← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ubanku na can yatafi yana yimuku fafutukar abinda zai kawo muku kuci kukuma kuna nan kuna bawa hammata iska?

Wadannan iyayen naku basu baku tausayi ba?

Bakwa tunanin wata ta yanke jiki cikinsu ta fadi saboda bacin rai....."
Ta inda iya take shiga bata nan take fitaba har baba yadawo nan take sanar dashi kudurinta na tafiya da badiyya gano ko hakan zai kawo zaman lafiya agidan,
Badiyya tattara nata ya nata tayi shamsiyya sai faman yanka mata harara take kamar idonta zai fado itama tana ramawa,iya mai koko da niyyarta tayi kwanaki biyu agidan amma yanda taga lamarin yasa kawai ta yanke shawarar komawa gida aranar ai kuwa aranar suka kama hanyar gano itada badiyya bayan tabar musu duk tsarabar da ta taho musu da ita daga kauye..........
*_Ummi Shatu_*
[1/30, 2:08 PM] Nawarty
: 19***Bayan tafiyar badiyya da yan wasu kwanaki abdurrahman yashirya yabita can kauyen gano,gaba daya kanta yagama kullewa domin tana son abdurrahman Amma kuma bata son zumuncinsu yasamu rauni ata sanadiyyar haka tunda tasan ayanzu dai idan za atambayi shamsiyya babban makiyinta to ita zatace wannan dalilinne ma yasa da abdurrahman yayi mata maganar turo magabatansa tace sai tayi shawara,langabe kai yayi yana tambayarta wai wacce shawara kuma zatayi tunda dai tana sonshi duk da haka dai bata aminceba tace yajira zata kirashi.

Har bahijja tayi zazzabinta tagama tafara rubuta exam dinta yaya sagir baya daukar wayarta,text massage kuwa tayi masa shi yafi akirga amma bai taba replying dinta ba kuma har lokacin bai sanarwa matarsa da abinda yafaru ba ita kuma gashi sosai suna gaisawa da bahijjan dan kusan kullum sai sunyi chaten,
Abangaren bahijjan kuwa har yau dai hali na nan babu abinda ya canja fitarta club tare da faruk babu abinda yaragu shiyasa karatun exam dinma sama sama take yinsa danma suna samun interval sosai amma duk da haka bata yin wani karatu sosai kamar da dan yanzu har takai takawo bata shigowa makarantar sai ranar da takeda paper dan wani guest lodge faruk yakama musu suke sha'aninsu sosai yake kashe mata kudi har abin yafara bata tsoro,suna zaune dakinta ya bararraje kan gado tana zaune kusa dashi tana kallon kyakkyawan zoben gold din da yabata dazu daga fitarshi yadawo dashi, daga ganin zoben kasan mai tsadane dan yanada kauri sosai ga kyalli da yake faman yi,
"Guy.....wai a Ina kaketa samun kudin nan haka?

Naji last time kuma kana cewa account dinka yayi kasa....."
Dan tashi zaune yayi ya kalleta,
"Baby kawai ki basar.....

Dad na yiwa 419....."
Shiru tayi tana kallonsa wato ayanda ta fahimta faruk yayiwa kudi mummunan sabo sam bazai iya rayuwa batare da kudi ba tabbas kashe kudi dabi'arsace da bazai iya canja ta ba sai dai wani kadari na Allah.

Lumshe idanuwanta tayi tana kallonshi,
"Faruk 419 kuma?

Dad din naka?"
"Baby to ya hanani kudi yahanani inji dadin rayuwata kinga kuwa ai dole nima inrinka ha'intarsa......"
"Gaskiya guy karka kara ai mahaifi babu kamarsa aduniya.....kaji?"
"Naji baby....yanzu bari naje nayi bacci kafin zuwa yamma sai mu fita ko?"
"Babu matsala guy....ina jiranka"
Tashi yayi yafita ita kuma taci gaba da zama tana kallon zoben da yabata,to me faruk yake nufi?

Ita dai tasan bawai soyayya suke yiba amma dai suna kulawa da juna a matsayinsu na abokai, Koda yake watakila shima kawai yabata dinne amatsayin friendship bawai soyayya ba.

Aranar tunda suka fita dashi basu waiwayo masaukinsu ba sai karfe 1 nadare,washe gari tashiga school tunda sassafe domin tanada exam da rana,adakinsu lady tayi masauki ta iskesu suna baccinsu na asara kamar yadda suka saba bayan sunyi kurbe kurbensu.

Bayan sun kammala exam dinsu gaba daya bata tafi gidaba saida ta kara sati daya awurin faruk aranar da zasu tafi umarah shida dad dinsa aranar itama tatafi gida,
Tasamu kyakkyawar tarba awurin marakisiyya matar yaya sagir amma shi kam bai sakar mata fuskaba fushi yake da ita sosai da sosai duk da yana kokarin boyewa dan kar matarshi ta gane,
Wani abu dake kara daure masa kai shine tunda bahijja tadawo bata da wani aiki sai na barci wuni zatayi tana kwance duk lokacin da zai tambayi marakisiyya ina bahijja amsar guda dayace shine tana bacci babu wani aikin gida da take taya marakisiyya sai gayyar bacci nan yasoma tsarguwa da wannan baccin nata marar karewa,
Fara saka mata ido yayi sosai ko zai gano wani abu amma batare da saninta ba,yau yakasance weekend yana gida itama marakisiyya na nan amma tace masa zataje asibiti dubiyar mijin yayarta,yana zaune afalo Bayan fitar marakisiyya bahijja tafito cikeda bacci a idonta ta shiga kitchen,daki tawuce rikeda filet dinta na abinci da robar lemu,
Saida tagama komai ta koshi sannan ta daga katifar dake kan gadon ta dauko kwalbar syrup tabude zata fara sha kenan taji andauketa da wani gigitaccen mari dukanta yashiga yi da kafa babu kakkautawa domin tuni tafado kasa daga kan gadon,ahaka marakisiyya tazo ta sameshi duk kafarsa na ciwo sakamakon bubbugewar da yayi wurin dukanta sannan itama bahijjan tana daki sai kuka takeyi dan ta daku sosai ba kadanba sai faman murkususu take yi,
Cikin tashin hankali marakisiyya ta shiga ta riketa tana tambayar ta abinda ke faruwa amma takasa magana sai kuka takeyi,shima kuma yaya sagir din yaki fadin laifin da tayi masa da yagama ta dameshi da tambaya hade rai yayi yawuce dakinsa yana cemata ta dafa masa ruwan zafi zai gasa kafarshi,
Yana gefen gado azaune abun duniya yataru ya isheshi marakisiyya tashigo dauke da ruwan zafin ta ajiye agabansa tana kallonshi,
"Kafafuwa na Zaki gasa min please...." Yafada yana kokarin kwanciya,
Batayi magana ba ta dauko towel karami ta tsoma tafara gasa masa kafafuwan nashi saida ta kusa gamawa sannan tayi magana cikin sigar lallashi,
"Amma yaya sagir ni ina ganin koma wanne laifi bahijja tayi maka bai dace karinka yimata irin wannan dukan ba,nasiha zaka rinka yimata da kuma bada shawara amma duka baya gyara.... sannan kadai san ita ba lafiyayya bace baka gudun ka ja mata wata lalurar kuma?

Yanzu dan Allah meye amfanin wannan dukan da kayi mata kamar wata karamar yarinya...."
Shiru yayi bai tanka ba yanajin zuciyarshi nayi masa radadi ganin alamun bazai yi magana ba yasata tashi tafita dauke da ruwan zafin da yasoma hucewa,
Wurin bahijja tasake komawa wacce har lokacin tana kwance tana kuka,zama tayi agefenta tasoma yimata magana cikin kwantar da hankali,
"Bahijja koma wanne laifi kika yiwa yayanki nasan mai girmane dan haka kawai bazai kamaki awannan shekarun naki yace zai dakeki ba....kefa yanzu ba yarinya bace,dan Allah kidaina laifi irin wannan....yanzu kiyi hakuri kiyi shiru ki daina kuka idan yaso anjima sai muje kibashi hakuri....kiyi hakuri kinji"
Dakyar marakisiyya ta shawo kanta tatashi tahau saman gado ta zauna ita dai marakisiyya sai bin dakin take da kallo ko wai zataga wata alama wacce zata bata haske akan laifin da bahijja ta aikata amma bata ga komai ba domin tuni yaya sagir ya tattare duk wasu kwayoyi da syrup da yagani akasan gadon yaje ya boye a inda bazasu taba ganiba,domin acikin motarshi ya boye,
Cigaba da lallashinta marakisiyya tayi daga bisani tafita tabar dakin ta nufi nata,tana fita kiran faruk yashigo cikin wayarta da number dinshi ta waje domin bayan sun bar saudiyya da Dad dinshi kasar Spain suka wuce,
Muryarta adashe da alamun kuka ta dauki wayar tana sharar hawaye,
"Baby.... me kuma yafaru?

Najiki kamar kina yin kuka, what's happening?

Tell me please"
Kwashe abinda yafaru tayi ta fada masa tana sake zubar da wasu hawayen,
"Ayyah baby....gaskiya wannan brother din naki baida kirki.......am very sorry kinji,kiyi shiru kin san ban son kukanki........"
Tamkar wata jaririya haka yasata agaba yana rarrashi har ta saki ranta, lokacin da marakisiyya tazo ta isketa tana zuba fara'a da hira sosai sai abin yabata mamaki nan tafita tabarta da murmushi akan fuskarta,
Har dare bata yarda tafito falo ba gudun kar su hadu da Yaya sagir asalima kunyar ganinshi take ji gashi bata jin dadin jikinta gaba daya kuma dan ganganci sai tayi wanka da ruwan sanyi,ahaka dai taketa daddaurewa amma ita kadai tasan me take ji ajikinta,
Tana kwance tukunkune cikin bargo Yaya sagir yayi sallama yashigo fuskarshi adaure,
"Ki shirya kayanki zuwa gobe zamu je tarauni zan kaiki gidan hajiyan tarauni dazu ta kirani awaya tace inkaiki kije ki karasa hutunki acan",daga haka taga yajuya yafita bai jira yaji abinda zatace ba,shi harga Allah baya son bahijja tayi nisa da gida ayanzu saboda wadannan munanan halayen da ta koyo to amma babu yadda ya iya tunda hajiya itace takirashi da kanta tace yakaita,tun acikin daren ta kintsa kayanta ta zuba cikin jaka duk abinda tasan zata bukata ta sakashi ciki daga nan ta kwanta,tana nan kwance marakisiyya tashigo suka dan taba hira zuwa 9:30 tayi mata sallama tafita,faruk ta kira tana sanar dashi hutun da zataje.

Washe gari bayan ta kammala breakfast wanka tayi tashirya cikin doguwar riga ta atamfa ta yafa mayafi taja jakarta tafito inda yaya sagir ke jiranta fuskarshi babu walwala marakisiyya na tsaye gefenshi,
"To yan hutu kuma sai yaushe za adawo?"
Murmushi bahijja tayi sannan cikin rashin kwarin jiki tace,
"Before akoma makaranta dai..."
"To shikenan Allah yakaimu,ki gaida su hajiyan, yaya adawo lfy"
Ciki ciki ya amsa sannan yafita bahijja na biye dashi,bai kulataba har saida suka fara tafiya sannan yace,
"Wato ke irin rayuwar da kika zabawa kanki kenan ko?

Bahijja wai me kikeso ki zamane?

Mai kunnen kashi?
Chapter 22 · 0% Book details