← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dai dai yake taku har zuwa cikin sashen nata wanda ke kawace da ababen more rayuwa,babu motsin kowa sai kukan tsintsaye wanda har hakan yaso bashi mamaki domin yasaba ganin jama'a dankam asashen nata,anutse yabude kofa yashiga,yana shiga yasake shiga cikin wani mamakin domin wani hadadden decoration akayi kamar hall din biki ko ina balam balam ne different colours anyi ado dasu ganin wurin ya gauraye da duhu ya dan ji rass amma sai ga wasu kaloli sun fara kawo rubutu mai dauke da _Happy birthday maina_, kafin yayi wani motsi yajiyo ihun mutane suna ihun "Happy birthday to you...... happy birthday to you......"
Ajiyar zuciya yasaki ya dan fadada murmushinsa yajuya yana kallonsu,dukansu jere suke cikin kwalliya ta alfarma sunyi mutukar kyau,jinin sarauta kenan,sun doshi su goma mata da maza dukkaninsu kannenshi ne da cousins dinshi,kan kujerar da aka tanada dominsa yaje ya zauna yana kallonsu daya bayan daya cikeda nishadi,wani gingimemen cake ne girke gabansa ummussalma ta mika masa wuka wai ya taimaka ya yanka tashi yayi ya yanka yabisu daya bayan daya yana saka musu abaki,sai da yagama dasu sannan yanufi dakin umma jidda wacce yasan koda za ashekara ana wannan shagali tofa bazata fito ba shiyasa shima baya iya sakewa da ita,
Yana shiga ya isketa Kishingide kan carpet tana fuskantar kofa amma ganinsa sai ta juya baya shima asanyaye yakarasa gefenta ya durkusa ya gaisheta gaisuwar dai bata wuce uku kamar yadda aka saba daga nan suka cigaba da zaman kurame har na tsawon wasu mintuna kafin yamike yana fadin,
"Nabarki lafiya ranki yadade...."
Bata amsaba har yafita daga cikin dakin,har lokacin masu shagalin birthday na nan kamar yadda yabarsu sunata faman shan rawa,dakyar shikam ya yarda yatsaya sukayi hotuna dasu sannan yafita yanufi sashen gwaggo kilishi.

Tun daga bakin kofa yake karaskiya da bayi amma babu wata gaisuwa tsakaninsu musamman ma matan saboda kasancewarshi ustaz kowa yasan halinsa a masarautar da iya maza kadai yake mu'a amalarshi banda mata tsakaninsa da mata sallama ce itama ba koda yaushe ba,
Lokacin da ya isa sashen kilishi ya iske sai drama ake yi da ita akan cin abinci ita alallai sai taci abinda likita ya hanata ci kasancewar tanada lalura,mabruka na gefenta sai lallabata takeyi shigarsa yasanya mabrukan fita zuwa cikin daki sukuma sauran bayin dake zagaye da ita suka fita izuwa sashensu,
Zama yayi yana kallonta irin kallon tuhuma,
"Ke wai meyasa kike da taurin kai da kakkafiya ne?

Ga abunda likita yace kici amma baza kici ba......kiduba fa kiga irin halin da kika shiga last month kika samu muka rinka wahala da dawainiya.....kece India kece chairo kece saudiyya duk dan kisamu lafiya amma shine yanzu saboda kin samu sauki zaki kara zuwa ki jangalo mana wata wahalar....."
Tunda yafara maganar take harararshi har lokacin da yagama saida ta kare masa harara sannan tace,
"Umhummm ai dama maganar kenan....fitinanne mai jarabar sa idon tsiya....idan mutum yayi magana kuma kaje ka kaishi gaba har wurin mai martaba....."
Dariya yayi ya jingina da jikin kujera bayan ya cire hular dake kanshi,
"Dan Allah dan saka akawo min wannan dambun naman kinji amaryas...."
Harara ta sake jifanshi dashi sannan ta ja dambun accha din dake gabanta wanda dazu su mabruka keta lallabata akan taci amma taki,
"Bani dashi.....kaima kayi zuciya ka auro mata tarinka yimaka mana"
Dariya yayi yamike yanufi hanyar bedroom dinta yana cewa,
"Maganar dai kenan kwaya daya kullum itace....bakida wata magana saita aure"
Yana jiyota tana fadin,
"Haisam karka yarda inshigo dakin nan insameka....kafito min daga cikin daki na fada maka"
Bai fito dinba har saida yadebo dambun naman cikin flate sannan yazo yasake zama kusa da ita,
"Maina kasan me nake so dakai?

Kasamu yarinyar can ku daidaita kanku daga nan zuwa watanni biyu domin ni ayanzu banida burin da yawuce naga na aurar daku gabaki daya...." Tafada tana nuna masa dakin da mabruka take ciki,
"Meyasa kika damu da wai lallai sai kin aurar damu ne?

Me muka tare miki?"
"Baku tare min komai ba maina amma lokaci yayi wanda yadace ace kasamu iyali....ka duba kaga duk kannenka kowa da iyalinshi daga matan har mazan kai kadai yarage yanzu kuma kaine babba....kaduba kaga duk kannenka mai martaba yabawa kowa sarauta mai daraja amma kai ya hanaka saboda bakada aure ko hakan bazai saka kayi aureba?"
Murmushi yayi yana taunar dambun naman dake bakinsa tabbas kam shi yasan wannan shine dalilin da yasa mai martaba bai bashi sarauta ba amma sauran kannenshi kowa yanada ita tunda ranar shagalin aurensu ake hadawa da na sarautar ayi amma dayake masarauta ba arabata da gutsuri tsoma da jita jita mutane sai suka juya maganar suka ce wai dan sarki yafi son haisam ne shiyasa bai bashi sarauta ba saboda shi yake son ya gajeshi kowa a cikin masarautar akan wannan tunanin yake sannan kuma dashi din ya yarda,
"Nidai dan Allah maina badan na isaba ku daidaita kanku kaida mabruka kaga ai yar uwarka ce cikinku daya...."
Sai lokacin ya dakata da taunar da yakeyi ya zuba mata dara daran idanuwanshi masu haifar da kasala,
"Wai gwaggo kilishi ana so dole ne?

Tace bata sona nima bana sonta to ba shikenan ba?"
"Shikenan kam to amma duk da haka bazaka zauna ahaka kaki aureba......munyi magana da mai martaba akwai yar amininsa zakaje kaganta tunda kai kowacce mace aka hadaka da ita sai kace bata yimaka ba...."
Baice komai ba ya ajiye flate din dambun naman dake hannunshi yatashi zai fita,
"Kafi ruwa gudu sarkin zuciya"
Yana jinta bai tanka ba yadauki hularshi yafita yana zancen zuci,shi wai meyasa aketa tallenshi ne kamar wani wanda ya shekara sittin baiyi aure ba?

Kullum su kenan cikin kai tallenshi wurin kananan yara bayan kuma idan yaje ba daidaitawa sukeyi ba, wannan karon kam babu inda zaije.......
*_Ummi Shatu_*
[2/2, 2:06 PM] Nawarty
: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
22***A zuciye yafita daga sashen gwaggo kilishi yana jin wayarshi na kara amma bai kulaba har saida ya isa wurinda zaidu ya ajiye motarshi shikuma yana can zaune shida sarkin gida da mabudi suna cin rogo da gyada wanda mabudi yasiyo a bakin kasuwa bayan yadawo daga sallar juma'ah,
Hango haisam da zaidu yayi yasashi azamar tasowa bama shi kadaiba hatta su mabudi da hanzarinsu suka taso suna kirari,
"Ran maigida yadade....barka da fitowa baya goya marayu....aljannah mai masoya da yawa...."
Shi ba ma'abocin dariyane satataaa ba shiyasa kawai yadan murmusa yadaga musu hannu cikin sanyin murya yace,
"Assalamu alaikum....kuna lafiya?"
Daga haka yashiga cikin gaban mota bayan zaidu ya bude masa,babu bata lokaci shima zaidun yazagaya yashiga yaja motar sukayi gaba,karar wayarshi da ta dameshi yasashi cirota daga aljihun rigarshi,
"Hello David......kasamo wani bayani ne?.....ok bari zan kiraka zuwa anjima"
Daga haka yakatse wayar yana mai yiwa baura nuni da yatsanshi alamar yakaishi bangarensa bawai fada ba kamar yadda yaga yana kokarin yi.

Sauya akalar sitiyarin motar baura yayi daga hanyar fada zuwa sashen maina wanda da akwai yar tazara tsakani,
Baura na yin parking maina haisam yafito rikeda hularshi yabude falonshi ya shiga bai tsaye anan ba yawuce bedroom dinshi yana shiga yafara kokarin cire rigar dake jikinshi yarage daga shi sai farar vest irinta maza sai dogon wandon shaddar dake jikinshi,jin ana kwankwasa kofa yasashi zama gefen Royal bed dinshi yana tankware kafarshi guda daya,
"Yes...." Yafada muryarsa akasa amma kasancewar baura yagama saninsa ciki da waje har yajiyo daga inda yake tsaye,shigowa dakin yayi yana dan russunawa,
"Ranka yadade akwai abinda kake bukata ne....?

Zan dan leka gidane"
"Bana bukatar komai baura...." Yace da zaidu wanda suke kira da baura,
"To amma ai ranka yadade baka ci abincin rana ba yakamata inje infara karbo maka tukunna...."
"Duba fridge afalo akwai fura da nono ka kawo min ita kadai ma ta isheni....."
Murmushi zaidu yayi sannan cikin wasa yace,
"Yallabai kai dai kam soyayyarka da fura ta musamman ce zaka iya rayuwa da ita ko babu abinci...."
Dan murmushi shima haisam din yayi yana matsa wayarshi,
"Ai ni indai da fura da tea da nama to zan iya rayuwa...."
"Ai nasani yallabai.....bari nakawo maka"
Ganin zaidu yabude kofa yafita yasashi tashi ya dauko laptop dinshi yahaye saman gadonshi yana kokarin kunnata,har lokacin da zaidu yakawo masa furar ya ajiye hankalinsa naga laptop dinshi saboda akwai muhimmin abun da yake dubawa,
Sallama zaidu yayi masa yafita zaije gida yadawo zuwa la'asar,saida ya dan jima idanuwanshi akan laptop din ko kifatawa bayayi sannan yadago ya janyo wayarshi yayi dialing number din David bayan ya dan tsiyayi furarshi kadan wacce tasoma hucewa sabanin da wanda harda kankara aciki,
"Hello David naga komai....yanzu kasan me zai faru?

Bani number din yellow inkirashi...."
Ba ajiyo abinda na kan wayar ke fada wato David,sake gyara zamansa yayi akan gadon ya bude bedside drewar dinshi yadauko wata waya kirar LG,
"Ok fadi muji....."
Saida yagama saka number din sannan yakatse wayar David yasoma kiran ta yellow wacce babu bata lokaci tashiga tana ringing.
Chapter 25 · 0% Book details