← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 26

Sashe 13

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zamanin da wani abunma idan kaji sai kaji kamar kayi me dan tsananin takaici da ban haushi, bata sake sanin halin da bahijja take cikiba saboda bata koma dakinba nan taji gaba da zama har la'asar lokacin ne tatashi domin yin sallar la'asar dakin ta leka taga bahijja ta hada kai da gwiwa amma dai da alama ba kukan takeyi ba,
"Bahijja fito ga abinci can kije ki zuba kizo kici...."
Daga haka bata kara cemata komai ba tafita zuwa falo ta fara salla, tana jin abinda umma tafada to amma kuma bata san ta yadda zata fita har su hada ido da itaba da wadannan watsattsun kayan dake jikinta, dabara ce ta fado mata nan tatashi taje ta bude wardrobe ta dauko atamfa daga cikin kayanta wadanda tabari bata tafi dasu school ba, doguwar rigace da dan kwali sakawa tayi sannan tafita duk jikinta shatin bulala sakamakon dukan da yaya sagir yayi mata, a falo tawuce umma tana salla tashiga kitchen don bin umarnin umma amma bawai dan tana son cin abincin ba, dan waken fulawa tagani cikin flask kadan ta zuba tasaka man gyada da yaji sannan ta dauko sinadarin dandano tafito aranta tana jinjina irin son da umma ke yiwa dan wake domin tana mutukar kaunarsa bata yin cikakken sati batare da ta yiba, anan tsakar gida ta zauna taci bayan tagama tashiga falo har lokacin umma na kan abin salla bata tashiba, daki tawuce taje tayi alwala itama tazo tafara nata sallolin saboda ko azahar bata yiba.

Har magrib tayi bata iya fitowa ba tana daki atakure ita daya domin tunda tazo umma bata shiga harkarta sau dayama dal tayi mata magana tun bayan lokacin da yaya sagir ya sanar da ita halin da ake ciki,
Tana jin umma na sauraron labarai a radio daga baya takashe bayan angama, tana son tafita taje wurinta amma bata da abinda zata fada mata idan taje bata San me zatace mata ba ita yanzu ma kunyar umman takeji sosai har lokacin sallar ishah yayi bata samu mafita ba daga karshe itama tatashi zata yi salla ananne ta dan leka umman ta kafar labule sai ta hangota tana salla, itama sallar tayi tana cikin yi tajiyo sallamar yaya sagir umma na amsawa,
Duk da tana son fita amma kasawa tayi Allah sarki rayuwa ada idan yaya sagir yazo tare suke haduwa su ukun suyi hirarsu kafin yayi aurema kuwa tare suke koda yaushe itace kuma yar gata shi yayi mata umma ma tayi mata amma yau gashi mugun halinta da ta fara yaja anwareta, sam bata jiyo abinda suke cewa har suka gama tajiyoshi yana yiwa umma sallamar cewa yatafi ita kuma tana cewa yagaida Marakisiyya matarsa.

Sai wurin karfe tara da yan mintuna sannan umma tashigo cikin dakin har lokacin takure bahijja take ta hada kai da gwiwa, shirin bacci umma tayi tahau kan gadonta ta kwanta tana fuskantarta,
"Bahijja naji duk abinda kikeyi kuma kin kyauta....

Dama irin wannan tarbiyar na baki?

Haka kika taso ni kikaga inayi?

Azagayen nan wacce yarinyar arzikin kika taba jin tana shan kayan maye ko tana rayuwar dabbobi tana neman mace yar uwarta?

Ai ko su dabbobin baki taba ganin mace ta nemi mace ba....

Ke yanzu bakiji kunyar kanki da kanki ba?

Sannan abin naki har yakai kibi saurayi wata uwa duniya kuje ku kwana tare?

Irin tarbiyar da na baki kenan?

Duk kokarina akanki so kike sai duniya ta zageni?

Duk irin son da nake na ganinki kin zama abar koyi acikin rayuwa shine kike neman rusa rayuwarki?

Kin kyauta kuma kinyi dai dai...

Yayanki ya hadani da basira naji komai daga bakinta...."
"Dan Allah umma kiyi hakuri wallahi bazan karaba....

Dan Allah ki yafe min...

Wallahi sharrin shaidanne..." Tafada cikin kuka,
Umma bata sake kulataba tayi shiru abinta kamar mai bacci amma azahiri ba baccin takeyiba kawai tsabar damuwace da bacin rai ke dawainiya da ruhinta, itama bahijja kasa baccin tayi sai da dare yaraba sosai sannan bacci ya dauketa anan inda take zaune kan sallaya.

Washe gari umma bata yimata magana ba lokacin da ta gaisheta ma dakyar ta amsa shima yaya sagir yanzu baya kulata idan yazo gidan ko kallonta bayayi tsakaninta da Umma kuwa gaisuwa ce amma bata sakar mata suyi hira kamar da.

Yau kwananta biyar da zuwa gidan tana daki tana gyarawa duk da umma bata nuna farin cikinta idan ta tayata aiki ahalin yanzu,kakarin aman umma tajiyo nan ta fancakalar da tsintsiyar tafita da sauri, ummace akofar kitchen durkushe tana aman jini....

Hannu tadora aka ta kurma ihu domin ba karamin tsorata da gigita tayiba cikin tashin hankali taje ta rike umma wadda jikinta yasaki sosai, duk ta gigice ta rude ta fita hayyacinta tama rasa me yakamata tayi da azamarta tasaki umma ta nufi falo da gudu tana zuwa ta dauki wayar umma takira yaya sagir, cikin karaji tayi masa magana lokacin da yadaga wayar, ko katse kiran batayi ba ta ajiye wayar takoma wurin umma wacce har lokacin jini bai bar fita ta bakinta ba, sake riketa tayi tana yimata sannu ahaka yaya sagir yazo yasamesu babu bata lokaci suka tafi asibiti mafi kusa suna zuwa aka shigar da ita emergency, bahijja sai kuka takeyi,dukkansu cirko cirko sukayi suna jiran abinda zaije yazo amma ita bahijja harda kuka take hadawa.

Anan asibitin suka wuni cur sai dai idan ana bukatar abu yaya sagir yaje yasiyo yadawo anan marakisiyya matarshi tazo ta samesu suna zaune jugum, duk wani abu da zasu bukata ta kawo musu kama daga kan su abinci, ruwan zafi, ruwan sha da komai da komai amma cikinsu babu wanda ya iya shan koda ruwa, marakisiyya ce keta kwantar musu da hankali tana basu baki, sai dare suka samu shiga wurin umma lokacin tana bacci amma tayi wani irin fari sosai, suna zaune harta farka likita yazo yasake dubata yafita, daga yaya sagir har bahijja a asibitin suka kwana da yace taje sutafi tare da marakisiyya su kwana sai tasaka masa kuka kawai shiyasa ya rabu da ita yabarta itama ta kwana a asibitin.

Kwanan umma biyu a asibitin ta dan samu sauki dan har tana bude baki suyi hira da ita aranar aka dauketa daga emergency aka sauya mata daki, hira tayi da bahijja sosai nan take cemata tayafe mata abunda tayi sannan dan Allah takula da rayuwarta saboda itafa macece abu kadan ke ruguza rayuwar ya mace, saida yaya sagir yazo sannan tace zataje gida tayi wanka tadawo har Umma nayi mata adawo lafiya, minti talatin yayi yawa taje tayi wanka agurguje tadawo tana zuwa taga yaya sagir da likita harda nurses akan umma suna lullubeta da zaninta dake ajiye gefe guda.....
*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
*_Ummi Shatu_*
[1/21, 5:08 AM] Nawarty
: 10***Wata razananniyar kara tasaki ta durkushe awurin tana kuka wiwi dan tagama tarbatarwa kanta cewa umma ta rigamu gidan gaskiya,
Yaya sagir ne yazo ya dagota ya rungumeta ajikinsa shima yana fitar da kwalla mai zafi, likita da nurses sai hakuri suke basu suna yimusu addu'ar Allah yajikan umma yasa ta huta, cikin karfin hali yaya sagir yaciro wayarshi daga aljihu sakamakon jin karar da takeyi yana dubawa yaga hajiyan taraunice yayar ummansu, cikin karyayyiyar zuciya mai cikeda raunin murya ya dauki wayar hawaye nabin idanuwanshi nan yasanar da ita dakin da suke saboda ita duba umman tazo yi dan jiya da daddare sunyi waya dashi anan yake sanar mata da rashin lafiyar umma,
Mayar da wayar aljihunsa yayi har lokacin yana rikeda bahijja wacce kanta ke neman juyewa domin wani irin kuka takeyi kamar mai aljanu kai da ganinta kasan bata cikin hayyacinta,
Zuwansu hajiyan tarauni da samarin yaranta guda biyu wadanda suka kawota amota yasake hargitsa dakin domin yaya sagir baiwa hajiya bahijja yayi suka rungume juna suna kuka shikuma shida su Annur suka fara kiciniyar fitar da gawar umma,
Tun kafin akai gawar gida jama'a sukayi cincirindo maza da mata domin umma tasamu shaida kowa alkhairi yake fada akanta sam bata da abokin fada, saida aka jira yan uwa sukazo sannan aka shiryata ita kuwa bahijja har lokacin bata san inda kanta yakeba sai sumbatu taketa faman yi marakisiyya matar yaya sagir da hajiyan tarauni na rikeda ita suna faman yimata addu'a duk da suma suna cikin tashin hankali da dimuwa fuskar kowannensu sharkaf da hawaye.

Har akayi kwana biyu da rasuwar bahijja bata dawo cikin hayyacinta ba kowa ita yake tausayawa saboda ganin itace mace sannan ga yanayin halim da take ciki, ranar sadakar uku ta dan fara nutsuwa amma kana kallonta zaka gane mutuwar nan ta bugeta saboda mutuwar mahaifi ba wasa bace sai yanzu tasan mutuwa nada mutukar daci idan akayi maka ji kake kamar duk duniya ba ataba yiwa waniba sai kai,
Tana zaune gurumm kusa da hajiyan tarauni da kannen umma guda biyu baba ladiyo da baba fatsima su azima suka shigo kawayenta domin yimata ta'aziya dakyar ta iya amsa musu daga nan bata kara maganaba har suka yimata sallama suka tafi, hawaye kwata kwata yakasa yankewa yadaina zuba daga idanuwanta.

Tun aranar wasu suka tattafi yarage sai iya dangi na jiki kadai musamman ma dangin mahaifiyarsu amma dangin abba duk yau suka tafi sai iya abban bebeji kawai kanin abbansu wanda yanzu shine amadadin mahaifinsu tun bayan rasuwar mahaifinsu lokacin ita tana secondary school shikuma ya sagir yana university level two,sai dai abinda ke kara sakata kuka shine yanda yaya sagir baya ko yimata magana ta lura kamar fushi yakeyi da ita mai tsanani.

Har akayi bakwai bata ga fuska awurin yaya sagir ba kuma aranar su abban bebeji zasu tattafi shiyasa bayan angama addu'o'i da sadaka abban yashigo yatarasu gaba daya yafara jawabi kamar haka,
"Allah yajikan Maimuna yakai haske kabarinta sannan halinta na gari yabita...

Hakika munyi rashi babba sai dai Allah yabamu hakurin jure wannan rashi....
Chapter 13 · 0% Book details