin sana'arsa ta k'ira ganin shamsiyya shima abin yasashi cikin yanayi marar dadi dama ranar adakin baba yake wato mahaifiyar su shamsiyya yana shiga yar turakarsa yakira shamsiyya domin jin abinda ke faruwa,kamar yadda ta fadawa su gwaggo amarya haka shima ta fada masa amma takare maganar da kuka tana cewa,
"Ko shakka banayi nasan budurwarsa wacce da zai aura amma yafasa itace taje ta shiryo asirinta dan ta rabamu"
"Ya isa ki daina kuka sannan kar na kara jin kin fadi wannan maganar....
Yanzu dare yayi amma insha Allah gobe da safe zanje gidan waliyyinsa inji abinda yake kwakwai....
Allah yarufa asiri, tashi kije."
Tashi tayi tafita tana jin kwalla na taruwa a idonta wannan wacce irin muguntace abdurrahman yashiryo mata haka kawai yazabi ya rabata da yaranta dan kawai ya kuntata mata?
Dakinsu abasiyya tashiga wanda ke dauke da wasu tsoffin katifa guda biyu sai ko yan kayayyakinsu daga gefe kuma dakinma ba wani girma gareshi ba dan ko su hudunma atakure suke acikinsa, zama tayi gefen daya daga cikin katifun dake dakin tana kokarin lallaba amrah wacce ke motsi tana son tashi,
Gwaggo amarya ce ta bankado labule tashigo tana dauke da kwanukan abinci dan sai yanzune tasamu nasarar gama tuwon da take girkawa tun la'asar,
"To ga abincin naki shamsiyya"
"Tom gwaggo amarya sannu da kokari...."
Saida ta tabbatar da cewa amrah takoma bacci sannan tajawo kwanon abincin ta bude, tuwon dawane miyar kuka gashi nan bakikkirin dashi haka dai ta dan runtse ido ta daure ta caccakula taci kadan ta kwashi kayan tafita dasu,
Har lokacin baba wato mahaifiyarta ba aji kalma ko guda daya daga bakinta ba har sai da lokacin kwanciya yayi ana maganar ta yadda zasu kwanta adakin tunda yayi musu kadan shine tace wata acikinsu tazo dakinta ta kwana sai gwaggo amarya tace a'a badiyya da zuhuriyya suzo dakinta su kwana tare, sai lokacin tayarda tabbas bahaushe yayi gaskiya dan duk wanda yabar gida to gida yabarshi, ahaka dai ta kwana batare da tayi cikakken bacci ba, gari da yawaye gwaggo amarya takawo mata koko da kosai da dumame duk dai sama sama taci su sannan tatashi taje tagaida baba anan yake sake bata hakuri sannan yace yanzu gidan walin abdurrahman zaije wanda ke unguwar sharada, daga nan dakunan iyayensu mata duk tabi tagaidasu daga karshe tayi zamanta adakin innah sabuwa.
Tunda baba yafita take zuba idon dawowarshi amma shiru har la'asar atakaice dai saida lokacin dawowarsa daga makera yayi sannan sai gashi yadawo bayan yahuta yakirata kamar jiya,
"Shamsiyya naje gidan Alhaji mai kwano kuma mun tattauna dashi....
Ashe ma yaran naki suna gidansa can abdurrahman din yakaisu, to abinda yake faruwa yanzu ma shi mijin naki baya nan wai ayau dinnan yabar kasar yatafi kasa mai tsarki sai nan da makwanni uku zai dawo...
To yabani hakuri akan mujira yadawo din domin shi koda wasa bai sanar dashi cewa yasakeki ba...."
"To shikenan baba dama shima bayin kansa bane wallahi budurwarsa ce ta shirya wannan abun"
"Koma dai menene shamaiyya kiyi hakuri insha Allahu Allah yana tare dake" inji innah sabuwa kasancewar tana cikin dakin.