← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mu masoyanki ne muna sonki bama so ki kasance cikin damuwa..."
Duk wadannan maganganun da Lady keyi bata tanka ba har tagama cin abincin ta dauki robar lemon ta dan kurba, da dadin baki da komai su lady suka sakata ta shanye lemon sannan ta mike dakyar tana faman hada hanya tanufi saman gado ta kwanta ko minti biyar batayi ba bacci ya dauketa baccin da yakaita har yammaci domin lokacin da ta farka karfe 4 da kusan rabi babu kowa cikin dakin sai zeetah tana gaban gas tana juya naman kajin da take dafawa cikin babbar tukunya,
Duk jikinta amace take jinsa tamkar babu jini ko kuma babu bargo, idanuwanta kuwa dakyar take budesu saboda dakansu suke rufewa wani irin bacci ne dankare cikinsu kamar ta shekara bata runtsa ba,
Tana so tabude baki tayiwa zeetah magana amma takasa haka so take ta tashi tayi salla nanma jitake bazata iyaba sakamakon daukar da jiri tareda hajijiya kemata, dole taci gaba da kwanciyarta har zeetah ta farga da ita lokacin ta sauke farfesun da take dafawa, wani babban flate ta dauka ta cikowa bahijja ta kawo mata kan gadon da take kwance,
"Gashi tashi kici...."
Dan bude idonta tayi tana kallon zeetah,
"Daina mamaki bahijja...

Mu nan haka muke sai abinda mukeso muke ci koda kuwa namane....bama dora tukunya adakin nan sai dai idan nama zamu dafa ko ruwan zafi"
Yunkurawa tayi dakyar ta tashi zaune ta dauki farfesun tafara ci, idanuwanta nasake yimata nauyi saida ta koshi dam sannan ta ture flate din tasake kwanciya babu jimawa Lady tashigo cikin riga da skirt yan kanti ta dan yane kanta da wani guntun vail baki fuskarta taci bakin glass kafcece hannayenta rikeda manya manyan ledoji, zama tayi tana shafa kumatun bahijja,
"Sannu beauty....

Har yanzu ciwon kanne?"
Daga mata kai bahijja tayi alamar ehh hakan yasata bude ledojin da tashigo dasu ta ciro mata apple guda daya ta mika mata, girgiza kai tayi alamun ta koshi, dishi dishi tafara kallon kowa zuwa dan lokaci kankani bacci yayi gaba da ita.

Misalin karfe 11 nadare tafarka ganinsu tayi dukansu zaune tsakar dakin suna kallo a system din da bata da masaniyar ko tawaye, kallonsu takeyi daya bayan daya saboda a lokacin jinta take cikin nutsuwarta sosai sai dai rashin kuzari dake addabar gangar jikinta,
"Beauty kinsha bacci....

Barka da tashi"
Dan murmushin yake tayi sannan tajuya ta kalli lady,
"Dan Allah kubani komai nawa intafi....

Zan koma hostel dinmu"
Tashi azima tayi takoma kusa da ita,
"Haba bahijja wai antayin magana daya kenan?

Nafada miki so muke kishigo cikinmu mu zauna tare....

Duk fa nan da kika ganmu matsalarmu iri dayace kamar taki sai dan banbancin da baza arasa ba, ki kara hakuri akwai wani lokaci wanda zamu fito fili mu sanar dake ko mu suwaye....ki saki jikinki domin mun zama daya"
Tabbas a lokacin kalaman azima sunyi mutukar tasiri agareta wannan dalilinne ma yasata sakin jiki kamar yadda aziman ta bukata.

Tsawon kwanaki uku ta dauka tare dasu babu abinda takeyi sai dai taci tasha kayan maye ta tiki baccinta, rabonta da taje lectures har tafara mantawa, saida tayi sati daya adakin su lady sannan tafara fita ranar da ta fita ba yan department dinsu kadai ba kusan kowa dake makarantar indai yasanta kallon mamaki zai tsaya yana yimata, taci riga da wando matsattsu sai karamin mayafi data yafa akanta irin shigarsu Lady sak,
Bayan anfito daga lecture tana zaune ita daya tana duba wayarta taji anzauna kusa da ita, dan bata rai tayi ta kawar da kanta gefe, cikin fada budurwar da ta zauna kusa da ita tafara magana,
"Bahijja ashe da gaskene maganganun dake yawo cikin school dinnan....

Bahijja kanki daya kuwa?

Yanzu idan yaya sagir ko Umma suka zo suka ganki cikin wannan mummunar sabuwar rayuwar da kika fara gudanarwa me kike tsammani?"
Kallon up and down tayi mata sannan tace,
"Ya isa malama, ina ruwanki da rayuwar da na zaba?

Tare muka zo school dinnan ne ko tare aka turo mu daga gida?

Kiyi rayuwarki kawai inyi tawa..."
"Lallai sai yanzu nayarda da maganar bahaushe da yake cewa zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai, yanzu bahijja acikin yan kwanakin nan har kin dauki dabi'ar da ba takiba?

Bahijja nice fa?

Ki tuna tsawon lokacin da muka dauka muna tare, tun level one...

Bahijja idan kika cigaba da wannan rayuwar wallahi baki yiwa mahaifiyarki da dan uwanki adalciba sannan baki rike maraicinki ba, lokacin da yaya sagir yakawo ki makarantar nan sanye kike da hijabi har kasa harda safa akafarki kuma irin wannan shigar kika cigaba dayi har kawo lokacin da shaidan ke yunkurin sauya miki rayuwa..."
"Basira kinfa dameni...

Nafada miki kifita daga rayuwata, kin san irin halin da nake ciki kuwa?

Ko kin san irin damuwar dake cunkushe cikin raina?

Soo is better kawai kiyi rayuwarki nima inyi tawa..."
"Naji bahijja, naji ban san damuwar da ruhinki ke cikiba amma kisani ba kece mace tafarko da aka fara saka ranar aurenta aka fasa ba, wadanda irin haka tafaru dasu suna nan dayawa bazasu lissafu ba kuma hakan bai hanasu cigaba da gudanar da rayuwarsu ba...

Nidai shawarar da zan baki itace yakamata ki zauna kiyiwa kanki karatun ta nutsu tun kafin lokaci yakure miki kuma kinga yanayin karatunki yana bukatar kulawa da bada himma idan har kika cigaba da irin haka to wallahi zaki bata shekarun da kikayi abaya abanza....

Sannan abu nakarshe da zan fada miki shine idan har yaya sagir ko umma suka bukaci jin wani abu daga gareni wallahi tallahi bazan rufa miki asiri ba zan sanar dasu gaskiyar abinda nasani..."
"Kanki akeji basira...."
Basira bata tanka mataba ta dauki handbag dinta takara gaba jitake kamar ta zubarwa da bahijja hawaye yarinyar da take kamammiya kuma kamilalliya mai ibada da nutsuwa wacce ake buga misali da ita wurin kyakkyawar tarbiya amma yau itace cikin wannan rayuwar?

Gaskiya yazama dole tayi wani abu ko dan ganin ta cetota daga halin halakar da take kokarin fadawa.

Abangaren bahijja kuwa ita saima yanzune take jin dadin rayuwarta domin tana shanawa son ranta kuma bata da damuwar komai su Lady suna bata kulawa duk abinda takeso shi suke yimata, suttura abinci da komai da take bukata sai wanda ta zaba ita kanta tana mamakin wai a ina su lady ke samo kudade har haka?

Sai ahankali tafara fuskantar tayadda suke samo kudin domin wasu alhazawa garesu wadanda ke basu kudi kamar basu san ciwon nemosu ba, sam ita yanzu babu ruwanta da basira domin kayanta ma dake can wurin basirar sannu ahankali taje ta sadada ta kwaso abunta tadawo dasu dakinsu Lady, sune zuwa clubs sune shaye shayen kayan maye sune shigar banza gaba daya makarantar nan duk wasu tantirai su biyo bayansu shiyasa cikin watanni biyu kacal bahijja ta goge acikinsu tazama tantiriyar yar duniya dan harma taso tafisu iya bariki kawai ita abu dayane bata yi bin maza wannan kam tayiwa kanta alkawarin bazata taba bin mazaba saboda ta tsani maza ayanzu bata ko kaunar hada hanya dasu sakamakon sune suka jefata halin da take ciki, cikin yawace yawacensu na zuwa party da picnic ta hadu da wani yaro tacacce irinsu waishi faruk tare suke haduwa suyi shaye shayensu yasake budar mata da ido,dayake shi bai nuna mata jikinta yakeso ba shiyasa ta yarda suke mu'amula dan bai taba ko gwada rike hannunta ba.

Har aka kafe musu time table din exams bata fara karatu ba,cikin wannan hali Yaya sagir yakawo mata ziyara kamar yadda yasaba saida yakira basira kawarta saboda ita wayarta akashe take tun jiya.

Yana sanye cikin shiga ta manyan kaya matashine wanda bazai wuce shekaru 34 ba, asanyaye basira tazo suka gaisa sai dai harga Allah bata da niyar boye masa gaskiya gara ta fada masa ko zai samu nasarar samo bakin zaren,
"Kanwata ya naganki ke daya?

Ina yan biyun taki?"
Murmushin yake tayi ta sunkuyar dakai,
"Yaya sagir ai yanzu bama tare da bahijja domin tabar dakinmu takoma na wasu...."
"Bakwa tare?

Fada kukayi ko me?"
"Sam ba fada mukayi ba yaya sagir, bahijja yanzu ta gujeni ta koma ta hada kai da wasu marassa tarbiya, yan shaye shaye, yan lesbian, marassa son karatu inbanda kule kulen maza da yawon zuwa clubs babu abinda sukeyi...

Bahijja gaba daya ta sauya hali tatashi daga bahijjan da kasani ada tadawo wata sabuwa ta daban....

Ko sutturar mutunci yanzu bata sakawa,duk wanda yasanta ada ayanzu ta sane masa sakamakon muyagun dabi'un da ta dorawa kanta, ni yanzu ko ahanya muka hadu bata yimin magana saboda bata son infada mata gaskiya...

Dama naki fada makane tun farko saboda gudun kada taga laifina na shiga tsakaninta daku amma dama araina nayi alkawarin muddin ka tambayeni to babu abinda zan boye maka...."
Dafe kansa yayi yakoma cikin mota ya zauna yana karanta Kalmar,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..."
"Yaya sagir kayi hakuri yanzu dai kawai mafita ya kamata anema domin agaskiya ko karatu bana jin tana zama tanayi gashi karatunta yana bukatar cikakkiyar nutsuwa..."
"Na kikkira wayarta akashe tun jiya amma shekaran jiya munyi waya da ita dama ban fada mata zanzo ba unexpected visit naso yimata...

Ko zaki je ki nemo min ita?

Yafada idanuwansa jajur sakamakon bacin ran da yake ciki,
"To bari naje na nemota.." Daga haka tajuya tatafi tabarshi cikin kunar rai, da dakinsu lady tafara amma basa nan dakin nasu arufema yake da wani garkamemen kwado daga can tawuce duk inda tasan zata iya samun bahijja amma bata sameta ba tafi awa daya da rabi tana yawon nemanta amma babu ita babu alamunta kai ko mai kama da itama bata ganiba su kansu kawayen nata su lady ko daya acikinsu bata ganiba haka ta dawo wurin yaya sagir jiki asanyaye gwiwa asace ta sanar dashi nemar wuri yayi yasake gyara parcking din motarshi dan ya daukarwa kansa alwashin cewa ko zai shekara a bauchi bazai tafiba sai yajira bahijja tadawo daga duk gidan uban da taje gashi wayarta har lokacin akashe take wuni guda har magrib yakai aciki makarantarsu amma shiru bata dawo ba duk da baizo da niyyar kwana ba amma yazam
a dole ya kwana.
Chapter 10 · 0% Book details