← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 26

Sashe 17

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin abinda baba yafada yasa shamsiyya taji wani irin sanyi cikin ranta yawwa ko babu komai abdurrahman zaizo yayi bikonta sannan ya musanta sharrin da badiyya ta kulla masa, su mardiyya ta kalla,
"Ku fara tattare min kayana dan yau dinnan zan koma gidana inbar muku dakinku yanmata"
Dukansu dariya sukayi ita dai alla alla takeyi su abdurrahman suzo amma basu karaso ba sai bayan sallar la'asar dawowar baba daga masallaci kenan suka ganshi yashigo tare da alhaji mai kwano da kuma abdurrahman wanda yake sanye cikin shadda ruwan toka harda hula, ta window shamsiyya ke lekenshi gaskiya yayi kyau sosai musamman ma da ta kwana biyun nan bata ganshi ba sai taga yasake zama wani handsome fiyeda da,
Mintuna uku baya taga gwaggo amarya ta leko dakinsu takirata hijabi tasaka sannan tafita taje ta zauna kusa da inna sabuwa,
"Abdurrahman rannan saiga shamsiyya tazo tana kuka tace wai ka saketa batare da kuma tayi maka laifin komai ba,muna son kafada mana abinda yafaru"
Sunkuyar da kai yayi kasa sannan cikin ladabi yace,
"Ehh baba abinda tafada gaskiya ne na saketa saki daya kuma bata yimin laifin komai ba"
"To dama ana sakine batare da laifi ba?" Alhaji mai kwano ya bukata yana kallon abdurrahman din,jin yayi shiru yasa yaci gaba,
"Maganar ka saketa babu laifin tsaye ba na zaune bai tasoba ka maida matarka kuje kuci gaba da rike yaranku"
"A'a Abba bazan iya maida itaba, gaskiya bazan iya sake zama da itaba amatsayin matata...."
"Tana yimaka wani abune wanda baka so?" Baba yabukata,yayinda ita kuma shamsiyya jin abinda abdurrahman yafada tuni hankalinta yatashi tashiga damuwa,
"Baba babu abinda take yimin kawai dai bana kaunar sake koda ganinta ne ahalin yanzu...."
Fashewa shamsiyya tayi da kuka mai sauti,
"Wallahi baba dama saida nafada muku tsohuwar budurwarsa ce tayi masa asiri dan ta rabamu....."
Sai lokacin abdurrahman ya kalleta ranshi nayi masa zafi saboda jin abinda tace,
"Ya isa shamsiyya yi shiru, to abdurrahman tsugunne fa bata kareba......

Sabuwa kirawo badiyya"
Har badiyya takaraso cikin sassarfa shamsiyya kuka takeyi ita wanne irin laifi tayiwa abdurrahman da yake ikirarin bazai maida ita dakinta ba?, tsaigata kukan da take yi tayi saboda jin abinda baba ke cewa,
"Ke badiyya yimana bayanin da kikayi abaya da bakinki kowa yaji ga abdurrahman ga waliyyinsa...."
Cikin kuka badiyya tafara rattabo jawabi kamar yadda tayi abaya nan bacin ran shamsiyya yasake nunkuwa jin har yanzu badiyya nakan bakanta tana cewa abdurrahman ne wai yayi mata ciki, cikin masifa da bacin rai tace,
"Kajiko...

Kaji sharrin da yarinyar nan keyi maka ko abban musaddiq...."
"Ke shamsiyya kiyiwa mutane shiru kibarshi ya amsa da bakinsa, abdurrahman menene gaskiyar lamari?" Baba yafada yana dubanshi,
"Ehh baba duk abinda badiyya tafada hakane kuma gaskiyane....."
Yafada hankali kwance kuma cikin nutsuwa sam bai nuna alamun tsoro kokuma alama ta rashin gaskiya ba.....
*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
*_Ummi Shatu_*
[1/24, 9:08 AM] Nawarty
: 14***Kowa dake wurin shiru yayi sakamakon mamaki da tashin hankalin da ya mamaye zuciyarsa saboda jin abinda abdurrahman yafada wato amsa laifinsa da yayi cikin hanzari da kuma sauki batare da ya wahalar da zukatansu ba,
"Abban musaddiq idan rufa mata asiri kake son yi ko taimakonta ai basai ka dauki laifin da ba naka ba....." Shamsiyya tafada cikin tashin hankali dan ita har yanzu zuciyarta takasa gasgata mata cewar shine ya aikata wannan danyen aikin,
"Abdurrahman kace Kaine kayi wannan aika aikar?

To shin kamanta ne cewa badiyya kanwar matarka ce uwa daya uba daya?" Baba yafada yana cikeda damuwa,
"Baba ban manta ba,tsautsayine da k'addara da kuma sharrin shaidan...."
"Kaji maganar banza, tsautsayi a ina?

Babu wata k'addara da wani shaidan kai ne nan babban shaidanin...gaskiya abdurrahman you highly disappointed me....dama abinda kake aikatawa kenan?" Alhaji mai kwano yafada cikin bacin rai da bakin ciki,
Kasa magana abdurrahman yayi illa sunkuyar da kansa ma kasa da yayi alamun jin nauyi,
"Yanzu malam menene abin yi?

Wanne mataki kake ganin yadace mu dauka?" Alhaji mai kwano ya bukata cikin tashin hankali,
"Ai alhaji Ina ganin kawai sai dai mujira zuwa lokacin da zata haihu tunda haka Allah ya kaddaro amma gaskiya ni baza ayi kisan kai agidana ba kaga idan akayi haka kamar andora wani laifinne akan wani.....muyi hakuri mu dauki k'addara mujira lokacin haihuwarta...."
Wani kuka shamsiyya tafashe dashi sannan tamike tashige daki tana gursheken kuka,har lokacin iyayensu mata basuce komai ba sakamakon jin iya mazanne ke tattaunawa ba asako bakinsu ba aciki.

"To maganar mayar da shamsiyya dakinta kuma fa?" Inji alhaji mai kwano,
"Abba gaskiya bazan mayar da itaba kawai idan ta kammala idda tana samun miji tayi aure....."
"Allah yasa haka shine yafi alkhairi..." Inji baba,mikewa alhaji mai kwano yayi Wanda daga gani kasan cikin bacin rai yake nan baba yatashi yabishi yana bashi baki yana cemasa babu komai k'addara ce,shi kam abdurrahman yakasa hada Ido da mutanen gidan akunyace jiki asanyaye yatashi shima yabi bayansu baba yabar su gwaggo amarya wacce ke rarrashin badiyya sakamakon kukan da take ta faman rerawa sannan itama shamsiyya daga dakin da take ana dan iya jiyo nata kukan, mahaifiyarsu kam takasa cewa komai bama ita kadai ba kowa dake zaune wurin duk jikinsa yayi la'asar.

Sumi sumi yake biye dasu abaya har zuwa gaban motar da suka zo da ita cikin bacin rai wanda ya bayyana karara saman fuskarsa alhaji mai kwano yabude kofar motar yashiga yana sake baiwa baba hannu domin yin musabaha shikam abdurrahman jiki asanyaye zuciya abace shima yashiga gaban motar yaja suka tafi wanda har sukayi nisa alhaji baice dashi ko ci kanka ba yasan hakan bai rasa nasaba da fushin da yakeyi dashi.

Dakyar gwaggo amarya ta daga badiyya zuwa cikin dakinta bayan fitarsu abdurrahman inbanda gunjin kuka babu abinda takeyi sannan itama shamsiyya tana daki tanata rusar nata kukan shiyasa hankalin mutanen gidan gaba daya atashe yake nan suka taru sunata bawa shamsiyya baki,tabbas yau tana cikin kaduwa tareda tashin hankali marar misaltuwa cikin kukan da taketa faman rusa tamika hannu tajanyo wayarta tana rage sautin kukanta sakamakon hakurin dasu zuhuriyya ke bata suna zaune zagaye da ita,
Number abdurrahman taketa faman kira amma yaki ya dauka domin Shi lokacin ma yana zaune kasa afalon alhaji mai kwano shida matarsa hajiya lubna sun sakashi agaba sai fada suke zuba masa kamar zasu koneshi saboda abinda ya aikata sai bayan da suka gama yabasu hakuri yataso yafito lokacin yasamu zarafin daga kiran da shamsiyya keta faman yimasa,cikin bakin ciki yace,
"Wai malama menene kika wani tisani agaba da kira kamar naci miki bashi?"
Cikin shasshekar ku
ka tace,
"Yanzu abdurrahman abinda ka aikata kayi daidai kenan?

Kanwata uwa daya uba daya ka iya rab'a?"
"Laifin waye?

Duk bakece kika janyo min wannan masifar ba?

Kece ummul aba'isin din shigarmu wannan bala'in,kuma wallahi Allah ya isa tsakanina dake....ban taba aikata zinaba amma saboda masifar kazamin zafin kishi irin naki kika shiga kika fita kika hanani kara aure daga karshe shaidan da sharrin zuciya suka kaini har na sabawa mahaliccina na aikata babban laifin da yayi hani dashi....kisani ayanzu banda makiyiyar data fiki kuma sai kinyi nadamar abinda kika aikata domin Dr Bala ya fayyace min komai...nayi nadamar kasancewarki uwar yayana nayi nadamar kasancewarki matata Ada...kash.... how i wish zan iya mayar da hannun agogo baya da wallahi nagogeki acikin tarihin rayuwata...azzaluma wacce bata san komai ba sai son kanta..." Daga haka bai jira amsar da zata bashiba yakatse wayar yana jiyo shasshekar kukanta gudun kada ta sake kiranshi ma gaba daya kashe wayar yayi ya cilla kujerar dake makotaka da ta driver yafigi matarsa aguje yabar gidan,gaba daya yanzu ji yake yatsani mata zaiyi wahala idan zai kara auren wata asauran lokutan da yarage masa acikin rayuwarsa.

Sai da taji fitarshi kuma ta tabbatar cewa fitar yayi sannan tafito daga cikin toilet din tana goge fuskarta da dan karamin towel,agefen gado ta zauna tana kallon yaransu dake kwance suna ta shakar baccinsu cikin nutsuwa jitake kamar zata fashe da kuka dan radadin da zuciyarta keyi mata kishi ne kawai ke dawainiya da ita shiyasa jinta take kamar daren yau shine mafi munin dare acikin rayuwarta jin kunci na neman lullubeta har shaidan yaci galaba akanta yasata soma ambaton Allah jin nutsuwa tasoma saukar mata yasata shiga tsakiyar su hanfa ta kwanta tare da kunna karatun alqur'ani awayarta kira'ar shaikh Ahmad sulaiman kano cikin suratul Ahqaf tun daga farkon surar har zuwa suratul juma'ah lokacin kam nutsuwarta tajima da dawowa gareta dan harma bacci yaci karfinta dakyar ta iya kashe karatun ta kashe wayar ta gyara kwanciyarta nan bacci yayi gaba da ita wanda ba ita ta farka ba sai karfe 7 nasafe wannan dinma Muhammad ne yatasheta kasancewar sun horar da yaransu yin salla akan lokaci ganin irin makarar da suka sheka abin yabata mamaki mutuka da azamarta tashiga toilet tayi alwala tafito tazo tayi salla lokacin suma yaran duka sun tashi amma banda Mimi ita kam har lokacin baccinta take ta sha.

Bata tsaya komai ba bayan ta idar da salla ta fada kitchen domin shirya musu breakfast da wayarta tatafi ta kunna karatun alqur'ani tana aikinta tana saurara sannan tana bi cikin lokaci kankani ta shirya egg rolls, chips sai kuma kidney vegetables sos da kunun alkama saboda yaranta shi suke sha safe da yamma wani sa'ilin ma har dare,
Sai da ta kammala komai tsaf sannan takoma daki lokacin karfe 9 saura wasu mintuna wadanda bazasu gaza biyu zuwa uku ba wanka tashiga saboda duk yaran bacci ta tarar dasu sun sake komawa har tafito basu tashi ba murmushi tayi tana tuno rashin jinsu da kiriniya shiyasa idan suka kwanta bacci kamar bazasu tashi ba saboda kowa kwallon kansane cikinsu.
Chapter 17 · 0% Book details