← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kayi min wani abune?"
Daga haka ta fincike tawuce bedroom dinta, duk yadda yaso yashawo kanta ta saurareshi suyi magana ki tayi har dare babu wani cigaba, lokacin da yakammala shirin bacci kamar jiya arufe yaji kofar tata yauma haka yayi kwanan takaici shiyasa tun jikin asubah wani zazzabi yafara hawa kansa kafin gari yawaye zazzabin yagama rufeshi ruf....
*Anan nakawo karshen d'andanon kumallon mata ga mai bukatar siyar wannan labari.... wato mulki ko sarauta Kashi na biyu na marubuciya phertymah xarah da kuma takwaransa kumallon Mata wanda ke dauke da cigaban labarin kamar da wasa wanda marubuciya ummi Aisha ta rubuta...

Wanda ke bukatar wadannan dadadan littattafan guda biyu zai biya 500 mai son guda daya kuma zai biya 300 ta wadannan lambobi kamar haka.*
2083371244
Aisha M.Salis.

Zenith Bank
Sai atura shaidar biya ta wannan no
+447894142004
Ko kuma recharge card ta wannan no
08169334980
*_Ummi Shatu_*
[1/21, 5:06 AM] Nawarty
: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
4***Yanda ya kwana da zazzafan zazzabinsa haka yatashi dashi shiyasa ma yakasa tashi bare yakai ga fitowa, bilkisu kwata kwata bata da masaniyar abinda ke faruwa shiyasa ko lekashi ba tayiba lokacin da ta tashi, saida ta kammala hadawa yara breakfast da wanda zasu tafi dashi school ta sallamesu suka tafi sannan ta gyara gidan, breakfast din fahad daban ta hada masa kamar yadda tasaba, tana kammalawa taje tayi wanka sannan tayiwa mimi ta shiryata ta dauko duk abinda take bukata tafito tana rikeda mimi, ruwan tea kadai tasha saboda daga shekaran jiya zuwa yau bata iya cin abinci.

Bata yi tunanin ta duba fahad ba ta sabi yarta suka tafi, gidan ammah tafara zuwa takai mimi kamar yadda ta saba sannan tawuce office, wayarta gaba daya kwana biyun nan akashe take saboda bata son damuwa,
"Allah sarki khulsum kawata, nayi missing dinki over, da kina nan na tabbata tare zamuyi shearing din wannan damuwar tawa..."
Ta furta ahankali sannan ta kwantar da kanta jikin kujerar da take zaune, tana aikinne dai kawai cikin karfin hali amma azahiri bata cikin nutsuwarta gaba daya bata da walwala, damuwace fal zuciyarta.

Shikam fahad yana can kwance cikin zazzabi gashi yanata kiran wayar bilkisu amma baya samunta wayar akashe hakura yayi ya zubawa sarautar Allah ido, zuwa can sai ga kiran husnah, tun daga yanayin yanda taji yana magana da kyar ta fahimci baida lafiya nan ta tambayeshi abinda ke damunshi ya sanar da ita, text massage ta turo masa na magungunan da za asiyo masa harda drip guda biyu dan yafi jin karfin jikinsa, salim ya turawa massage din da husnah ta turo, ba afi mintuna ishirin ba sai ga kiran salim, awahalce ya daga yacewa salim kawai yashigo master bedroom dinshi, babu bata lokaci yaji alamun bude kofa alamar salim yashigo kenan gaban gadon yakaraso ganin yanayin da fahad din ke ciki yasa salim komawa bakin kofar yacewa Rabi'u yashigo dama tare suka taho dashi makocinsu ne kuma yanada chemist dinshi da yabude nan jikin gidansu salim din,
Duk wata kulawa da yake bukatar abashi cikin gaggawa Rabi'u yabashi da taimakon salim daga karshe aka daura masa drip, kallon fahad salim yayi sannan yace,
"Ina ita Maman hanfa dinne?"
"Taje office" yabashi amsa atakaice,
"To akirata mana...

Ai yakamata tadawo ta zauna tare dakai..."
Shi dai baiyi magana ba saima lumshe idanuwansa da yayi.

Koda rabiu yatafi salim na nan tare dashi, breakfast din da bilkisu ta shirya shi yadauko yazuba yaci,duk inda take yasan karfe 1 nayi zata dawo saboda yin abincin rana, ai kuwa daya nayi sukaji dirin shigowar motarta,
Tana shigowa babban falo ta hango salim na fitowa daga dakin fahad,
"A'a abba salim kuna ciki dama?"
"Wallahi kuwa hajjaju, mijinki ashe babu lafiya shine nazo da likita yaduba shi yanzu gashi can ansaka masa karin ruwa...

Ni garama da Allah yakawoki dama inada uzuri"
"Subhanallahi, amma sai bayan da natafi ko?

Bari naganshi..."
Tare suka shiga dakin fahad, idanuwanshi alumshe alamar bacci yakeyi, sallama salim yayi mata yafita, cikin sauke ajiyar zuciya ta zauna gefenshi tana kallonshi sai taga ya fada gashi jikinsa akwai dan zafi kadan alamun zazzabi, goshinsa ta dafa sannan ta rike hannunshi wanda ba ashi ake kara masa ruwanba,
"Am sorry bae...

Sannu Allah yabaka lafiya....."
Tana nan tare dashi tun dazu aketa kiran wayarshi amma ita dai bata duba ba jin kiran yaki karewa yasata dauko wayar wacce ke can gefen pillownshi ta duba, husnah love taga anrubuta ajiki, tabe baki tayi ta ajiye masa wayar agefenshi daga karshe tasaki hannunsa bayan tayi masa kiss tamike tafita, girki mai sauki ta shirya tana yi tana zuwa tana lekashi amma har lokacin bai tashi ba,wanka tayi tasaka English wears riga da skirt tasake komawa wurin fahad lokacin yafarka,zama tayi gefensa,
"Sannu bae....

Yajikin?"
"Da sauki..."
"Allah yabaka lafiya....

Akira salim suzo su cire maka wannan ruwan ko?

Tunda naga yakare saura kadan"
Kai yadaga mata yamika mata wayarshi, karba tayi sannan ta nuna masa screen din wayar,
"Ankiraka...."
Kalla kawai yayi baice komai ba, ita dinma bata kara cewa komai ba ta kira salim ta sanar dashi sakon fahad,
Rigar jikinshi yayi mata nuni da ta dan cire masa botiran dake jiki saboda zazzabin jikinsa yasakeshi nan ta babballe masa sannan ta mike tafita zuwa bedroom dinta, hijabi tasako tadawo wurinshi ko zama bata yiba taji knocking sake juyawa tayi taje ta bude, salim ne da rabi'u suka shigo ganin yanda fahad yayi laushi yasa salim fara tsokanarshi,
"Haba ango yakuma zaka kwanta jinya tun amaryar batazo ba..."
Ita dai bilkisu tana jinsu dariya kawai take danyi har zuwa lokacin da rabi'u ya kammala komai sannan yakara jaddada mata lallai lallai yaci abinci yasha magungunanshi gasu nan, godiya tayi musu suka yi sallama dasu suka fita, bata fuska yayi yana kallonta,
"Me kuma kakeso?" Ta tambaya tana zama kusa dashi, hannunta yakama sannan yanunata da hannu,
"To menene na bata ran?

Saki fuskarka mana...

Dan yi murmushi nagani please...."
Makale kafada yayi hakan yasata dan murmusawa sannan ta mike tawuce bathroom tana fadin,
"Bari inhada maka ruwa kayi wanka sai kaci abinci kasha maganin..."
Da taimakonta yayi wankan yayi salla sannan yasake kwanciya, shi dama jinyarshi haka take sam baya kaunar shan magani da cin abinci, macaronin da ta dafa jalop wanda yaji kifi sukumbiya ta zubo masa saida tayita lallabashi kamar wani jariri sannan yayarda ya dan ci yasha magani yasake kwanciya,
"Wai tun yaushe ne kafara rashin lafiyar....?" Ta tambayeshi bayan ta ajiye cup din dake hannunta wanda tabashi ruwa yasha,
"Tun ranar da kika fara fushi dani...." Yafada yana maida kanshi kan cinyarta,
"Ayya bae kuma shine baka fada min ba?"
"Tayaya zan fada miki bayan kin ki kulani....

Ni wannan fushin naki yafi komai zafi agareni...

Da kiyi min irin wannan fushin gara ki hanani auren gaba daya...."
Yatsanta ta dora kan bakinshi,
"Yawuce please....

Idan nahaka aure zina nake son kaje kafara?

Karka damu Allah yabaka ikon yin adalci..."
"Allah idan kikace kar nayi hakura zanyi baby, bana son wannan fushin da kikeyi"
"Insha Allah bazan karaba, katashi daga zazzabin nan haka please ko dan ni da yaranmu"
"Nasamu sauki ai dama kin kulanin da bakya yine yajawo min shi...."
Dariya tayi ta sumbaci kumatunshi tana dagowa suka hada ido yayi dariya,
"Ina mimi na ne wai?"
"Ohh my God...

Ko kasan na manta da yarinyar nan..."
Murmushi yayi yamatsa hannunta dake cikin nashi,
"Ashe dai har yanzu ana sona tunda gashi ana mantawa da auta saboda lalurata..."
"Ai idan ina tare dakai bana tunawa da kowa bae...

U are my world...."
Murmushin jin dadi yayi yakafeta da ido yana motsa baki, harararshi tayi tafara kokarin mikewa,
"Kaida baka da lafiya amma shine zaka fara jan fada ko?

Dagani naje na kira ammah infada mata tasa akawo min baby nah"
Sake kankameta yayi dakyar ta banbareshi tafita, tana kunna wayarta bata kai ga kiran ammah ba kiran khulsum yashigo,
"Besty tun safe fa nake son kiranki..." Inji bilkisu,
"Allah sarki kawata, yagida ya yaran?

Kin san me?

Kiranki nayi infesa miki Dazu na haduda kawarki awani group anata fada da ita akan wai anturo wani topic wanda yashafi kishiya shikenan fa infada miki mutuniyarki ta rude taketa maganganu daga karshe har ta mayar da abun fada...

Daga fa cewa wai ai tunda masoyin masoyinka shima masoyinka ne dan haka ashe kishiya itace babbar masoyiyarka tunda masoyiyar mijinka ce shikenan tahau sababi...."
"Wai wa kike magana ne khulsum...?"
"Shamsiyya Abbas makaho fa, ai saida nabita private ina bata hakuri nagane ma ashe mun san juna, shamsiyya yar bencinku dai kuma yar hostel dinku..."
Dariya bilkisu tayi kafin tace,
"Assistant house captain fa?

Dan Allah tana ina yanzu?
Chapter 5 · 0% Book details